22
Feb
Daga BASHIR ISAH Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu su ne suka bayyana hakan ga manema labarai jim kaɗana bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ran Talata a Abuja. El-Rufai ya ce jami’yyar ta amince ta yi rabon muƙaman da babu kowa a kai a tsakanin yankin Arewa da Kudu gabanin babban taronta wanda zai gudana a ranar 26 ga Maris. Da alama dai jam’iyyar ta ɗauki wannan mataki ne duba da cewa tsoffin shugabannin jam’iyyar, wato John Odigie-Oyegun da kuma Adams Oshiomhole baki ɗayansu ‘yan Kudu ne, don…
