Gwamna Ganduje: Shin dankali sha kushe ne..? (2)

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Cigaba daga makon jiya.

A makon jiya na tavo tarihi kan yadda tsofaffin gwamonin Jihar Kano suke ƙarke wa da Kanawa, har ma na bayar da tarihin ba a iya zarcewa a gadon mulki karo na biyu sai a baya-bayan nan cikin shekara ta 2007 lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya zarce, sai kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ma ya samu ikon zarcewa a 2019. Mun fara taɓo batun yadda Gwamna Ganduje ya ke gudanar da manyan ayyuka a jihar, amma hakan bai hana samun suka mai tsananin daga masu adawa da shi ba.

Duk lokacin da ka ji Bahaushe ya kira wani abu ko mutum da ‘dankali sha kushe’, to ya na nufin a na amfanar sa, amma kullum a na sukar sa, domin ƙarashen azancin zancen shine, ‘a na cin ka, a na kushe ka’. Bisa la’akari da yanayin gudanar da Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ganduje za a iya cewa, wannan kirari ya yi daidai da shi, amma fa ga wanda ke son yin adalci a maganarsa.

Ta yiwu wani ba zai so ma a yi wa Ganduje kirari da hakan ba, amma babu wanda zai iya shure akin da ya ke gudanarwa a zahirance ba. Mutumin nan ya gina gadojin da a tarihin Arewacin Nijeriya da ma wataƙila Nijeriya bakiɗaya ba a taɓa samun wata jiha da ta gina makamantansu ba ta fuska girma.

Tabbas shine ya gina gadojin Sabon Gari, Sabon Titi, Dangi da Bukabo, kuma ya yi nisa wajen cigaba da aikin gadar Hotoro, wacce tun kafin a kammala ta ya raɗa mata sunan Shugaba Muhammadu Buhari. Kazalika, shine ya kammala aikin gadojin ƙofofin Gadon Ƙaya da Kabuga, waɗanda tsohon Gwamnan Jihar ta Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi nisa wajen fara aikinsu.

Bugu da ƙari, Gwamna Ganduje shine Gwamnan Kano, wanda ya kafa tarihi wajen kammala ayyukan gwamnonin baya, wanda ba kasafai ’yan siyasar Nijeriya suke yin hakan ba. Sun fi yarda su ƙirƙiri sababbin ayyuka, maimakon su ɗora daga inda waɗanda suka gada suka bari. Hatta Kwankwaso, duk da irin kallon da ake yi masa na ɗan siyasa mai kishi, amma bai iya cigaba da yawancin ayyukan da ya gada daga Shekarau ba. Misali; kamar titin Yahaya Gusau, asibitocin Giginyu da Zoo Road, titin Ja’en da sauransu.

To, amma Ganduje ya haɗiye duk wata adawar siyasa da ke ransa, ya kammala kusan yawancin waɗannan ayyuka a zamaninsa. Kuma babban abin yabawa shine, hakan bai hana shi ƙirƙirar nasa ayyukan ba. A taƙaice ma dai, daga dukkan alamu zai kasance gwamna mafi ƙarancin gadar da manyan ayyuka a jihar, domin ya kusa kammala dukkan ayyukan da ya faro, duk da cewa, ya na ragowar fiye da shekara guda kafin zangon mulkinsa ya ƙare a halin yanzu.

To, sai dai kuma dole a nan mu sake nanata cewa, hakan bai hana Gwamna Ganduje fuskantar matsananciyar adawa ba. To, shin me ya janyo hakan? Wannan amsar za mu yi ƙoƙarin amsawa a makon gobe da yardar Allah.

Sai wani satin idan Allah ya yarda.