24
Feb
Mawallafin na jaridun Blueprint da Manhaja ya bada gudunmawar naira miliyan 43 da motocin safa 31 ga jam'iyya a jihar DAGA WAKILIN MU Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Jihar Neja a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi alƙawarin cewa idan har ya ci zaɓe zai kula da haƙƙin mata da matasa a gwamnatin sa. A yayin da ya ke jawabi ga shugabannin jam'iyyar lokacin da ya kai masu ziyara a ranar Talata a Minna, Malagi ya ce: "Za mu ci gaba da bai wa mata da matasa kyakkyawar kulawa kamar…
