25
Feb
Daga WAKILINMU Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika ta sanar da takwararta ta Nijeriya cewa an sauya ranakun da tawagar Super Eagles za ta kara da Black Stars ta Ghana, a wasan neman gurbin zuwa gasar kofin duniya cikin watan Nuwamba. Daraktan sadarwa na NFF, Ademola Olajire ne ya fitar da sanarwar, wadda ke cewa, “an sauya lokacin da za a buga wasannin share fagen zuwa gasar kofin duniya na Qatar 2022 tsakanin Nijeriya da Ghana.” A baya an shirya cewa Super Eagles da Black Stars za su buga gida da waje a ranakun 24 da 27 ga watan Maris. To…
