02
Mar
Daga CRI HAUSA Larabar nan ne, aka haɗa wutar gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 daga harsunan wuta tara zuwa ɗaya a wurin ibadar aljannar duniya da ke birnin Beijing wato Temple of Heaven. Ɗaya daga cikin harshen wutan, ya fito ne daga wurin gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta samo asali, wato Stoke Mandeville da ke ƙasar Birtaniya, daga bisani aka aika da shi zuwa birnin Beijing, don haɗa shi da sauran harsunan wutar guda 8 da suka fito daga yankunan gasar guda uku na Beijing, da Yanqing da kuma Zhangjiakou. An dai fara…
