Editor

9513 Posts
NDLEA ta lalata kadada 255 na gonakin tabar wiwi a Ondo

NDLEA ta lalata kadada 255 na gonakin tabar wiwi a Ondo

Daga BASHIR ISAH Mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Femi Babafemi, ya bayyana cewa jami'an hukumar sun kama tare da lalata gonakin tabar wiwi da suka girman kadada 255 a tsakanin ƙananan hukumomi biyar na jihar Ondo. Babafemi ya bayyana hakan ne cikin bayanan da ya wallafa a shafin Facebook na hukumar a ranar Laraba, inda ya ce ya ɗauki jami'an nasu mako guda suna aiki a yankin. Kazalika, ya ce sun kama mutum 13 da ake zargi da noman tabar kana an gano irin tabar mai nauyin kilogiram 250 da…
Read More
Kotun Minna ta yanke wa mutane 11 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Kotun Minna ta yanke wa mutane 11 hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Babbar Kotu mai lamba 6 dake garin Minna a cikin jihar Neja ta yanke wa waɗansu mutane 11 daga ƙaramar hukumar Lavun hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same su da ɗabagogin laifuka guda tara yayin zaman shari’ar. Kotun, ta kuma sallami wasu mutanen 15 waɗanda aka gurfanar tare da waɗanda aka yi wa hukuncin kisa, saboda rashin ƙwazo da rashin gurfanar da su bisa tsari ko ƙa’ida. Waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa sune Mohammed Mohammed, Baba Mohammed, Mohammed Isah, (wanda aka fi sani da Madu), Abubakar Saba, Mohammed Adamu Babamini, Ibrahim Mohammed…
Read More
Me ya kai Aisha Buhari zauren Majalisar Dattawa?

Me ya kai Aisha Buhari zauren Majalisar Dattawa?

Daga BASHIR ISAH Bayanan da suka riski MANHAJA a daidai wannan lokaci na nuni da cewa a karon farko, uwargidan Shugaban Ƙasa Buhari, Aisha Buhari ta ziyarci zauren Majalisar Dattawa. Ziyarar Aisha ya zuwa zauren Majlisar a yau abu ne mai cike da tarihi, kasancewar wannan shi ne karon farko da irin hakan ya taɓa aukuwa a tarihin Nijeriya inda Majalisar Dattawa ta karɓi baƙuncin matar Shugaban Ƙasa. Aisha ta halarci majalisar ne don ta shaida miƙa rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima. Majalisar ta jinkirta karɓar rahoton ne musamman don bai wa Aisha damar…
Read More
Ƙungiyar R-WIN-WIN ta gudanar da taron shawartawa kan takarar Tunubu

Ƙungiyar R-WIN-WIN ta gudanar da taron shawartawa kan takarar Tunubu

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Ƙungiyar matasa masu neman cigaba a harkar siyasa mai suna R-WIN WIN, ta gudanar da taron tattaunawa da kuma neman shawarwari a game da siyasa da kuma kakar zaɓen shekarar 2022 da ta ke tunkarowa. Taron wanda aka gudanar da shi a ranar Asabar 5 ga Fabrairu, 2022 a wajen shirya taro na Hajjo Event Center da ke titin Audu Baƙo a cikin garin Kano, ya samu halartar matasa masu yawan gaske da suka haɗar da mata da maza. Tun da farko da ya ke bayanin manufar taron da Kuma tafiyar ƙungiyar ta su. Shugaban…
Read More
Ma’aikatar Kuɗi ta ƙaryata tashin gobara a babban ofishinta na Abuja

