Editor

9513 Posts
Yawan jarin kai tsaye da bai shafi kuɗi ba da ƙasar Sin ta zuba ya ƙaru da kashi 6.3 a rubu’i na farko

Yawan jarin kai tsaye da bai shafi kuɗi ba da ƙasar Sin ta zuba ya ƙaru da kashi 6.3 a rubu’i na farko

Daga CMG HAUSA Wasu alkaluma da ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin ta fitar jiya Alhamis sun nuna cewa, jarin kai tsaye da ƙasar ta zuba wanda bai shafi harkokin kuɗi ba, ya kai kuɗin Sin yuan biliyan 170.95 a watannin ukun farko na shekara, ƙaruwar kaso 6.3 bisa dari kan na shekarar bara. Inda aka juya zuwa dalar Amurka kuwa, jarin na ODI ya ƙaru da kashi 8.5 daga shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan 26.92. A cikin rubu’i na farko, jarin kai tsaye da bai shafi harkokin kuɗi ba da ƙasar Sin ta zuba a cikin ƙasashen da ke…
Read More
An yi jana’izar Alaafin na Oyo

An yi jana’izar Alaafin na Oyo

Daga WAKILINMU A ranar Asabar aka yi jana'izar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III a mahaifarsa Oyo. An binne basaraken ne a harabar fadar masarutar. Marigayi Lamidi Adeyemi ya rasu yana da shekara 83. Adeyemi ya rasu ne da safiyar Juma'ar da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Afe Babalola da ke Ado Ekiti. Da safiyar Asabar aka zo da gawar marigayin Oyo inda aka gudanar da wasu tanade-tanade na gargajiyaarsu kana daga bisani aka binne ta. Bayanai sun nuna marigayin ya kasance sarki mafi daɗewa a kan karagar mulki inda ya shafe shekara 52 a matsayin sarki.…
Read More
Zhao Lijian: Duniya na sane da ƙasar da ke cin ribar rikicin Rasha da Ukraine

Zhao Lijian: Duniya na sane da ƙasar da ke cin ribar rikicin Rasha da Ukraine

Daga CMG HAUSA A ranar Laraba ne hukumar MDD mai lura da ‘yan gudun hijira, ta bayyana cewa, sama da ‘yan ƙasar Ukraine miliyan 5 ne suka kwarara zuwa ƙasashen Turai makwafta, lamarin da ya haifar da gagarumar matsalar ‘yan gudun hijira. To sai dai kuma, yayin da wasu sassan ke ganin nahiyar Turai ce mafi tafka asara, tun bayan ɓarkewar rikicin Rasha da Ukraine, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce tun bayan ɓarkewar rikicin watanni 2 da suka gabata, a yanzu duniya na kara fahimtar ɓangaren da ke more riba, sakamakon rikicin. Xi ya aike…
Read More
Ka cika surutu – Munguno ya caccaki el-Rufai

Ka cika surutu – Munguno ya caccaki el-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai bai wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Shawara Kan Harkokin Tsaron Ƙasa, Babagana Munguno, ya caccaki Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed el-Rufa'i akan maganganun da yake yawan yi akan matsalar tsaro, wanda ya ce maganganun gwamnan za su iya kawo tasgaro a ƙoƙarin da ake na magance matsalar. Munguno ya bayyana hakan ne bayan wani taron majalisar tsaron ƙasa da aka yi da manyan shuwagabannin tsaro da ministoci, wanda Shugaba Buhari ya jagoranta a fadar Aso, Abuja. Sojojin Najeriya sun gama da Malam Baƙo, magajin Shugaban ISWAP ɗin da suka kashe, Al-Barnawiy Munguno…
Read More
2023: Tinubu ya yi wa gwamnatocin baya har da ta Buhari jirwaye

2023: Tinubu ya yi wa gwamnatocin baya har da ta Buhari jirwaye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jigon Jam’iyyar APC kuma mai neman tsaya wa takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa gwamnatocin da suka shuɗe da wacce ke tafiyar da mulki a yanzu jirwaye, inda ya dangwali hancin Shugaba Muhammadu Buhari da sauran tsoffin shugabannin Nijeriya a fakaice, inda ya ce, zai cika alƙawurran da shugabannin Nijeriyar suka kasa cikawa, idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa. Da ya ke magana a Legas, yayin da ya ke wa ɗaruruwan matasa jawabi waɗanda suka hallara domin nuna masa goyon baya, Tinubu ya ce, “Mu da…
Read More
Za a gudanar da gagarumin bajekolin kayayyaki a Jihar Kebbi

