Editor

9513 Posts
Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja

Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja

Ma'aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja Daga BASHIR ISAH Ma'aikatan gwamnati a Jihar Neja, sun fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin biyar haƙƙinsu a wajen gwamnati. Da safiyar Laraba ma'aikatan suka fara yajin aikin bisa umarnin Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) reahen jihar, lamarin da ya haifar da tsaiko a harkokin jihar. NLC reshen jihar ta ɗauki wannan mataki ne bayan da gwamnatin jihar ta kasa cimma buƙatun mambobinta a jihar. Shugaban NLC na jihar, Idrees Lafene da takwaransa na ƙungiyar 'yan kasuwa, Ibrahim Gana, su ne suka bai wa ma'aikatan jihar unarnin shiga yakin aikin bisa abin da suka kira gazawa…
Read More
Mu yi ƙorafi, kuma mu yi haƙuri

Mu yi ƙorafi, kuma mu yi haƙuri

Daga RAHAMA ABDULMAJID A gaskiya ana jin jiki daga sama har ƙasa, tashin dala, tashin abin masarufi, ƙarancin kuɗi, ƙaruwar talauci da yunwa. Ga kuma matsalolin tsaro, dole 'yan ƙasa mu yi fushi, mu kuma harzuƙa, Yunwa da rashin tsaro abin tayar da hankula ne, babu mai ganin laifin wanda hankalinsa ya tashi saboda hakan. Don haka, wallahi ba ma ganin baikenku, hasali ma har yau ban taɓa shiga wani ɗakin taro a fadar shugaban ƙasa ba na ji ana zargin talaka don ya yi fushi ba. Sai dai ga shawarwari: Ku yi ƙorafi: Ƙorafi wani lokaci tamkar shawara ne…
Read More
Auren Dole a Kano: A zaɓa a darje

Auren Dole a Kano: A zaɓa a darje

Daga FATUHU MUSTAFA Ya kamata dai a yi mana cikakken bayani, shi wannan auren da ake so a ƙulla a jihar Kano, wai bazawara ce ko budurwa, ko ƙwaila ce za a aurar. Wa za a ba, kuma wai ma wa zai aura? Shin ma an kai kayan mun gani muna so kuwa? Ko an kai kayan banti? Allah ya sa bazawarin ko saurayin yana bayar da kuɗin toshi, ko ɗaurin kaba (in har wacce za a aurar din ta fara ƙirgar dangi). To amma wane irin aure ne ma za a yi? A ƙyanƙyara ne (auren zamani), ko auren…
Read More
Darasin haƙuri a zamantakewa (2)

Darasin haƙuri a zamantakewa (2)

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanku da jimirin karatun Manhaja. A wannan mako mun zo muku da bayani a game da yadda za a gyara aure ta hanyar yin haƙuri a gidan Malam Bahaushe. Amma fa haƙurin ta ɓangaren masu gida, wato maza. Saboda a zahirin gaskiya, rayuwar auren Bahaushe tana cike da rashin haƙuri da rashin fahimtar juna musamman kum ta fi ƙarfi a ɓangaren maza. Kuma an fi ganin mata ya kamata su yi haƙuri banda maza. A kullum idan aka samu kuskure daga namiji, sai iyaye su tursasa 'ya'yansu mata su yi haƙuri su zauna da shi, su…
Read More
Mahangar duniya tana ga mai ita

Mahangar duniya tana ga mai ita

Daga SAFIYYA JIBRIL ALIYU Yayin da malam Bahaushe a azancinsa yake kallon ta a matsayin budurwar wawa, a musulunce kuma sai ake kallon ta a Aljannar kafiri kurkukun mumini. Shi kuwa Shehin marubucin Ingilishi William Shakespeare sai ya kalle ta kacokan a dandali, fage na kafcen kwaikwayo da kowa yake da ƙofar shiga da ƙofar fita, da kuma rawar da zai taka a tsakar dandalin. To amma shi ɗan sama-Jannati Carl Sagan ya kalle ta ne kacokan a matsayin shuɗin ɗigo, mahangar da gaba ɗaya ta sa na tsunduma ciki a matsayina na 'yar Nijeriya. Tafiya nake cike da mamakin…
Read More
Bashin kuɗin wutar lantarki: Tinubu ya bada umarin biyan bashin da ke kan Fadar Villa bayan AEDC ya yi barazanar katse wutar fadar

