Biri ya yi kama da mutum

Daga CMG HAUSA

Tun bayan da ƙasar Rasha ta bankado wasu muhimman takardu, da hotuna, gami da shaidu na zahiri game da dakunan binciken ƙwayoyin halittun Amurka dake kasar Ukraine, ɓangaren Amurka ya yi amfani da kalmar wai “bayanan ƙarya” don gyara abubuwan da suka gabata, wanda zai yi matukar wahala ta gamsar da al’ummar duniya.

A ranar 11 ga wata ne, kwamitin sulhu na MDD, ya gudanar da wani taro, don tattauna batun tsaron ƙwayoyin halittun dake dakunan gwajin da Amurka ta kafa a ƙasar Ukraine. Yayin da kwamitin na MDD ke ƙoƙarin neman karin bayani kan wannan batu, sai ita kuma wakiliyar din din din ta ƙasar Amurka a MDD Linda Thoms-Greenfield ta bayyana cewa, wai ƙasar Sin tana yada labaran karya don tallafawa ƙasar Rasha.

Sanin kowa ne cewa, Amurka a ko yaushe tana ambato “gaskiya a baki”. Amma a zahiri lamarin ba haka yake ba. Masu bibiyar al’amuran yau da kullum na cewa, Idan har Amurka ta ce, wannan “bayanan ƙarya ne”, to me ya sa ba ta ba da cikakkun bayanai don tabbatar da cewa ba ta da laifi? Ina tsabar kuɗi har dala miliyan 200 din da Amurka ta kashe? Kuma wane bincike Amurkar ta gudanar, kuma a kan waɗanne cututtuka? Waɗannan duk tambayoyi ne da duniya ke buƙatar amsoshin su daga ɓangaren Amurka. Kuma rashin bayar da gamsassun amsoshi, na iya tabbatar da cewa, akwai wani abu da Amurka ba ta son duniya ta sani game da waɗannan ɗakunan bincike. Akwai lauje cikin nadi.

Ana haka ne kuma, sai aka wari gari shi ma ofishin jakadancin Amurka a Ukraine, ya goge duk wasu bayanan da suka shafi wannan batu a shafinsa na intanet. Tambaya a nan ita ce, wai me mahukuntan Amurka suke ƙoƙarin ɓoyewa? Me ya sa Amurka ke adawa da kafa tsarin bincike na ɓangarori da dama game da yarjejeniyar makamai masu guba ta shekaru 20 da suka gabata?

Idan Amurka tana son jefar da ƙwallon mangoro da huta da ƙuda, ya kamata ta bude waɗannan ɗakunan gwaje-gwaje na kwayoyin halittu da sauran irin waɗannan ɗakunan gwaje-gwajenta kamar yadda ga tawagar masanan lafiyar ƙasa da ƙasa don gudanar da bincike a kansu. Idan ba haka ba, to, Wannan na ƙara tabbatar da cewa, Biri dai ya yi kama da mutum.

Fassarawa: Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *