Editor

9513 Posts
Amurka mai iƙirarin wai tana “kare haƙƙin bil Adam”

Amurka mai iƙirarin wai tana “kare haƙƙin bil Adam”

Daga CRI HAUSA Bayan harin “9.11” a shekarar 2001, Amurka ta ƙaddamar da yaƙi a Afghanistan da sunan “yaƙi da ta’addanci”. A cikin shekaru 20 da suka wuce, matakan soja da Amurka ta ɗauka a Afghanistan sun yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, a yayin da wasu sama da dubu 60 suka jikkata. Baya ga haka, kusan kaso 1/3 na al’ummar ƙasar ta Afghanistan sun kuma zama ‘yan gudun hijira. Hakan abun takaici ne, kuma abin da ya faru a Afghanistan wani ɓangare ne kawai na matsalolin da Amurka ta haifar…
Read More
Sin ta fitar da takardar bayani game da wasannin masu buƙatar musamman

Sin ta fitar da takardar bayani game da wasannin masu buƙatar musamman

Daga CRI HAUSA A Alhamis ɗin nan ne ƙasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “wasannin masu buƙatar musamman”, wadda ke ƙunshe da fashin baki game da irin ci gaban da ƙasar ta samu, a ɓangaren raya wasanni tsakanin rukumin mutane masu buƙata ta musamman. Majalissar gudanarwar ƙasar Sin ce ta fitar da takardar bayanin, kwana guda kafin buɗe gasar Olympics ta 2022, ajin masu buƙatar musamman ko Paralympic, wadda birnin Beijing ke karɓar baƙunci. Takardar bayanin ta ce, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin a shekarar 1949, ake ta samun ci gaba a fannonin kyautata rayuwar…
Read More
Gasar Paralympic ta 2021 za ta ingiza aikin raya sha’nin wasan motsa jiki na nakasassu na duniya

Gasar Paralympic ta 2021 za ta ingiza aikin raya sha’nin wasan motsa jiki na nakasassu na duniya

Daga AMINA XU An rufe gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing kwanan baya, nan da nan ne an canja na'urorin ƙauyukan Olympics dake Beijing, da garin Yan Qing da birnin Zhang Jiakou dake lardin Hebei, don dacewa da gasar Paralympic wato gasar Olympics ta nakasassu, haka nan an shirya tsaf don gudanar da gasar dake tafe. An kammala gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing lami lafiya duk da cewa cutar COVID-19 ke ci gaba da bazuwa a duniya. Hakan ya ƙara wa al'ummar duniya ƙwarin gwiwar cimma nasarar gudanar da gasa ta nasasassu da za a buɗe a…
Read More
Duk mace mai aiki tsakanin maza tana tare da ƙalubale – Laraba Ahmed

Duk mace mai aiki tsakanin maza tana tare da ƙalubale – Laraba Ahmed

"Rashin sauke haƙƙin aure ne ke sa wasu mata ɗora wa 'ya'yansu talla" Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Hajiya Labara Ahmed Kawu, Shugabar ƙungiyar nan mai zaman kanta ta 'Ahmed Kawu Hearth for Children Initiative', marubuciya da ta rubuta littafin koyon Fulatanci na 'Ekkito Fulfulde', kuma babbar sakatariya ce a aikin gwamnati, wato 'permanent Secretary' da ke hukumar kula da ƙananan hukumomi da kuma sanya ido a ofishin shugaban ma’aikata na Jihar Gombe. Gogaggiyar ma’aikaciya ce, wacce yanzu haka saura mata watanni uku ta yi ritaya. A cewar ta, ba ta da burin da ya wuce ta inganta rayuwar…
Read More
Sau 11 aka gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a Sin

Sau 11 aka gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta nakasassu a Sin

CRI HAUSA Yau Alhamis, ofishin yaɗa labarai na gwamnatin ƙasar Sin, ya fidda takardar “raya harkokin motsa jiki ta nakasassu da kare ikonsu”. Cikin takardar, an ce, ’yan wasan motsa jiki 96, za su halarci gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta nakasassu a lokacin hunturu da za a buɗe a birnin Beijing. Cikin takardar, an ce ƙasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa ga bunƙasar harkokin motsa jiki na nakasassu a fadin duniya. Daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, tawagar ’yan wasan motsa jiki ta nakasassu ta ƙasar Sin, ta halarci gasannin ƙasashen duniya guda 160, inda suka lashe…
Read More
Soyayya ce sanadiyyar fara rubutuna- MD Asnanic

