28
Feb
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar ‘Save the Children International’ (SCI) a Nijeriya a ranar Laraba ta yi kira ga hukumomi a Nijeriya da su ɗauki ƙwararan matakai na kare yara masu nakasa. Daraktar SCI ta ƙasa, Mercy Gichuhi ta bayyana haka a cikin wata sanarwa a Abuja cewa, akwai buƙatar a haskaka halin da waɗannan yara ke ciki. Gichuhi ta ce, “taron duniya kan nakasassu da aka gudanarwa a watan Fabrairu na da nufin jawo hankalin duniya tare da mai da hankali kan wuraren da aka yi watsi da su, da dai sauransu. Ta kuma ce, yana da niyyar magance…
