Editor

9513 Posts
Tsada da ƙarancin fetur: Mun kusa rufe harkar sufuri – Kamfanonin jiragen sama

Tsada da ƙarancin fetur: Mun kusa rufe harkar sufuri – Kamfanonin jiragen sama

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Nijeriya sun bayar da sanarwar yiwuwar su rufe harkokinsu na sufuri nan da kwanaki kaɗan masu zuwa. Kasancewar abokin aikin nasu na sufuri wato man fetur ya yi tsananin ƙaranci kuma farashinsa ya ƙara hauhawar fiye da ƙima. Wato ana sayar da shi a kan farashin Naira 600 kowacce lita guda.  Allen Onyema, babban jami'in zartarwa na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Airpeace shi ya bayyana haka a yayin da yake magana da yawun sauran kamfanonin jiragen saman. Ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a…
Read More
Dalilinmu na naɗa hadimin Gwamnan CBN sarautar Ɗan Amanan Bauchi – Sarkin Bauchi

Dalilinmu na naɗa hadimin Gwamnan CBN sarautar Ɗan Amanan Bauchi – Sarkin Bauchi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, ya bayyana amana a matsayin wani babban nauyi ne wanda ya jiɓanci kowane bani adam, amma kuma kaɗan ne daga cikin mutane a cikin al’umma suke iya riƙewa. Sarkin Bauchi ya bayyana cewar, fadar sa ta ɗauki tsawon lokaci tana jimamin wanda ya kamata ya ɗauki ko riƙe wannan matsayi na sarautar Ɗan Amanan Bauchi daga cikin masarautar, sai yanzu da Allah ya bayyana Dokta Ahmad Shehu a matsayin mutumin da ya dace ya riqe amanar, ba masauratar Bauchi kaɗai ba, har ma da jiha, Nijeriya da…
Read More
PDP ta buƙaci a rushe shugabacinta a Kano

PDP ta buƙaci a rushe shugabacinta a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam’iyyar PDP tsagin Aminu Wali, ta buƙaci a rushe shugabancin jamiyyar na jihar Kano. Wannan na zuwa ne a wani taron gaggawa da uwar jam’iyyar ta kasa ta gudanar tare da dukkanin ɓangarorinta a Abuja a Alhamis da ta gabata. Tsagin Aminu Wali dai ya ce a yanzu jam’iyyar na cikin wani hali, la’akari da yadda tsagin Kwankwasiyya ke neman hada shugabanci jam’iyyar da kuma inda yake son komawa ta NNPP. To sai dai kuma, da yake mayar da martani kan batun Bashir Sanata da ke zaman mai Magana da yawun jam’iyyar tsagin Kwankwasiyya ya…
Read More
Inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko

Inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko

Da ya ke tabbatar da halin rashin kula da harkokin kiwon lafiya a matakin farko ke ciki, Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko na Ƙasa, Dakta Faisal Shuaib, a ranar 14 ga Fabrairu, ya ce, sama da kashi 70 cikin 100 na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na Ƙasar (PHC) ba su da ingantattun ababen more rayuwa, magunguna da sauran abubuwan kula da lafiya. Shuaib, wanda ya yi maganar a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar da wata ƙungiyar farar hula ta ‘Connect Development’ (CODE), kan ƙarfafa al’amuran kiwon lafiya, ya kuma ce…
Read More
Sin: Makullin warware rikicin Ukraine yana hannun Amurka da NATO

Sin: Makullin warware rikicin Ukraine yana hannun Amurka da NATO

Daga CMG HAUSA Dangane da zargin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi a baya-bayan nan cewa, wai ƙasar Sin ba ta yi Allah-wadai da matakin soja da Rasha ta ɗauka ba. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Zhao Lijian, ya bayyana Alhamis din nan cewa, kalaman da ɓangaren Amurka ya yi kan ƙasar Sin kazafi ne, kuma hakan ya ƙara fallasa ra'ayin ɓangaren Amurka na yakin cacar baka da yin fito na fito. Kuma irin waɗannan kalamai ba za su taimaka wajen magance matsalar ba, kuma Sin na adawa da su matuƙa. Zhao Lijian ya…
Read More
Haɗarin matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamai

