Editor

9513 Posts
Taron APC: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga ’yan jam’iyyar APC

Taron APC: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga ’yan jam’iyyar APC

Ya ku dattawanmu na APC, mun rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce, don buƙatar a gudanar da al’amura masu matuƙar muhimmanci tare da neman gyara a siyasa a babban taron jam’iyyarmu ta APC mai zuwa. Ya ku dattawanmu na jam'iyyar, mu ’Yan Ƙungiyar Masu Son Cigban APC (CAY), mu ba a haife mu a matsayin ma’asumai a siyasa ba, don haka za mu so mu bi ku da cikakken ladabi. Kafin mu cigaba da yin rubutu akan wannan batu, za mu so mu bayyana cewa, ƙungiyar matasa masu kishin APC, wacce a ƙarƙashinta mu ke rubuta wannan wasiƙa, za ta cigaba…
Read More
Rubutu da hisabin marubuta

Rubutu da hisabin marubuta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Yau za mu yi nazari ne a harkar rubutun adabi, wacce wata daɗaɗɗiyar hanya ta faɗakarwa da nishaɗantar da jama'a. Masana da manazarta da fitattun marubuta sun daɗe suna rubuce-rubuce game da tasirin harkar rubuce-rubuce ga ci gaban zamantakewa, al'adu, ilimi da cigaban rayuwar ɗan Adam. Tun tsawon zamani tarihin duniya ya zo da bayanai game da hikayoyi kan rayuwar mutanen baya, domin ɗaukar darasi kan yadda suka gina rayuwar su, kurakuran su da nasarorin su. Hatta tarihin Annabawa da bayin Allah nagari da muke karantawa a littattafan addini duk suna zuwa ne da manufar koyar…
Read More
An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa game da hukuncin kotu kan Dokar Zaɓe

An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa game da hukuncin kotu kan Dokar Zaɓe

Daga WAKILINMU An samu rarrabuwar kawuna yayin zaman sanatoci a wannan Talatar dangane da kiran da aka yi wa Majalisar Dattawa na tafka muhawara kan hukuncin da Babbar Kotu ta yanke game da haramta Sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe. Rikicin ya soma ne sa'ilin da Sanata George Sekibo daga jihar Rivers, ya dogara da doka ta 10 da ta 11 na dokokin majalisa wajen nusar da takwarorinsa irin ayyukan da suka rataya a kan sassa ukun da gwamnati ke da su, wato ƙananan hukumomi, jihohi da kuma gwamnati tarayya. Ya ce hukuncin da kotun ta yanke na sauke matakin…
Read More
‘Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da babbake ‘yarta a Ogun

‘Yan sanda sun cafke matar da ake zargi da babbake ‘yarta a Ogun

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a jihar Ogun sun cafke wata mata mai suna Aisha Tijani bisa zargin babbake 'yarta. Wacce ake zargin ta faɗa a komar 'yan sanda ne biyo bayan ƙarar da wani mai suna Moroof Ayinde ya shigar a ofishin 'yan sanda na yankin Mowe a jihar. Ayinde ya faɗa wa 'yan sanda cewa a gida ɗaya suke zaune da matar da ake zargi da babbake 'yarta 'yar shekara 10 da haihuwa. A cewarsa, matar ta fusata ne bayan da yarinyar ta ɗauki wayar da ta ƙwace daga hannun ɗaya daga cikin 'ya'yanta ta ɓoye sannan ta…
Read More
Sabon gwamnan Katsina

Sabon gwamnan Katsina

An ce mai kamar zuwa kan aika. Tun daga zaɓen 1999 wanda ya kawo gwamna marigayi Alhaji Umar Musa Yar'aduwa har zuwa gwamna Barista Alhaji Ibrahim Shehu Shema inda daga nan sai Hon Alh Aminu Bello masari wanda shi ne gwamna mai daf da miƙa ragamar mulki ga magajinsa nan da shekara ta 2023 idan rayuwarmu ta kai. Katsina ba mu zave a kan ƙabilanci ko ɓangarenci na san cewa Jam'iyyar PDP ta yi gwamnoni biyu duka daga Katsina ta tsakiya amma Jam'iyyar APC ta yi gwamna a kudanci inda wasu ke fatan ina ma wancen gudan yanki na Arewa…
Read More
2023: Matasa sun saya wa Saraki tikitin takara kan miliyan N40

