Editor

9513 Posts
Gasar Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing ta nuna nasarar da Sin ta cimma a fannin kare haƙƙin ɗan Adam

Gasar Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing ta nuna nasarar da Sin ta cimma a fannin kare haƙƙin ɗan Adam

Daga CRI HAUSA A daren yau ne, za a buɗe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing a hukumance, inda yan wasan motsa jiki daga ƙasashen duniya za su yi ƙoƙarin samun nasara a wannan dandali mai muhimmanci. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na ƙasa da ƙasa Andrew Parsons ya ce, masu aikin sa kai na birnin Beijing suna da himma da kwazo, yadda suke gudanar da ayyukansu, ya nuna min yadda alummar Sin suke karɓar baƙi da hannu bibbiyu. Ƙasar Sin ta duƙufa wajen shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu bisa Ƙa'idojin kare muhalli, yin…
Read More
Ƙasar Amurka ce mai kisan ƙare-dangi

Ƙasar Amurka ce mai kisan ƙare-dangi

Daga CRI HAUSA A ranar 2 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin ta fidda dogon bayani mai taken “Shaidu game da yadda ƙasar Amurka ta yi wa mazaunan India kisan ƙare-dangi”, inda ta fidda cikakkun bayanai da shaidu kan yadda ƙasar ta yi musu kisan ƙare-dangi da goge al’adunsu. Bisa ƙididdigar da aka yi, daga shekarar 1492 zuwa farkon ƙarni na 20, yawan al’ummomin Indian ya ragu matuka daga miliyan 5 zuwa dubu 250, sabo da raguwar yawan al’umma, Amurka ta tilastawa al’ummomin Indian daidaitawa da goge al’adunsu, lamarin da ya sa, ta kawar musu ’yancin kai baki ɗaya,…
Read More
Farashin gangar mai ya kai Dala 110 dalilin yaƙin Rasha da Ukraine

Farashin gangar mai ya kai Dala 110 dalilin yaƙin Rasha da Ukraine

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi zuwa Dala 110 kowacce ganga, sakamakon fargabar da ake da ita na yaƙin da ke gudana a Ukraine da kuma takunkumin karya tattalin arzikin da ƙasashen duniya ke ƙaƙaba wa Rasha. Rahotanni sun ce masu zuba jari da masu masana’antu na fargabar katsewar samun man a daidai lokacin da suke ƙoƙarin farfaɗo wa daga annobar Korona, wadda ta yi wa ƙasashen duniya illa. Yau ake sa ran ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, ta gudanar da taro domin duba yadda za a ƙara yawan man da ake kaiwa kasuwannin duniya…
Read More
Nijeriya za ta kashe Naira biliyan uku wajen kwaso ’yan ƙasar daga Ukraine

Nijeriya za ta kashe Naira biliyan uku wajen kwaso ’yan ƙasar daga Ukraine

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da kashe Dala miliyan takwas da rabi, wato fiye da Naira biliyan uku kenan, wajen aikin kwaso 'yan Nijeriya daga ƙasashe huɗu maƙotan Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi a can. Ma'aikatar harkokin waje da haɗin gwiwar ta agaji ne za su gudanar da aikin kwashe 'yan ƙasar kusan 5,000 daga ƙasashen Poland da Ramania da Slovakia da Hungary. Ƙaramin Ministan Harkokin Waje Zubairu Dada ya faɗa wa manema labarai a ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa, cewa za a tura jirage uku don gudanar…
Read More
Yadda hada-hadar cinikin ’yan wasa ke kasancewa

Yadda hada-hadar cinikin ’yan wasa ke kasancewa

Daga WAKILINMU Ƙungiyar Paris Saint-Germain ta shirya tsaf, don bai wa ɗan wasan ƙungiyar mai shekara 23 Kylian Mbappe sabon kwantiragi kan albashi mai ɗimbin yawa na Yuro 799,000 a duk mako, domin ya zauna, inda ita kuma Real Madrid ta ce, tana son sayen ɗan wasan na Faransa. Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti, mai shekara 62, ya bayar da mamaki bayan ya shiga cikin jerin waɗanda ake sa ran za a zaɓa, domin zama kocin Manchester United na gaba. Bayern Munich da Tottenham da Arsenal suna son sayen ɗan wasan bayan Middlesbrough xan ƙasar Ingila mai shekara 21, Djed…
Read More
Za mu sasanta da Sarkin Kano, don mutum ne mai dattaku – Air Peace

