Editor

9513 Posts
Gwamnatin tarayya ta sake buɗe iyakokin ƙasa a wasu jihohi

Gwamnatin tarayya ta sake buɗe iyakokin ƙasa a wasu jihohi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Juma’a ne gwamnatin tarayya ta amince da sake buɗe wasu ƙarin kan iyakokin ƙasar guda huɗu da aka rufe a watan Agustan 2019 a wani mataki na daƙile fasa ƙwauri da bunƙasa noman shinkafa a cikin gida a ƙasar nan. A wata sanarwar da hukumar kwastam ta Nijeriya ta fitar mai ɗauke da sa hannun mataimakin kwanturola Janar E. I. Edorhe a madadin shugaban hukumar ta Kwastam Hameed Ali, iyakokin sun haɗa da kan iyakar Idiroko a jihar Ogun, kan iyakar Jibiya a jihar Katsina, Kamba iyaka a jihar Kebbi da Ikom iyaka a…
Read More
Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga Oxford Zuwa Maiduguri: Labarin Farfesa William Richards

Daga PORTIA ROELOFS Cigaba daga makon jiya. A waɗannan lokutan da tafiyar gobe-yau-jiya ke gudana, wato Time Travel ga tunanin Farfesan, a lokaci guda kuma jasadinsa da ruhinsa suka kasa mayyaze da bambance shin har yanzu a cikin Saharar Maiduguri suke ko kuma a katafaren gurin da ake kira da Queens College Oxford da ya ke a Jamiar Oxford suke. Sai ya cigaba da sambatun sa kamar haka: Maimakon na bi ta ƙofofin zinare da azurfah na Aljannah, kullum abunda na fi so sama da hakan shi ne na roƙi alfarmar St Paul ko zan iya zama kusa da shi…
Read More
2023: Fitattun ’yan takarar da ke zawarcin Nijeriya

2023: Fitattun ’yan takarar da ke zawarcin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alamu sun nuna gangar siyasar 2023 ta fara zaƙi, inda masu sha'awar ganin sun gaji kujerar Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya a zaɓen mai ƙaratowa na 2023 sai ƙara wasa wuƙarsu irin ta siyasa suke yi ta fuskar kwarzanta kai da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a sha'anin siyasa. Blueprint Manhaja ta yi nazarin wasu fitattun 'yan takarar neman kujerar Shugaban Ƙasar Nijeriya da suka fito daga jam'iyyu daban-daban, kamar haka: Yan takarar APC: Yemi OsinbajoOsinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya ce, ya tsaya takara…
Read More
Na gama haddace halayen Buhari don zama Shugaban Ƙasa – Osinbajo

Na gama haddace halayen Buhari don zama Shugaban Ƙasa – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ce ya naƙalci duk wasu halaye na Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce hakan zai taimaka masa wajen zama Shugaban Ƙasa. Osinbanjo ya furta hakan ne ranar Juma'a yayin wata ganawa da ya yi da wakilan Jam'iyyar APC a Jihar Oyo. Da yake bayyana nagartar sa a gaban wakilan, mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya share shekaru dama yana samun horo da kuma shirye-shirye. Osinbanjo ya yi amannar cewa yana da ƙwarewar da zai tafiyar da ƙasar nan matuƙar ya gaji kujerar Shugaba Buhari a zaɓen 2023…
Read More
Jerin matan marigayi Oba na Oyo guda 13 da ‘ya’yansa

Jerin matan marigayi Oba na Oyo guda 13 da ‘ya’yansa

Daga AISHA ASAS A ranar Juma'ar da ta gabata, 22 ga Afrilu, 2022, Jihar Oyo ta yi rashin jigo kuma smbasarakenta, wato Alaafin Oba Lamidi Adeyemi. Ya rasu yana da shekaru 83. Shekara 52 da hawansa karagar mulki. Marigayin ya kasance na farko a tarihin masarautun Nijeriya na wannan zamani da ya tara adadin matan aure 13 da suke ƙarƙashin ikonsa. Kafin mutuwar basaraken, ya ɗaura aure da mata ɗaɗaya har 13, ciki kuwa har da 'yar ƙabilar Ibo da ya aura a shekarar 2020 kuma amarya daga cikinsu, wato ta cikon sha uku.Oba Lamidi Adeyemi ya zama Alaafin na…
Read More
Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alaafin na Oyo

