Editor

9513 Posts
Siyasarmu a yau

Siyasarmu a yau

Assalamu alaikum. Barkanmu da har haka, da fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya. Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja, Amin. Gabanin zuwan zaɓe, waye zai zama angon Nijeriya a 2023? Shekaru 23 kenan, da fara mulkin dimukraɗiyya a Nijeriyya, an yi shugabanni daban-daban, a kuma yi jami'iyyua na siyasa daban-daban, kamar irin su; Jam'iyar PDP, wanda ita ce ta fara mulkin ƙasar nan a tsari ma dimukraɗiyya, sai kuma APC, wanda ita ce ke kan mulki yanzu haka bayan da PDP ta yi shekara 16 a mulki, yanzu kuwa APC ne ke kan mulki. Cif Obasanjo ne ya mulki ƙasar…
Read More
Bikini Ista: APCON za ta Maka Bankin Sterling a kotu bisa ɓatanci ga Yesu Al-Masihu

Bikini Ista: APCON za ta Maka Bankin Sterling a kotu bisa ɓatanci ga Yesu Al-Masihu

AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai cibiyar kula da harkokin tallace-tallace ta ƙasa (APCON) za ta maka Bankin Sterling a kotu kan wani saƙon taya murnar bikin Ista da bankin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo, wanda cibiyar ta APCON ta ayyana a matsayin cin fuska ga Yesu Al-Masihu.  APCON ta bayyana saƙon taya murnar da bankin ya wallafa wanda yake kwatanta ɗaukakar Yesu ɗin da tashin fitaccen biredin Legas ɗin nan mai suna, 'Agege bread' a matsayin abinda bai kamata ba. A cewar ƙungiyar wannan saƙon na talla da Sterling ya wallafa ya yi gaban kansa ne…
Read More
Kawo ƙarshen satar ɗanyen mai

Kawo ƙarshen satar ɗanyen mai

A kwanakin baya ne wata Babbar Kotun Tarayya da ta ke zamanta a garin Fatakwal taJihar Ribas ta samu wasu mutane biyar da laifin satar man fetur da kuma safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba kuma ba tare da lasisin da ya dace ba sannan ta yanke musu hukunci daban-daban. Wannan dai na ɗaya daga cikin yawaitar satar mai da ake tafkawa a harkar mai da iskar gas wanda bisa ga dukkan alamu hakan ba wai a fannin mai kaɗai ya ke kawo cikas ba, har ma da ƙasa baki ɗaya. Tony Elumelu, Shugaban Kamfanin Bankin UBA kuma Shugaban…
Read More
Kasuwanci da rashin lokaci suka sa ban mallaki gidan kaina ba – Biloniya Elon Musk

Kasuwanci da rashin lokaci suka sa ban mallaki gidan kaina ba – Biloniya Elon Musk

Daga AMINA YUSUF ALI A yayin da manyan attajirai musamman a Nijeriya suke rige-rigen mallakar katafarun gidajen shiga su kwanta, ko su adana a matsayin kadara, Ba'amurken Biloniya nan Elon Musk wanda shi ne mutumin da ya fi kowa kuɗi a Duniya ya bayyana cewa, har yanzu shi ba shi da gidan kansa.  Attajirin Biloniyan a wani bidiyo da aka yi hira da shi ya bayyana cewa, shi a halin yanzu bai mallaki gidan kansa ba sai dai ya yi ta zaga gidajen abokansa yana kwana.  Elon Musk ya yi wannan tattaunawar tare da 'yan jaridu a ranar Litinin a…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Jonathan ya amince ya koma APC don takarar Shugaban Ƙasa a 2023 – Reuben Abati

Da ɗumi-ɗumi: Jonathan ya amince ya koma APC don takarar Shugaban Ƙasa a 2023 – Reuben Abati

Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Reuben Abati, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, ya shirya tsab domin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC. Abati ya ƙara da cewa Jonathan zai bayyana aniyyarsa ta takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyya mai mulki, APC nan ba da daɗewa ba. Magu ya miƙa takardar neman murabus2023: Na fi kowane ɗan takara cancantar zama shugaban ƙasa — Ngige Da ma dai wasu rahotanni sun nuna tsohon shugaban ƙasar ya gindaya sharaɗin cewa zai koma APC ne idan har za a ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023. Ko a ranar…
Read More
Buhari ya gama lalata rayuwar ‘yan Nijeriya – Hassan Mathew Kukah

