21
Mar
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata mata mai suna Hajiya Hauwa Mai-kitso da ke zaune a unguwar Danbare B da ke Ƙaramar Hukumar Kumɓotso a Jihar Kano ta koka akan yadda gobara ta addabe ta. Gobarar wacce ya zuwa yanzu ba a san daga ina matsalar ta ke ba, amma al'umma sun fara hasashen cewa ko aljanin nan mai suna Batoyi ne ke haɗa mata gobarar, duba da cewa wutar ce ka tashi ba tare da wani musabbabi ba. A zantawarsa da manema labarai Hajiya Hauwa ta ce sau goma sha biyar kenan wutar na tashi, inda ta ce ko…
