24
Apr
Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Mai son tsayawa takarar gwamnan Sakkwato a tutar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 kana ɗa ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sagir Attahiru Bafarawa ya tsallake rijiya da baya ne bisa ƙoƙarin hallaka shi da wasu da ake zargi ɓatagari ne da yunƙurin yi a Sakkwato. A wani bayani da dandalin goyon bayan Sagir Bafarawa suka fitar, sun bayyana cewa wani sanannen ɓatagari a Sakkwato Alu KC ne suka dirar wa gidan Sagir da nufin hallaka shi jim kaɗan bayan kammala sallar Taraweeh a daren ranar Talata wanda ya tsallake rijiya da baya a lokacin. “Yau…
