Editor

9513 Posts
Gbajabiamila ya sake taɓa zukatun jama’a a mazaɓarsa

Gbajabiamila ya sake taɓa zukatun jama’a a mazaɓarsa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Kakakin Majalisar Dokoki ta Tarayya, Femi Gbajabiamila, a ranar Asabar da ta gabata ne ya kuma rarraba tallafi wa jama’ar mazaɓar sa ta Surulere 1 da ke birnin Ikko, inda ɗimbin mutane suka amfana. A wani ƙasaitaccen shiri na miƙa hannu wa jama’ar mazaɓar sa, wanda aka gudanar a filin wasa na Teslim Balogun dake birnin Ikko, an bayar da tallafin ƙaro ilimi wa ɗalibai 351dake jami’o’in gwamnati da a halin yanzu suke karatu a sassa daban-daban na ƙasar nan, yayin da shugabannin makarantun sakandare guda 1,020 aka ba su na’urorin kwmfuta domin su sauƙaƙa…
Read More
NATO ta buƙaci gwamnati ta sa baki a batun cin mutunci mambobinta a Keffi

NATO ta buƙaci gwamnati ta sa baki a batun cin mutunci mambobinta a Keffi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ƙungiyar masu motocin sufuri ta ƙasa da aka fi sani da NATO shiyyar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, ta yi kira na musamman ga hukumomin ƙaramar hukumar ta Keffi da na jihar bakiɗaya su sa baki a batun cin mutunci da cin zarafin mambobinsu da ’yan takwararsu na ƙungiyar NURTW a ƙaramar hukumar suka yi kwanakin baya. Shugaban ƙungiyar ta NATO a ƙaramar hukumar Keffi, Aalhaji Maiwada Sidi ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke sakatariyar ƙungiyar a kan hanyar Keffi zuwa Kaduna a…
Read More
2023: INEC ta fitar da sabon jadawalin zaɓe

2023: INEC ta fitar da sabon jadawalin zaɓe

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada sanar lokacin da zaɓuɓɓukan 2023 za su kankama. Shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da sanarwar haka a wajen taron manema labarai a birnin tarayya, Abuja. A cewar Yakubu, yadda al'amarin yake a yanzu shi ne, za a gudanar da zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Ƙasa ne a ranar Asabar, 25 ga Fabrairun 2023, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokoki kuwa za su gudana ran 11 ga Maris, 2023. Yakubu ya ƙara da cewa, an tsayar da sabbin lokutan zaɓen ne daidai da…
Read More
An ɗaura auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, bayan canjin waje da lokaci

An ɗaura auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya, bayan canjin waje da lokaci

Daga WAKILINMU A jiya Juma'a aka ɗaura auren jarumar Kannywood, Aisha Muhammad Ali, da aka fi sani da Aisha Tsamiya, tare da agonta Alh Buba Abubakar. An ɗaura auren ne kamar yadda aka tsara, sai dai an samu sauyin wajen ɗaurin auren da kuma lokaci saboda dalilai na tsaro. Bayanan da Blueprint Manhaja ta kalato sun nuna an samu sauyin wuri da kuma lokacin ɗaurin auren ne kasancewar angon babban mutum ne sananne, haka ma amaryar fitacciyar jaruma ce wadda ke da ɗimbin masoya, wanda hakan ya sa aka ɗauki matakin sauyin don kauce wa duk matsalar da ka iya…
Read More
Birtaniya za ta ba wa Nijeriya Fam miliyan 10 don bunƙasa makamashi

Birtaniya za ta ba wa Nijeriya Fam miliyan 10 don bunƙasa makamashi

Daga AMINA YUSUF ALI Birtaniya ta yi alƙawarin bayar da Fam Miliyan ɗari ga sashen samar da makamashin Nijeriya. Ministan ƙasar Birtaniya a kan harkokin Afirka, Vicky Ford, ita ta ba da wannan sanarwar a ranar Litinin ɗin da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, ƙasar Birtaniyan za ta ba wa Nijeriya tallafin Fam Miliyan 10 don bunƙasa harkar makamashi.  A cewar Malama Vicky Ford, ƙasar tasu za ta ba da tallafin ne ga Nijeriya domin bunƙasar sashen makamashi na ƙasar don samar da sauƙi a kan fanshon ma'aikatan sashen da sauran al'amuran tafiyar da harkar bunƙasa makamashi a Nijeriya.…
Read More
Rasha ta fara ƙaddamar da farmaki kan Ukraine