Za a gudanar da gagarumin bajekolin kayayyaki a Jihar Kebbi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Shirye-shirye sun kankama na soma bajekolin kayayyakin da ake sarrafawa na cikin gida da jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara ke shiryawa. Da yake magantawa a lokacin tattauna yadda bajekolin zai kasance a ɗakin taro na cibiyar ciniki da masana’antu ta jiha, Kwamishinan Ciniki, Ayukkan Noma, da Albarkatun Ƙasa na Jihar Kebbi Garba Ibrahim Geza wanda babban sakataren ma’aikatar Alhaji Ahmad Yarima Ɗakingari ya wakilta, ya bayyana cewa taron na zuwa ne bayan wanda suka gudanar tunda farko a jihar Kebbi. Tarihin kasuwanci a KanoFarfagandar ƙyamar ƙasar Sin ba za ta yi kasuwa a tsibiran…
Read More
Masalaha a PDP: Su Saraki sun yi min yankan baya, cewar Tambuwal

Masalaha a PDP: Su Saraki sun yi min yankan baya, cewar Tambuwal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu shirye-shiryen ’yan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a Arewa na masalaha ya ruguje bayan da ɗaya daga cikin masu neman jam'iyyar ta tsayar da shi takara kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi ɗaya daga cikin masu neman takarar kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, da yi masa yankan baya tare da haɗin bakin wasu. Don haka Tambuwal ɗin ya fice daga tsare-tsaren fitar da ɗan takarar na masalaha a jam'iyyar ta PDP. Ƙungiyar kamfen ɗin Tambuwal ta Tambuwal ‘Campaign Organisation’ (TCO) ce ta bayyana…
Read More
Hukumar Zakka da Waƙafi ta Sakkwato ta raba tallafi da kayan gwamnati a Yabo

Hukumar Zakka da Waƙafi ta Sakkwato ta raba tallafi da kayan gwamnati a Yabo

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato A cigaba da raba zakkar da aka tara a gundumomi da kuma raba kayan Gwamnatin Jihar Sakkwato. A ranar Talata, Shugaban Zartarwar Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya jagoranci ƙaddamar da rabon kayan gwamnatin jiha da suka haɗa buhunan abinci guda 100 da kuɗi rabin miliyan tare da kayan sallah ga marayu 100 da kuɗin ɗinki Naira 100,000 ga marayun yankin, tare da raba zakkar da gundumar ta tara ta dabbobi, abinci da kuɗi. Shugaban ya yaba wa gundumar kan wannan ƙoƙarin, kana ya yi kira a gare su da su dage da…
Read More
Gidauniyar Jema’a ta rantsar da sabbin shuwagabanni

Gidauniyar Jema’a ta rantsar da sabbin shuwagabanni

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan Gidauniyar Jema'a wadda ke da hedikwata a Kafanchan cikin Ƙaramar Hukumar Jema'a a Jihar Kaduna, ta rantsar da sabbin shuwagabannin ta da su ja ragamar gidauniyar tsawon shekara uku. An gudanar da gagarumin taron rantsar da sabbin shuwagabannin ne cikin makon nan a babbar sakandaren Isah Mohammed da ke Kafanchan, inda shugaban kwamitin zaɓen, Alhaji Adamu Makadi ya bayyana cewa rantsuwar ta biyo bayan zaɓen da aka yi ta hanyar yarjejeniyar sulhu da dukkan zaɓaɓɓu ba tare da yin zaɓe ba. A nasa jawabin dangane da taron, shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, Alhaji Bala Adamu…
Read More
Kwamishinan Ganduje ya ajiye aiki duk da ƙin amincewa da murabus ɗinsa

Kwamishinan Ganduje ya ajiye aiki duk da ƙin amincewa da murabus ɗinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ranar Laraba da ta gabata ne dai kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar Kano, Alhaji Nura Dankadai ya miƙa al’amuran gudanarwar ma’aikatarsa duk da rashin amincewar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi na murabus ɗinsa. Rahotanni sun nuna cewa a ƙarshen makon da ya gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba da wa’adi ga masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaven baɗi da su yi murabus kafin ko kuma ranar Litinin 18 ga Afrilu, kamar yadda dokar zaɓe, ta bana da aka yi wa kwaskwarima ta tanada. Kotu…
Read More