Soyayya ce sanadiyyar fara rubutuna- MD Asnanic

"Marubuci mutum ne mai keɓaɓɓiyar ƙwaƙwalwa" Daga AISHA ASA Sanannen abu ne, Arewacin Nijeriya kewaye ta ke da albarkatun ƙasa da ko su kaɗai mu ka doga da su, za su iya cin ƙarfin buƙatunmu. Duk da wannan ni'ima da aka ba mu, Allah ya mana daɗɗi da baiwar ƙirƙira, musamman a tsakanin matasanmu. Muhammad Iliyass, wanda aka fi sani da MD Asnanic, matashi ne da ƙwaƙwalwarsa ke zagaya tsakanin ɓangarorin rubutu, kai har ma da na rera waƙa. A taƙaice, matashi ne mai ƙwaƙwalwar mutane da yawa. A wannan makon, shafin adabi na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ta…
Read More
Kwankwaso ya tattara komatsansa don ficewa daga PDP

Kwankwaso ya tattara komatsansa don ficewa daga PDP

Daga WAKILINMU Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa kafin ƙarshen watan Maris da ake ciki zai sauya sheƙa ya fice daga jam'iyyar PDP. Kwankwaso ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa kamar yadda kafar ta bayyana. Kwankwaso ya tabbatar da cewa ya yi nisa da shirinsa na neman sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP. Wata majiya ta kusa da jigon siyasar ta bayyana cewa, rashin tsari dangane da yadda ake tafiyar da sha'anin jam'iyyar PDP shi ne babban dalilin da ya tilasta wa Sanata Kwankwaso tattara komatsansa don ficewa daga cikinta. Idan ya tabbata…
Read More
Za mu soma fitar da fetur ba dare ba rana – NNPC

Za mu soma fitar da fetur ba dare ba rana – NNPC

Daga BASHIR ISAH Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya ce babu buƙatar 'yan Nijeriya su riƙa sayen fetur suna ɓoyewa saboda a cewarsa an tanadi wadataccen mai da za a fitar. Shugaban NNPC, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Laraba a Abuja jim kaɗan bayan ganawarsa da ƙungiyar ma'aikatan man fetur da ƙungiyar direbobi masu jigilar mai (PTD) da ƙungiyar 'yan kasuwar mai (DAPMAN) da kuma ƙungiyar manyan 'yan kasuwar mai (MOMAN). Kyari ya ce, "ba a fama da ƙarancin mai a ƙasar nan, jerin gwanon abubuwan hawa da ake gani a gidajen mai wahala ce…
Read More
Ana wata ga wata…

Ana wata ga wata…

Daga IBRAHIM YAYA A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda hukumomi da masana a fannin yaƙi da sauyin yanayi, na yin gargaɗi game da yadda yunwa za ta addabi sassan duniya. Wai ana maganar “targaɗe sai ga karaya”. Masana sun sha yin kashedi tun kafin annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba ganin irinta ba, tun a lokacin yaƙin duniya na biyu, saboda wasu dalilai. Amma duk da wannan babbar matsala da aka yi hasashen za ta kunno…
Read More
Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan ne da mugun nufi

Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan ne da mugun nufi

Daga CRI HAUSA Yau ne, tsohon sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Mike Pompeo ya ziyarci yankin Taiwan na ƙasar Sin tare da mugun nufinsa, wanda kullum yake yunƙurin zama shugaban Amurka. Nufin Mike Pompeo na ziyartar Taiwan a wannan karo, shi ne domin neman samun goyon bayan masu adawa da ƙasar Sin a Amurka da kuma ƙarfafa tasirinsa. Kwana guda kafin Mike Pompeo ya ziyarci Taiwan, gwamnatin Amurka ta aika da wata tawaga mai ƙunshe da tsoffin jami’an tsaron ƙasa zuwa Taiwan, lamarin da ya nuna cewa, dukkan jam’iyyun siyasar Amurka waɗanda suka yi mulki ko ba su yi mulki…
Read More