2023: Matasa sun saya wa Saraki tikitin takara kan miliyan N40

Daga BASHIR ISAH A Litinin da ta gabata wata ƙungiyar matasa ta saya wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, fom ɗin takarar shugaban ƙasa domin ya yi takara a zaɓen 2023. Ƙungiyar ta ce ta cimma wannan matsaya ne saboda fahimtar da ta yi kan cewa babu ɗan siyasar da zai iya shawo kan matsalar matasan ƙasar nan in banda Bukola Saraki. A cewar shugaban ƙungiyar, Abubakar Danmusa, ƙungiyarsu ta magoya bayan Bukola Saraki ce. Ya ci gaba da cewa, sun yi imani Saraki zai iya kawo gyara ga ƙasar nan wanda hakan ya sa suka haɗa kuɗi miliyan…
Read More
Auren talaka ko mai arziki ko kuma ƙwarya ta bi ƙwarya

Auren talaka ko mai arziki ko kuma ƙwarya ta bi ƙwarya

Daga AMINA YUSUF ALI Barkan mu da sake haɗuwa a wani sabon makon, tare da sabon maudu'i a shafinku na 'Zamantakewa' na jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako mu na tafe da maudu'i a kan aurarrakin da su ke faruwa a tsakanin gidajen masu arziki da marasa ƙarfi da ya zama babban abin jin daɗi, kuma wani babban ƙalubale a wannan al'umma tamu. Shi dai zaɓen abokin aure duk da ma'aurata ko iyaye ko wasu danginsu ne suke yi, amma abin ya fi kama da rubutacciyar ƙaddarar ma'auratan. Masu iya magana da ma su. riga sun ce:…
Read More
Buhari ya amince da sake fasalin hukumar NBC

Buhari ya amince da sake fasalin hukumar NBC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin kwamitin gudanarwa ta Hukumar Yaɗa Labarai ta Ƙasa (NBC). Hakan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin tsohon kwamitin kamar yadda rahotanni suka bayyana. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Bashir Bolarinwa ne sabon shugaban kwamitin. Ya ce wani wakilin rundunar tsaro ta farin kaya (DSS), wani wakilin ma’aikatar labarai da al’adu da kuma darakta janar na hukumar su ma mambobi ne a kwamitin. Sauran mambobin su ne Wada Ibrahim, Iheanyichukwu…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta cire tallafin Naira biliyan 600 na wutar lantarki

Gwamnatin Nijeriya ta cire tallafin Naira biliyan 600 na wutar lantarki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Samar da.Wutar Lantarki a Nijeriya (NERC), ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta. Raranar Larabar da ta gabata an jiyo hukumar NERC ta na cewa tallafin shan wutar da ya ci wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 600 ya zo ƙarshe a halin yanzu. NERC ta bada sanarwar ƙara farashin shan wutar lantarki a Fabrairun wannan shekara ta 2022. An ɗauki wannan mataki ba tare da wani vata lokaci ba. Hakan na zuwa ne a lokacin da kamfanonin da ke samar da wuta su ka soki aikin NBET, suka ce kamfanin ya gagara…
Read More
2023: Yadda Mohammed Malagi ya mayar da APC tsintsiya maɗaurinki ɗaya a Jihar Neja

2023: Yadda Mohammed Malagi ya mayar da APC tsintsiya maɗaurinki ɗaya a Jihar Neja

Daga AMINA YUSUF ALI A kwanakin nan ne dai Shugaba kuma Mawallafin rukunin kamfanin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi (MIM), ya kai wata ziyara zuwa reshen Jam'iyyar APC na Jihar Neja a Minna, Babban Birnin Jihar. Wakilinmu ya rawaito cewa, wannan ziyara ta Kakakin Nufe ta buɗe wani sabon shafi a kan muradinsa na nuna sha'awarsa ga takarar Gwamnan Jihar Neja a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023.  Shigowar uban gayya:Da ƙarfe 7 na safiyar ranar Talatar, wato daidai da 22 ga watan Fabrairu shekara ta 2022, ƙofar shiga garin Minnan jihar Neja ta ɗinke da cincirindon 'yan…
Read More