Buhari ya gama lalata rayuwar ‘yan Nijeriya – Hassan Mathew Kukah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban limamin mabiya ɗariƙar Katolika da ke Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kammala lalata duk wani ɓangare na rayuwar jama’ar ƙasar a ƙarƙashin gwamnatin sa tare da bai wa cin hanci da rashawa damar haɓaka. Yayin da yake gabatar da saƙon bikin Easter a mujami’ar sa, Kukah ya ce duk wani ɓangaren rayuwar jama’ar Nijeriya ya lalace, yayin da ƙasar ta zama sashen gobe da nisa na asibiti ɗauke da tarin marasa lafiya. Limamin ya ce zukatan ‘yan Nijeriya tare da iyalansu da gidajen su da…
Read More
Wahalar ruwa: Ganduje ya bada umarnin gyara rijiyoyin burtsatsen Birnin Kano

Wahalar ruwa: Ganduje ya bada umarnin gyara rijiyoyin burtsatsen Birnin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta umarci Hukumar Samar da Ruwan Sha da Tsaftar Muhalli (RUWASSA) da ta gaggauta gyara dukkan rijiyoyin burtsatse da su ka lalace a ƙananan hukumomi takwas na cikin ƙwaryar Birnin Kano, a wani mataki na magance matsalar ruwan sha a jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abba Anwar, Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamna Abdullahi Ganduje ya fitar ranar Lahadi a Kano. Ya ce, Ganduje ya bada umarnin ne a wani taro da jami’an Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jiha, RUWASSA da kuma shugabannin ƙananan hukumomi takwas na jihar. Gwamna…
Read More
Fadar Shugaban Ƙasa ta gaskata afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame, cewar Garba Shehu

Fadar Shugaban Ƙasa ta gaskata afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame, cewar Garba Shehu

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Fadar Sugaban Ƙasa ta gaskata afuwar shugabanci da aka yi wa tsoffin gwamnoni Joshua Dariye da Jolly Nyame, tana mai faɗin afuwar ta biyo bayan tanade-tanaden dake cikin kundin tsarin mulkin ƙasa ne. Fadar ta kuma bayyana cewar, afuwar ba ta yi tsaiko ko karan-tsaye wa yaƙi da rashawa da cin hanci ba, har ila yau an zaƙulo tsofaffin gwamnonin ne da zummar yi masu afuwa bisa la’akari da yanayin lafiyar su. Tun makon da ya gabata, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya bayyana cewar, an yi wa ‘yan Nijeriya kimanin…
Read More
Ku ba mu Naira miliyan 200 cikin kuɗin tallafin fetur – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Ku ba mu Naira miliyan 200 cikin kuɗin tallafin fetur – ASUU ga Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHNAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osedeke ya ce gwamnatin tarayya har yanzu tana nuna halin ko-in-kula akan yajin aikin ASUU wanda hakan ya sa ɗaliban jami’o’in gwamnatin Nijeriya suke zaune a gidajensu. A cewarsa, gwamnati ta kawo mafita akan kuɗin tallafin man fetur da kasafin Naira tiriliyan 4 amma kuma har yanzu ba ta ce komai ba akan ilimin jami’o’inta. Farfesa Osodeke ya ce Naira biliyan 200 gwamnati za ta cire daga kuɗin kasafin tallafin man fetur, Naira tiriliyan 4, sannan ta samu rarar Naira tiriliyan 3.8 wurin kawo ƙarshen matsalolin jami'o'i.…
Read More
Kano 2023: Za mu inganta ilimi da yashe dam-dam a Jihar Kano – Balarabe Rufa’i

Kano 2023: Za mu inganta ilimi da yashe dam-dam a Jihar Kano – Balarabe Rufa’i

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano A cigaba da zagayawa, don ƙara neman goyon bayansa ga al'ummar ƙananan hukumomi 44 da suke Jihar Kano, ɗan takarar kujerar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Balarabe Rufa’i, ya alƙawaranta cewa, idan ya samu nasara zai inganta harkar ilimi da yashe dam-dam da ke akwai a jihar don inganta harkar noma da sauransu. Ya ce babu abinda ya fi a yanzu face matasa da sauran al''umma su tashi tsaye don zaɓar wanda zai kawo masu cigaba da canje-canje don cigaban yankinsu da rayuwarsu. Ɗan takarar gwamnan ya kuma ƙudurci…
Read More