Editor

9513 Posts
Rashin haihuwa: Laifi matar ne! (2)

Rashin haihuwa: Laifi matar ne! (2)

Daga AMINA YUSUF ALI To ko laifi ta ne, ko ba laifi ta ba ne, a ƙasar Hausa da wasu wurare a Afirka sun ce laifin matar ne rashin haihuwa. To maimakon a dinga nuna yatsa ga wani a ce laifinsa ne matsalar haihuwa, me zai hana a  yi ninƙaya a kogin bincike a samo mafita? Don muna ganin abubuwa da dama a rayuwar zahiri. Inda za ka ga mace tana zaune shekara da shekaru da namiji ba haihuwa, amma tana fita daga gidansa, ta yi wani auren, sai ka ga ta samu haihuwar. Idan mai rabon tagwaye ce ma…
Read More
Matasa ne barazanar Arewa da ‘yan Arewa a yanzu?

Matasa ne barazanar Arewa da ‘yan Arewa a yanzu?

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN Wato a yau da kuma wasu 'yan shekaru masu zuwa, ba abinda hasashe ya nuna yane barazana ga Arewa da kuma 'yan Arewa irin matasanta 'yan shekara 13 zuwa 25.  Yawancin wannan yaran ba su san inda suka dosa ba a rayuwa, ba su da manufa, kuma ba a ɗora su a kan wata hanya mai kyau ba. Hakazalika, ba ruwansu da tarbiyyar addini, ba abunda ya shafe su da tarbiyya kyakyawa ta al'ada.  Yara ne da babban abin da suka sanya a gaba shi ne, ya za su yi kuɗi, kuma za su iya yin…
Read More
Maciji ya tilasta wa jirgin sama saukar gaggawa

Maciji ya tilasta wa jirgin sama saukar gaggawa

An tilasta wa wani jirgin sama yin saukar gaggawa bayan wani ya ga maciji a cikin jirgin. An hangi macijin a cikin gurbin fitilar da ta ke haska saman jirgin na Kamfanin AirAsia. Jirgin ya taso ne daga Kuala Lumpur Babban Birnin Malaysia zuwa Gundumar Tawau da ke Jihar Sabah a Malesiya. Yau APC za ta fara sayar da fom ga ‘yan takaraSakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix Har yanzu dai ba a bayyana wanda ya fara ganin macijin ba, amma an sanar da matuqan jirgin nan take, kuma Kyaftin ɗin jirgin ya yanke shawarar yin saukar gaggawa…
Read More
Yau APC za ta fara sayar da fom ga ‘yan takara

Yau APC za ta fara sayar da fom ga ‘yan takara

Daga BASHIR ISAH An bayyana cewa a wannan Talatar jam'iyyar APC za ta fara sayar da fom na neman tsayawa takara a zaɓuɓɓukan 2023. Tun farko, APC ta shirya sayar da fom ɗin ne a Asabar da ta gabata amma sai ta ɗage saboda wasu ƙalubalai da ta fuskanta inda aka cim ma matsaya game da sabon lokacin da za a soma sayar da fom ɗin ranar Juma'a da addare. Sanarwar da ta sami sa hannun babban jami'in yaɗa labarai da ke hedikwatar APC a Abuja, Yusuf Ali, ta nuna 'yan takarar Majalisar Dokoki a jihohi za su sayi nasu…
Read More
Sakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix

Sakataren MOPPAN ya zama jami’in shirye-shiryen Kamfanin Northflix

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An farkon makon nan aka naɗa fitaccen jarumin Kannywood, Umar Gombe, a matsayin jami’in shirye-shirye na Kamfanin nuna finafinai na Northflix. A cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sa hannun Shugaban Kamfanin Northflix, Alhaji Jamilu Abdulsalam, ta nuna cewa, an naɗa Mataimakin Sakataren MOPPAN na Ƙasa, wato Umar Gombe, a matsayin Jami'in Shirye-shiryen kamfanin na farko.Gombe zai jagoranci fannin shirye-shirye na kamfanin wajen bunƙasa harkar kasuwancin finafinan Hausa a duniya.  A yayin da ya ke yin ƙarin haske dangane da kamfanin, Alhaji Abdulsalam ya nuna cewa, musabbabin buɗe cibiyar Northflix shi ne, domin ƙara…
Read More
’Yan Nijeriya Miliyan 33.4 na amfani da Kirifto Karansi duk da haramcin CBN – Bincike