Bashin kuɗin wutar lantarki: Tinubu ya bada umarin biyan bashin da ke kan Fadar Villa bayan AEDC ya yi barazanar katse wutar fadar

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarni kan a biya bashin kuɗin wutar lantarkin da kamfanin Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bin Fadar Shugaban Ƙasa. Wannan na zuwa ne biyo bayan sanarwar da AEDC ya fitar dangane da waɗanda yake bi bashin kuɗin wuta wanda ya haɗa da Fadar Villa da ke Abuja. Da fari dai AEDC ya fitar da wata sanarwa inda ya yi barazanar katse wutar ma'aikatu da hukumomin gwamnati su 86, ciki har da Fadar Shugaban Ƙasa muddin suka ƙi biyan bashin kuɗin wautar lantarki biliyan N47.1 da ke kansu. MANJAHA ta rawaito…
Read More
Za a yanke wutar lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa da CBN saboda bashi

Za a yanke wutar lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa da CBN saboda bashi

Daga BASHIR ISAH Kamfanin rarraba wutar lantarki, wato Abuja Electricity Distribution Company, ya ba da sanarwar zai yanke wutar lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa da Babban Bankin Nijeriya (CBN) da wasu ma'aikatu da hukumomi 85 na Gwamnatin Tarayya saboda bashin kuɗin wuta da ya kai sama da Naira biliyan 47,195 ya zuwa Disamban 2023. AEDC ya bayyana haka ne a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, 19 ga Fabrairu, 2024. AEDC ya bayyana cewa, “Hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ta bada wa'adin kwana 10 ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati 86 kan su biya bashin kauɗin wuta, N47.1bn…
Read More
Zaki ya kashe mai kula da shi a Osun

Zaki ya kashe mai kula da shi a Osun

Daga BASHIR ISAH Wani zaki ya kashe mutumin da ya yi shekara tara yana renonsa a Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Jihar Osun. Mai magana da yawun jami'ar, Abiodun Olarewaju, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin kuma a daidai lokacin da marigayin ke ƙoƙarin bai wa zakin da sauran 'yan uwansa abinci kamar yadda ya saba. An ce marigayin shi ne jami'in da ke kula da lafiyar dabbobin da ke ajiye a sashen ajiye dabbobi na jami'ar, inda ya shafe shekara tara yana kula da matashin zaƙin da ya yi ajalinsa. Bayanai sun ce kafin waɗanda…
Read More
Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero ya koma APC

Tsohon Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero ya koma APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya koma Jam'iyyar APC, watanni kaɗan bayan ficewarsa daga Jam'iyyar PDP. Ramalan Yero ya sanar da ficewar tasa ne a wani bayani da ya yi wa manema labaru, ranar Litini ta makon jiya a garin Kaduna. A bayanin nasa, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya koma APC ne bisa dalilai na ƙashin kansa bayan ya tattauna da wadanda ke kusa da shi a harkar siyasa. A cikin watan Oktoban shekarar 2023 ne Yero ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP. Ramalan Yero ya riƙe gwamnan jihar…
Read More
Kamfanoni sun kama hanyar rage farashin siminti da kaso mai ma’ana

Kamfanoni sun kama hanyar rage farashin siminti da kaso mai ma’ana

Daga BASHIR ISAH Kamfanonin siminti a Nijeriya sun amince su saukar da farashin buhun suminti mai nauyin 50kg zuwa tsakanin N7,000 da N8,000. Kamnonin sun ce za su saukar da farashin ba da ɓata lokaci ba da zarar Gwamnatin Tarayya cika shariɗin da aka cimma a yarjejeniyar da aka yi. An cimma wannan yarjejeniya tsakanin kamfanonin da lamarin ya shafa da kuma ɓangaren gwamnati ne a wajen taron da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya shirya ranar Litinin a Abuja. Uzoka-Anite ya ce gwamnati ta ba da himma wajen ganin ta daƙile dalilan da suka haifar da tashin farashin siminti…
Read More