Editor

9513 Posts
Nasarorin Sin a gida na da tasirin bunƙasa haɗin gwiwar ta da ƙasashen Afirka

Nasarorin Sin a gida na da tasirin bunƙasa haɗin gwiwar ta da ƙasashen Afirka

By CMG HAUSA Mai fashin baki kan harkokin siyasa da tattalin arziki, dan ƙasar Congo (Brazzaville) Alphonse Ndongo, ya ce irin nasarorin da ƙasar Sin ke samu a cikin gida, za su ci gaba da ingiza moriyar da ake samu, daga haɗin gwiwar ta da ƙasashen Afirka. Ndongo ya bayyana hakan ne a kwanan baya, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Yana mai cewa, albarkacin ƙasar Sin, da yawa daga ƙasashen Afirka sun bunkasa, kuma Sin da ƙasashen nahiyar na ci gaba da morar juna cikin gwamman shekaru. Masanin ya ce, Afirka ta ci gajiya mai tarin yawa,…
Read More
Shugaban Nijeriya ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama da Sin ta tallafa wajen ginawa a Legas

Shugaban Nijeriya ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama da Sin ta tallafa wajen ginawa a Legas

Daga CMG HAUSA Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabon sashen sauka da tashin jiragen sama, a filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed dake birnin Ikon jihar Lagos. Yayin ƙaddamarwar, shugaba Buhari ya ce an tsara sabon sashen ne, ta yadda zai riƙa karɓar fasinjoji miliyan 20 a duk shekara, yayin da kuma zai samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye har 3,000, da kuma wasu guraben da ba na kai tsaye ba. Shugaban ya ƙara da cewa, kammalar aikin ya buɗe wani sabon babi na sufurin jiragen sama, mai cike da tsaron lafiya da…
Read More
Shugabancin APC: Gwamnoni sun yi mubaya’a ga ɗan takaran Buhari

Shugabancin APC: Gwamnoni sun yi mubaya’a ga ɗan takaran Buhari

Daga BASHIR ISAH Yayin da ya rage 'yan kwanaki ga babban taron jam'iyya, Gwamnonin jami'yyar APC sun yi mubaya'a ga ɗan takarar da Shugaba Buhari ke ra'ayin ya zama shugaban APC na ƙasa, wato Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi). Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taronsu da Shugaba Buhari ƙarkashin ƙungiyarsu ta Progressive Governors’ Forum a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Gwamna jihar Kebbi, Alhaji Bagudu Atiku, ya ce sun cimma daidaiton bambance-bambancen da ke tsakaninsu game da babban taron jam'iyyar da ke gabansu wanda zai gudana Asabar mai zuwa. Atiku ya tabbatar cewa lallai da…
Read More
Tushen Zamfara da Zamfarawa

Tushen Zamfara da Zamfarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jaridar Blueprint Manhaja ta binciko tare da tattaro bayanai daga wuraren daban-daban dangane da asalin Zamfara da Zamfarawa. Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata ɗaya daga cikin Banza Bakwai waɗanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shi ne, ana ganin Bare-bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa sun kafa asalinsu daga Maguzawa maharba waɗanda sun zauna a yankin ƙasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala. A…
Read More
Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Zargin karkatar da kuɗaɗe: Kotu ta wanke Sanata Umar Tafida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alƙalin babbar kotun Jihar Sakkwato, Mai shari’a Mohammed Mohammed a ranar Litinin ya kori shari’ar karkatar da kuɗaɗe da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu'annati (EFCC) a madadin gwamnatin tarayya ke yi wa Sanata Umar Tafida tare da sallamar Sanata Tafida babu laifi. A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Mohammed ya caccaki EFCC a matsayin mai shiga tsakani da ta ƙi yin aikinta kafin ta gurfanar da mutane a kotu. A cewar mai shari’a Mohammed, EFCC ta gaza bin ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gabatar da tuhumar da ake wa…
Read More
Taron APC: Sanata Abdullahi ya fi dacewa da shugabancin jam’iyya – Masu ruwa da tsaki