Za mu sasanta da Sarkin Kano, don mutum ne mai dattaku – Air Peace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban kamfanin jirgin sama na Air Peace, Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin za su ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da daɗewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru. A makon da ya gabata ne aka ɗan samu rashin jituwa tsakanin Fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace a yayin dawowar sarkin zuwa Kano da ga tafiyar da ya yi zuwa wasu ƙasashe na Afirka. Sai dai kuma Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada ƙura ba saboda ya san Sarkin Kano mutum ne…
Read More
Osinbajo da Sanwo-Olu sun ƙaddamar da kamfanonin ƙunzugun jarirai da audugar mata

Osinbajo da Sanwo-Olu sun ƙaddamar da kamfanonin ƙunzugun jarirai da audugar mata

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Juma'ar da ta gabata ne, Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu suka ƙaddamar da buɗe kamfanonin ƙunzugun mata da jarirai wanda aka yi a kan Dalar Amurka Miliyan $100. Wato sun ƙaddamar da  ƙunzugun jarirai na babban kamfanin Huggies, sannan kuma audugar mata ta kamfanin Kotqex, waɗanda aka gudanar a yankin Odogunyan dake Ikorodu, a jihar Legas. Sabon kamfanin wanda kamfanin Kimberly-Clark Nigeria, a filoti mai faɗin, 86,000m², an fara shi ne a cikin watanni 4 na ƙarshen shekarar da ta gabata, 2021. Amma matsalar dokar annobar…
Read More
Ko za a iya fille wuyan Buba Galadima?

Ko za a iya fille wuyan Buba Galadima?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Me ya sa za a fille wa mutum kai in ba da laifin da shari’a ta tabbatar da shi ba. To in ba haka ba, a bar wa kowa kansa a kan wuyarsa ya yi iya wa’adin zamansa a duniya. A nan ina son tsokaci ne kan alwashin da shaharerren ɗan siyasar hamayya a Nijeriya, Injiniya Buba Galadima ya yi cewa matuƙar shugaba Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe to a fille ma sa kai. Biyo bayan sanya hannu sai wasu musamman marubutan yanar gizo su ka riƙa tambaya shin wai yaushe za a…
Read More
Tashin gwauron zabin kayan masarufi a Nijeriya

Tashin gwauron zabin kayan masarufi a Nijeriya

Magidanta a mafi yawan jihohin Nijeriya na cigaba da ɗanɗana kuɗarsu sakamakon matsananciyar tsadar kayan abinci a kasuwannin ƙasar. Wannan kuwa na zuwa ne daidai lokacin da har yanzu al’umma ke fama da wahalar ƙarancin man fetur da kuma tsadarsa. Mutane suna ta bayyana takaici kan wannan yanayi da aka samu kai a ciki, inda batun ya zama abin tattaunawa a zauruka da dama na shafukan sada zumunta. Tuni dai farashin kayan masarufi dama sauran kayayyakin amfanin yau da kullum ya yi tashin goron zabi abin da ya sa jama'a da dama suka shiga cikin ƙuncin rayuwa. A yanzu haka…
Read More
Sin ta ciri tuta wajen tallafa wa masu buƙata ta musamman

Sin ta ciri tuta wajen tallafa wa masu buƙata ta musamman

Daga SAMINU ALHASSAN Ga duk mai bibiyar manufofin ƙasar Sin, waɗanda suka jibanci ƙara inganta rayuwar alumma, ba zai gaza lura da yadda mahukuntan ƙasar ke bullo da shirye-shirye daki-daki ba, na kyautata rayuwar sassan alummun ta masu buƙatu na musamman, da suka haɗa da masu nakasar sassan jiki, ko rashin lafiya, ko tsufa. Akwai tarin manufofi da mahukuntan ƙasar ke tsarawa, domin ganin dukkanin sassan masu buƙatar musamman a ƙasar sun more rayuwa mai inganci cike da walwala. Ga misali, ƙasar Sin ta tsara shirye shirye na musamman, domin kula da lafiyar tsofaffi, musamman wajen samar musu da hidimomin…
Read More