Sin za ta mayar da martani idan Amurka ta nace ga saka mata takunkumi

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ba da amsa kan barazanar saka takunkumi da Amurka ta yi wa ƙasar Sin, a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba, inda ya jaddada cewa, ƙasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata, kuma idan har Amurka ta dage kan ganin bayan ta, to ko shakka babu ƙasar Sin za ta mayar mata da martani.

Kwanan nan, jami’an Amurka sun sha bayyana cewa, idan ƙasar Sin ta yi watsi da gargaɗin da Amurka ta yi mata game da taimakawa Rasha kan batun Ukraine, to za ta fuskanci mummunan sakamako.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, takunkumi bai taba zama wata hanya mai dacewa ta warware matsaloli ba, kuma ƙasar Sin za ta ci gaba da kiyaye ɗaiɗaikun hakkoki da moriyar kamfanoni da jama’arta. A yayin da take neman samun goyon baya da haɗin gwiwa daga ƙasar Sin, a daya ɓangaren kuma, Amurka ta sanyawa ƙasar Sin takunkumi, wanda hakan ba abu da za ta lamunta ba.

Ban da wannan kuma, game da kalaman ministan harkokin wajen ƙasar Rasha Sergei Lavrov kan ɗakin gwaje-gwajen kwayoyin halittu na soji na Amurka, Zhao Lijian ya bayyana cewa, ya kamata Amurka ta martaba yarjejeniyar haramta makaman masu guba, ta kuma yi ƙarin haske kan damuwar da al’ummar duniya ke nunawa kan wannan batu.

Rahotanni na nuna cewa, Sergey Lavrov ya fada a baya-bayan nan cewa, Amurka na da daruruwan ɗakunan gwaje-gwajen kwayoyyin halittu na soja a wurare daban daban na duniya, ciki har da kusan 30 a Ukraine, wanda ke yin mummunar barazana ga dimbin fararen hula.

Zhao Lijian ya kara ƙalubalantar ɓangaren Amurka, da ya canja matsayinsa na adawa da kafa tsarin bincike, yana mai nuni da cewa, hakan zai taimaka wajen dawo da amincewar ƙasashen duniya kan Amurka, na sauke nauyin da suka rataya a wuyanta kan harkokin ƙasa da ƙasa, har ila yau, zai taimaka wajen ƙarfafa matsayin kare tsaron halittun duniya.

Fassarawa: Bilkisu