’Yan Nijeriya Miliyan 33.4 na amfani da Kirifto Karansi duk da haramcin CBN – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI  Rahotanni sun nuna cewa, kaso 20 da shiga daga masu zuba hannun jari a harkar sulalla na yanar gizo da aka fi sani da Kirifto Karansi sun fara dillancinsa a kwanakin nan. Haka zalika sabon rahotan ya bayyana cewa kaso 35 na balagaggun mutanen Nijeriya suna zuba hannun jari a kasuwancin sulallan.  Kodayake a kwanakin nan Babban Bankin Nijeriya ya haramta amfani ko hada-hadar sulallan Kirifto karanci a dukkan bankunan Nijeriya. Amma duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa, kimanin 'yan Nijeriya miliyan 33.4 sun mallaki kadara ta Kirifto ɗin ko kuma suna hada-hadar cinikayyarsa.  Haka…
Read More
FIRS ta karrama Yobe saboda lashe gasar jiha mafi tara mata haraji a 2021

FIRS ta karrama Yobe saboda lashe gasar jiha mafi tara mata haraji a 2021

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar tattara haraji ta tarayyar Nijeriya, FIRS, ta miƙa kambun girmamawa ga Jihar Yobe a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha tattara haraji mai yawa daga cikin jihohi na shirya ta 'B'. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito.  Jihar Yobe ita ce ta lashe gasar FIRS a matsayin  jahar da ta yi zarar a samar da haraji ga hukumar daga jihohin shiyyar 'B'.  Shugaban tsare-tsaren FIRS na shiyyar B, Mista Mohammed Mayanda, shi ya bayyana haka a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Damaturu, jim kaɗan bayan ya miƙa kambun girmamawar…
Read More
Mace ’yar kwalliya ce

Mace ’yar kwalliya ce

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake saduwa a cikin shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja. Allah ya karɓi ibadunmu Ya sa mu cikin bayinSa da zai 'yanta a wannan wata na Ramdana.  A halittar 'ya mace a duk inda ta tunkaro, ana fara kallon abin da ta sa, yanayin shigar ta kafin kallon halittar jikinta. Wannan na nufin shigar mace ko kwalliyar ta ce annurinta. Duk kyawon ki, zai samu nakasu inhar ba kya gyara ko ince kwalliya. Kwalliyar da na ke magana kai a nan ba wai ta shafe-shafen kayan ƙyalƙyali ko ƙarin haske ko canza wani…
Read More
Amfanin dabino a jikin ɗan adam (2)

Amfanin dabino a jikin ɗan adam (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI Kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata. Dabino shahararren itaciya ce a duniya da ta shahara. Binciken masana da ƙwararrun masana kiwon lafiya ya tabbatar cewa dabino yana da sinadari masu tarin yawa wanda ke da tasirin gaske wajen bunqasa lafiya da garkuwar jikin ɗan’adam. Dabino yana da sinadarai kamar su magnesium da calcium da potassium da makamantansu. A addinin Musulunci dabino yana da tasiri da gurbi na musamman. Dabino yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam wanda zai yi wuya a iya zayyano amfaninsa a lokaci guda. Daga cikin amfaninsa akwai:- Ana sarrafa…
Read More
Yadda ƙasar Sin ta bai wa fannin lafiyar duniya tagomashi

Yadda ƙasar Sin ta bai wa fannin lafiyar duniya tagomashi

Daga AHMAD FAGAM Masu hikimar magana na cewa, “yabon gwani ya zama dole.” Yayin da ranar 25 ga watan Afrilu ta kasance a matsayin ranar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro wato maleriya ta ƙasa da ƙasa, ko shakka babu, duniya ba za ta taba mantawa da dunbun alheran da ƙasar Sin ta samar ga fannonin daban-daban ba, musamman fannin kiwon lafiyar bil adama. Albarkacin wannan rana ta bikin yaƙi da cutar maleriya ta shekarar 2022, bari mu yi tsokaci kan wata muhimmiyar gudummawa da ƙasar Sin ta baiwa duniya wajen yaƙi da cutar maleriya. Ƙwayar maganin Artemisinin, wani magani…
Read More