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi Alaafin na Oyo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ’Yan Nijeriya sun wayi gari da wani labari mai firgitarwa na rasuwar Sarkin Yarbawa, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III wanda ya rasu a daren Juma’a 22 ga Afrilu, 2022. Oba Lamidi Adeyemi III, mai shekaru 83 (marigayi), wanda aka fi sani a Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan sarakuna a ƙasar wanda ya kwashe kusan shekarun Nijeriya akan karagar mulki. Mulkinsa na Alaafin na Oyo ya fara ne a shekarar 1970 shekaru 10 kacal bayan Nijeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Ingila. Ya shafe shekaru 52 akan karagar mulki,…
Read More
Ƙaddarar Assange ta nuna makircin zaman walwala mai salon Amurka

Ƙaddarar Assange ta nuna makircin zaman walwala mai salon Amurka

Daga CMG HAUSA Kwanan baya kotun birnin Landon ta ƙasar Birtaniya ta amince da mika Julian Paul Assange wanda ya kafa shafin yanar gizo na Wikileaks a ƙasar Amurka a hukumance, lamarin da ya sa aka nuna shakku ko kuma adawa gare shi. Wasu mutane dake goyon bayan Assange su ma sun yi taro a wajen kotun domin yin adawa da ƙudurin. Kana lauyan Assange ya yi nuni da cewa, mai yiwuwa ne za a tsare Assange a gidan yari har tsawon shekaru 175, babban editan shafin yanar gizo na Wikileaks Kristinn Hrafnsson ya bayyana cewa, matakin da Amurka da…
Read More
An kammala taron dandalin Boao na 2022

An kammala taron dandalin Boao na 2022

Daga CMG HAUSA Jiya Juma’a 22 ga wata, an kammala taron shekara shekara na dandalin Asiya na Boao mai taken “Annoba da duniya: Ingiza ci gaban duniya da gina makoma tare”, babban sakataren dandalin Li Baodong, ya bayyana yayin taron manema labaran da aka shirya jiya da yammacin ranar cewa, shawarar gudanar da tsaron duniya, babban sakamako ne da aka samu yayin dandalin na wannan karo. Li Baodong ya kara da cewa, tsaro ya fi muhimmanci yayin da ake ƙoƙarin samun ci gaba, kuma ya dace bil adama su hada kansu a yayin da ake ƙoƙarin tabbatar da tsaro, don…
Read More
Ranar littafi ta duniya: Adadin litattafan da Sinawan suka karanta ya ƙaru a 2021

Ranar littafi ta duniya: Adadin litattafan da Sinawan suka karanta ya ƙaru a 2021

Daga CMG HAUSA Cibiyar nazarin dab’in labarai ta ƙasar Sin ta fitar da sakamakon binciken da aka yi game da karanta litattafai na al’ummun Sinawa karo na 19 a yayin babban taron karanta litattafai karo na farko da aka shirya da yammacin yau Asabar 23 ga wata, inda aka bayyana cewa, adadin litattafan da kowanen Sinawan da suka kai shekarun haihuwa 18 ya karanta a shekara 2021 ya kai guda 4.76, adadin litattafan da ya karanta ta yanar gizo ya kai guda 3.3, duka sun karu bisa na shekarar 2020. Kana adadin litattafan da kowanen Sinawa waɗanda ba su kai…
Read More
Mahalarta taron dandalin Boao sun yi kira ga ƙasa da ƙasa da su ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da cutar Covid-19

Mahalarta taron dandalin Boao sun yi kira ga ƙasa da ƙasa da su ƙarfafa haɗin gwiwar yaƙi da cutar Covid-19

Daga CMG HAUSA Har zuwa yanzu, cutar Covid-19 na ɗaya daga cikin ƙalubalolin da ’yan Adam ke fuskanta. A gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao da ke gudana, mahalarta taron sun ba da shawarwarinsu ta fannin rage giɓin da ke tsakanin ƙasa da ƙasa ta fannin yaƙi da cutar, waɗanda kuma suka yi nuni da cewa, ƙasar Sin na ba da babbar gudummawa ta wannan fanni. Alƙaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, bayan da ƙasar Sin ta ƙirƙiro rigakafin cutar, ya zuwa yanzu ta riga ta samar da alluran rigakafin sama da biliyan…
Read More