Haɗarin matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamai

Daga SAMINU HASSAN Masharhanta da dama na ci gaba da ganin baiken alaƙa, da cuɗanyar dake wakana tsakanin Amurka da yankin Taiwan na ƙasar Sin, inda sau da dama, Amurka ke sayarwa yankin na Taiwan makaman aikin soji, matakin da ya yi matuƙar sabawa dokokin ƙasa da kasa, da ƙa’idojin da ƙasashen duniya suka amincewa, da yarjejeniyoyin da ita kanta Amurka ta ƙulla tare da ɓangaren ƙasar Sin. A lokuta mabanbanta, Sin ta sha nuna rashin amincewarta da waɗannan matakai na tsoma hannu cikin harkokin gidan ta, matakin da ka iya haifar da yanayi na rashin jituwa tsakanin Sin da…
Read More
Ya dace ƙasashen yamma su gane cewa “abun da ka shuka shi za ka girba”

Ya dace ƙasashen yamma su gane cewa “abun da ka shuka shi za ka girba”

Daga CMG HAUSA Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake ƙasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Alhamis, inda kakakinta Xu Guixiang ya ce, a halin yanzu ana gudanar da taro na 49 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Geneva, inda akwai wasu ƙasashen dake kokarin jirkita gaskiya, da neman fakewa da batun kare haƙƙin bil-Adama a Xinjiang don su shafawa ƙasar Sin bakin fenti. Xu ya ce, mutuntawa gami da kare haƙƙin ɗan Adam, ba maganar fatar baki ba ce, mataki ne na zahiri. Tun bayan da aka…
Read More
Ƙasar Sin na ƙara ƙarfafa wa duniya gwiwa wajen farfaɗo da tattalin arziki

Ƙasar Sin na ƙara ƙarfafa wa duniya gwiwa wajen farfaɗo da tattalin arziki

Daga CMG HAUSA A wajen taro na musamman da kwamitin tabbatar da ci gaban harkokin hada-hadar kuɗi na majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin ya shirya a jiya Laraba, an maida martani daya bayan daya kan wasu batutuwan da suka jawo hankalin kasuwannin ƙasar, ciki har da raya tatttalin arziki daga manyan fannoni, da batun kadarorin gidaje, da sauransu. Manazarta da dama sun nuna cewa, an kira taron ne cikin lokaci, wanda ya aike da wani sako a fili cewa, gwamnatin ƙasar Sin na bakin kokarinta wajen tabbatar da raya tattalin arziki bisa hasashen da aka yi, da neman jarin waje…
Read More
Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (I)

Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nufe a Nijeriya (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yau, Jaridar Bleuprint Manhaja za ta yi duba ne kai tsaye zuwa ga asalin ƙabilar Nufawa da yadda suka fara rayuwa bayan isowarsu ƙasar Nijeriya da kuma kafuwar Masarautarsu. Nupe wasu ƙabilu ne da suke rayuwa a tsakiyar Nijeria kamar su Jihar Neja, Jihar Kwara, Jihar Kogi da Abuja, Hausawa suna kiransu da suna Banufe (ɗaya) ko Nufawa, wato masu yawa kenan. Maƙwaftansu Gwarawa suna kiran su da suna Anupeyi, kuma Yarbawa suna kiran su da suna Tapa (Takpa). Akwai wasu yaruruka sama da biyar wadda su ke ƙarƙashin Nufawa wato Kakanda, Dibo, Kupa, Gana…
Read More
Sin za ta mayar da martani idan Amurka ta nace ga saka mata takunkumi

Sin za ta mayar da martani idan Amurka ta nace ga saka mata takunkumi

Daga CMG HAUSA Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ba da amsa kan barazanar saka takunkumi da Amurka ta yi wa ƙasar Sin, a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba, inda ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana adawa da duk wani nau'i na takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata, kuma idan har Amurka ta dage kan ganin bayan ta, to ko shakka babu ƙasar Sin za ta mayar mata da martani. Kwanan nan, jami'an Amurka sun sha bayyana cewa, idan ƙasar Sin ta yi watsi da gargaɗin da Amurka ta yi mata…
Read More