Taron APC: Sanata Abdullahi ya fi dacewa da shugabancin jam’iyya – Masu ruwa da tsaki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gabanin babban taron jam'iyyar APC mai mulki a ranar 26 ga Maris, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun jaddada goyon bayansu ga ɗan takarar shugabancin jam'iyyar kuma tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu. Ƙungiyar wacce ta ƙunshi dattawan jam’iyyar na yanzu da kuma tsoffin ’yan majalisar APC da na yanzu, da na tsohuwar jam’iyyar da kuma matasan jam’iyyar a faɗin jihohi 36 na tarayya, sun ce ya zama wajibi a bayyana matsayinsu da ranar da za a yi zaɓe, gabanin kusantowar taron. Da ya ke zantawa da wasu zaɓaɓɓun manema labarai, shugaban ƙungiyar kuma…
Read More
Babban taron APC na kasa: Shinkafi ya janye wa Adamu daga takarar shugaban jamityar APC na kasa

Babban taron APC na kasa: Shinkafi ya janye wa Adamu daga takarar shugaban jamityar APC na kasa

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau Kwanaki kaɗan gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar APC na ƙasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Maris mai zuwa, jigo a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara wanda ke neman kujerar Shugaban Jam'iyyar na Ƙasa, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, ya janye daga takararsa. Dokta Shinkafi, wanda tsohon Sakataren Jam’iyyar APGA na Ƙasa ne kafin ficewarsa zuwa Jam'iyyar APC tare da Gwamna Matawalle, ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Gusau ranar Talata. A cewarsa, janyewar tasa ya biyo bayan mayar da kujerar Shugabancin Jam'iyyar na Ƙasa zuwa yankin Arewa…
Read More
Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello: Shekaru bakwai akan karagar Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa

Mai Martaba Alhaji Ibrahim Bello: Shekaru bakwai akan karagar Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD Yana riƙe ne da sarautar Sardaunan Wonaka har zuwa ranar 9 ga Maris, 2015, da Allah ya ɗaga likkafarsa zuwa jagoran Gidan Malam Sambo Ɗan Ashafa, wanda fitaccen almajirin Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo (Muhammad Sambo Ɗan Ashafa) ne ya assasa a shekara ta 1806. Tun lokacin da aka ƙirƙiro Sarautar Sardauna a cikin tsarin Daular Sakkwato a ƙarni na 19, sannan kuma Sarkin Musulmi na wancan lokaci, wato Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Usmanu Bn Fodiyo, ya naɗa Malam Halilu bin Malam Hassan bin Usmanu bin Fodiyo a matsayin Sardaunan Sakkwato na farko kuma Sarkin Marnona (Marnona a…
Read More
Taron APC: Neman jirgin fito

Taron APC: Neman jirgin fito

Daga DR. KABIRU ABUBAKAR MAGAMA Idan akwai wani abu da na tsana a siyasa, musamman ta Nijeriya, shine biyayya, ƙwarewa da kuma sakayyar ƙoƙarin da ka yi da ke tashi a tutar babu a wajen wasu 'yan siyasa, har ga waɗanda suke ganin kansu sun fi kowa cancanta da nagarta. Wannan misalin shi zai nuna yadda wasu ke hamayya da takarar Sanata Abdullahi (Turakin Keffi) na neman Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa.  Ni ba masoyin Sanata Abdullahi Adamu ba ne, amma ku faɗi duk abinda za ku faɗa akan sa, ya yi abin a zo a gani a Jihar Nasarawa…
Read More
Taron jam’iyyar APC na ƙasa

Taron jam’iyyar APC na ƙasa

An ce, sannu ba ta hana zuwa. Mu na fatan yadda jama'a ke dako da burin ganin wannan lokaci na gangamin taron jam'iyya mai mulki APC ya zamo an gudanar da komai lafiya. Amma kuma kar mu manta a kullum akwai wasu ababe masu darajja shugaba kuma su karo mai tagomashi da ƙwaƙƙwarar ƙauna ga talakawa. Adalci idan ya wanzu mulki zai kyautatu. Amana da gaskaya ga shugaba idan sun bayyana tamkar darussa ne daga shugaba zuwa ga jama'arsa. Tausayi tare da ungo ta kyautata wa duk waɗannan ne makamashin armashi ga mai mulki domin idan an rasa waɗannan duk…
Read More