Rasha ta fara ƙaddamar da farmaki kan Ukraine

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya sanar da ƙaddamar da ayyukan soji a kan Ƙasar Ukraine bayan share tsawon makwanni ana zaman tankiya da kuma gazawar matakai na diflomasiyya tsakanin Rasha da ƙasashen Yammacin Duniya. Shugaba Putin ya sanar da ƙaddamar da farmakin yayin wani jawabin ba zata da ya gabatar a gidan talibiji da misalin ƙarfe shida na safiyar yau agogon Rasha, inda ya buƙaci dakarun Ukraine su gaggauta ajiye makamansu musamman a yankunan da ke gabashin ƙasar ta Ukirane. Putin, ya ce, ya ɗauki wannan mataki ne domin kauce wa faruwar kisan kiyashin da mahukuntan birnin Kiev suka tsara…
Read More
Sin ta buƙaci a yi watsi da tunani irin na cacar baka game da batun Ukraine

Sin ta buƙaci a yi watsi da tunani irin na cacar baka game da batun Ukraine

Daga CRI HAUSA Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki za su yi watsi da tunani irin na cacar baka, game da taƙaddamar Ukraine, kuma su kafa wani tsarin kiyaye tsaron nahiyar Turai mai daidaito da kuma inganci, ta hanyar komawa tattaunawa da gudanar da shawarwari. Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’ar, ya ce Sin na fatan ganin dukkanin sassa, sun rungumi matakan martaba damuwar junan su ta fuskar tsaro, tare da kaucewa abubuwan da za su iya rura wutar yaƙi. Fassarawa:…
Read More
Dokar zaɓe: Buhari ya ƙi amincewa da Sashe na 84

Dokar zaɓe: Buhari ya ƙi amincewa da Sashe na 84

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna rashin amincewarsa da sashe na 84 (12) na dokar zaɓe da ya sanya wa hannu a ranar Juma'a yana mai cewa sashen ya hana wa masu riƙe da muƙaman siyasa damarsu. Buhari ya ce Dokar Zaɓen 2022 da aka yi wa kwaskwarima tana ƙunshe da alƙaura da dama na burin inganta sha'anin zaɓen ƙasar nan da kuma gabatar da sabon tsarin amfani da fasahar zamani. Yayin bikin sanya wa dokar hannu a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, Buhari ya shaida wa Majalisar Ƙasa da ta hanzarta gyara Sashe na 84 (12)…
Read More
Garkuwa: Kotu ta yanke wa Attajiri Evens ɗaurin rai-da-rai

Garkuwa: Kotu ta yanke wa Attajiri Evens ɗaurin rai-da-rai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babbar kotun Jihar Legas da ke Ikeja ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga wani hamshaƙin attajiri kuma ƙwararre a fannin garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike da aka fi sani da Evans da wasu mutane biyu, Uchenna Amadi da Okuchuwkwu Nwachukwu. Mai shari’a Hakeem Oshodi ya yanke wa mutanen uku hukuncin ne a ranar Juma’a bayan da aka same su da laifuka biyu da suka haɗa da haɗa baki da kuma yin garkuwa da wani ɗan kasuwa, Donatus Duru. Wanda lamarin ya rutsa da shi ya kasance Manajan Darakta ne na kamfanin Maydon Pharmaceuticals Ltd. Da yake…
Read More
Zaɓen 2023: Nijeriya ba za ta wargaje ba, inji Jonathan

Zaɓen 2023: Nijeriya ba za ta wargaje ba, inji Jonathan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya ce Nijeriya ba za ta wargaje ba sakamakon zaɓen 2023. Jonathan ya bayyana haka ne a wajen taron Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) na majalisar masana da kuma tsare-tsare da aka gudanar a Legas. Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa kan yadda ƙungiyar ECOWAS za ta iya magance ƙalubalen da ke fuskantar yankin. A wani labarin kuma, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce tilas ne Nijeriya ta tunkari ƙalubalen yara fiye da miliyan 13 da ba sa zuwa makaranta a ƙasar nan, domin magance mummunar…
Read More