Ma’aikatar Kuɗi ta ƙaryata tashin gobara a babban ofishinta na Abuja

Daga BASHIR ISAH Babban Ofishin Ma'aikatar Kuɗi na Ƙasa da ke Abuja, ya ƙaryata labarin da wasu kafofin yaɗa labarai suka yayata da safiyar Larab cewa gobara ta kama ofishin. Taƙaitaccen bayanin da ma'aikatar kuɗin ta wallafa a shafinta na facebook da safen nan mai ɗauke da sa hannun mai bai wa Ministar Kuɗi shawara kan harkokin labarai da sadarwa, Yunusa Tanko Abdullahi, ya nuna abin da ya faru ba gobara ba ce, ɗan akasi ne aka samu a ma'ajin batura wanda kuma tuni an shawo kan matsalar ba tare da wani jinkiri ba. Ma'ajin batura inda akasin ya auku…
Read More
‘Yan kasuwa sun fusata da sabuwar dokar CBN kan sufuri

‘Yan kasuwa sun fusata da sabuwar dokar CBN kan sufuri

Daga AMINA YUSUF ALI ’Yan kasuwa masu shigo da kaya daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya sun caccaki sabuwar dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kan harkar fatauci. Sannan kuma sun gargaɗi al'umma a kan hauhawar farashi da tsadar rayuwar ma gabaɗaya.  'Yan kasuwar sun nuna tsananin ɓacin ransu game da dokar da CBN ta kafa a kan tilas kowanne ɗan kasuwa mai shigo da kayan ƙasar waje ya yi rajista a zauren yanar gizo na CBN ɗin, sannan kuma tilas ya amince da tsarin daidaita farashi da Bankin ya tsara.  A kan haka 'yan kasuwar suke gargaɗin al'umma da su…
Read More
Koyi da Saudiyya: Za a fara fille kan masu ta’ammalli da miyagun ƙwayoyi a Kano

Koyi da Saudiyya: Za a fara fille kan masu ta’ammalli da miyagun ƙwayoyi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙudirin dokar yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, wanda ya ƙunshi kisa, ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dokoki ta Jihar Kano. Majalisar Dokokin Jihar Kano dai ta ce za ta duba yiwuwar yin wata doka kwatankwacin irin ta Ƙasar Saudiyya da za a riƙa fille kan duk wanda aka same shi da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi ko kuma safararsu.  Kakakin Majalisar Dokokin ta Jihar Kano, Rt. Hon. Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan yadda matasa da 'ya'yan masu faɗa-a-ji suke yawan ta'amilli da…
Read More
Ma’aikata ta nesanta kanta daga sanarwar bogi

Ma’aikata ta nesanta kanta daga sanarwar bogi

Daga BASHIR ISAH Ma'aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta nesanta kanta daga wata sanar da ke nuni da 'yan ƙasa su dakatar da tafiye-tafiye zuwa wasu keɓaɓɓun ƙasashen waje har zuwa ƙarshen watan Mayun 2022. Cikin sanarwar manema labarai da Ma'aikatar ta fitar a jiya Talata, ta ce sanarwar dakatar da tafiye-tafiyen ba gaskiya ba ne kuma ba daga gare ta take ba. An ga wata sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 18/02/2022 da aka yaɗa mai nuni da hana 'yan Nijeriya tafiye-tafiye zuwa ƙasashen da suka haɗa da; Belarus, Poland, Slovakia, Hungary, Romania da kuma Moldova wai har sai…
Read More
Bunƙasa harshen uwa wata dama ce ta samun ci gaba da haɗin kan al’umma

Bunƙasa harshen uwa wata dama ce ta samun ci gaba da haɗin kan al’umma

Daga FA'IZA MUSTAPHA Harshe ko yare, wata alama ce ta mutane daban-daban dake akwai a duniya. Shi ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wata rana guda, ta 21 ga watan Fabrairun kowacce shekara, a matsayin ta tunawa da muhimmancin harshen uwa ga ci gaban duniya da al’adu da cudanya tsakanin al’ummun daban-daban. Ban da haka, a ganina, karewa da kyautata amfani da harshen asali na wata ƙasa ko al’umma, na bada gagarumar taimako ga ci gaban al’umman. Misali, amfani da harshen uwa wajen koyarwa da gudanar da harkokin ƙasa, ba ƙaramin taimakawa ƙasashe masu tasowa zai yi ba wajen…
Read More