19
Mar
Daga JOHN D. WADA a Lafiya Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa (NAPTIP), ta umurci duka shiyyoyin ta dake duka jihohin ƙasar nan da su fara gudanar da sintiri na musamman cikin gaggawa a yankunan su don tabbatar an cafke duka waɗanda ke safarar yara ƙanana, ciki har da waɗanda ke da hannu cikin harkokin saya da sayar da mutane don su fuskanci hukuncin doka. Darakta Janar ta hukumar, Dr. Fatima Warizi-Ari ce ta ba da umurnin a cikin wata takardar jawabin harkokin hukumar cikin shekara ɗaya, wanda daraktar ta sanya hannu sa’anan mai magana da yawun hukumar Misis…
