01
Mar
Daga BASHIR ISAH Yayin da ake shirin tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Ukraine, Fadar Shugaban Ƙasa ta ce 'yan Nijeriya kimanin mutum dubu huɗu haɗe da wasu 'yan Afrika da dama ne suka maƙale a Ukraine. Sanarwar da ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu a ranar 27 ga Fabrairu ta ce, "Abu ne mai daɗaɗɗen tarihi yadda 'yan Nijeriya da sauran 'yan Africa ke tafiya karatu a ƙasar Ukraine, musmaman ma don nazarin likitanci. Kuma galibin ɗaliban 'yan jami'a ne." Garba Shehu ya ci gaba da cewa wani sahihin hoton bidiyon da gwmanati…
