Editor

9513 Posts
Makaɗin Hausa: Marigayi Salihu Jankiɗi (1852-1973)

Makaɗin Hausa: Marigayi Salihu Jankiɗi (1852-1973)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haifi Salihu Jankidi ne a garin Rawayya ta ƙasar Bungudu ne a yanzu cikin Ƙaramar Hukumar Gusau, wajejen shekara ta 1852. Sunan mahaifinsa Alhassan ɗan Giye ɗan Tigari mai abin kiɗi. Salihu shi ne sunansa na yanka, amma ƙanen mahaifiyarsa Kardau ya yi masa laƙabi na Jankiɗi saboda jan da Allah ya ba shi, wanda ya bi shi har bayan rasuwarsa. Alhassan Giye Ɗan Tigari: Mahaifin Jankidi Alhassan Makadi ne na kalangu kuma mai yawan yawace-yawace don kiɗa. Yakan bar garinsu Rawayya ya shiga uwa duniya don sana’arsa ta kiɗa. Shi kuma makaɗi ne na…
Read More
Kiɗa a Ƙasar Hausa

Kiɗa a Ƙasar Hausa

Daga HAFIZ ADAMU KOZA Gabatarwa: Ana zaton ɗan Adam ya fara amfani da kiɗa ne a lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma da mutane suka fara yaƙe-yaƙe a tsakaninsu, sai sana’ar kiɗa ta ƙasaita (Ibrahim, 1983:vii). Masana adabi da al'adun Hausawa suna ganin busa ita ce abu na farko da Hausawa suka fara fahimta a matsayin wani nau’i na kiɗa (Salihu, 1985:1). Hausawa mutanen farko, sun fara amfani da wannan amo don yin sadarwa da kuma faɗakarwa. Sukan yi amfani da ƙaho wajen faɗakar da junansu bisa wani abu na murna ko na tsoro…
Read More
Ƙuncin rayuwa: NLC ta nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira miliyan 1

Ƙuncin rayuwa: NLC ta nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira miliyan 1

Daga AMINA YUSUF ALI Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC ta bayyana cewar idan har tsadar rayuwar da ƙasar ke fama da shi ta ci gaba ko shakka babu ba su da zavin da ya wuce su miƙa buƙatar neman Naira miliyan guda a matsayin mafi ƙarancin albashi. A wata zantawarsa da manema labarai Mista Joe Ajaero, shugaban ƙunyiyar NLC ta yanzu, ya koka da yadda rayuwa ke ci gaba da yi wa ‘yan Nijeriya tsada tun bayan hawa mulkin shugaba Bola Tinubu sakamakon cire tallafin man fetur da wasu manufofin kuɗi da ya ce dole su ƙalubalance su. Kafin yanzu…
Read More
Ya kamata Nijeriya ta ƙara cire tallafin man fetur da na kuɗin lantarki – Bankin IMF

Ya kamata Nijeriya ta ƙara cire tallafin man fetur da na kuɗin lantarki – Bankin IMF

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai Bankin ba da lamunin Duniya (IMF) ya shawarci ƙasar Nijeriya da ta qara cire tallafin fetur da tallafin kuɗin lantarki. Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF), ya bayyana cewa, ya ba da wannan shawara ga Nijeriya na ƙara cire ɗan sauran tallafin fetur da tallafin kuɗin wutar lantarki, domin ta magance matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin ƙasar. IMF ta ce barin kuɗaɗen tallafin su ne ke ƙara damalmala tattalin arzikin Nijeriya. Bankin ya ce kuma wannan matsala ta tallafi ce ke ƙara rura wutar talauci da matsalar abinci. A cikin…
Read More
‘Yan bindiga sun kai hari hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zamfara, sun kashe DCO

‘Yan bindiga sun kai hari hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zamfara, sun kashe DCO

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu gungun ‘yan ta’adda ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Zurmi, hedikwatar karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a Lahadin da ta gabta. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Lawali Zurmi, ya tabbatar da faruwar harin ga wakilinmu a hirarsu ta wayar tarho. A cewarsa, ‘yan bindigar sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda reshen ƙaramar hukumar inda suka banka ma ofishin wuta. "Kamar yadda nake magana da kai, yanzu an ƙona ofishin 'yan sanda na sashinmu kuma yawancin jama'a sun gudu don kare lafiyarsu," in ji shi. Wakilinmu ya tattaro cewar 'yan…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Gwamnan Kwara ya faɗa komar EFCC

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Gwamnan Kwara ya faɗa komar EFCC

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwamnan Jihar Kwara State, Abdulfatah Ahmed, ya faɗa a komar Hukumar EFCC bisa zargin almundahana biliyoyin Naira a lokacin mulkinsa. News Point Nigeria ta rawaito cewa, an ga lokacin da Ahmed ya isa ofishin EFCC na Ilorin da safiyar ranar Litinin. Majiyar ta tamu ta ƙara da cewa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne don amsa mata tambayoyi dangane da yadda ya kashe kuɗaɗen da ake ya wawushe a lokacin mulkinsa a jihar. Ahmed ya yi gwamnan Kwara ne daga 2011 zuwa 2019 inda ya miƙa mulkin jihar ga Abdulrahman Abdulrazaq. Ko a shekarar 2021 EFCC…
Read More
Zan yi aiki da Sweden don cigaban Zamfara – Lawal

Zan yi aiki da Sweden don cigaban Zamfara – Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da ƙasar Sweden wajen bunƙasa ɓangarorin jihar. Ya ce fannonin jihar da za a bunƙasa sakamakon haɗin kan sun haɗa da harkar haƙar ma'adinai, fannin noma, ilimi da kuma ɓangaren makamashi. Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Jakadiyar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund a ofishinsa da ke Abuja a makon da ya gabata. Sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mai Magana da Yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, wadda aka fitar a ranar Lahadi, ta ce ziyarar Jakadiyar…
Read More
Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Oyo

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Oyo

Daga BASHIR ISAH Al'ummar garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu dangane da matsalar tsaron da ke ci wa ƙasa tuwo a ƙwarya da kuma tsadar rayuwar da 'yan ƙasa ke fama da ita. Don haka masu zanga-zangar suka yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ya magance waɗannan matsaloli domin walwalar 'yan ƙasa. Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, sun ce sun karaya da irin halin da ƙasa ke ciki, don haka suke buƙatar gwamnati ta ɗauki ingantattun matakai domin gyara. An ga matasan ɗauke da kwalaye masu ɗauke…
Read More
Ko motsa jiki na rage ƙiba?

Ko motsa jiki na rage ƙiba?

Daga AISHA ASAS Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake ce da wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar vangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma vangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki wanda lokuta da dama shi ne limamin…
Read More
Tsadar rayuwa: Mata a dinga yi wa maza uzuri

Tsadar rayuwa: Mata a dinga yi wa maza uzuri

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Allah Ya albarkace zuri'armu. A yau dai shafin iyali zai yi jan kunne ne zuwa ga mata, ko in ce rarashi, kasancewar abinda za mu yi magana kansa haƙƙinsu ne a ba su, kuma daidai ne idan sun yi bori yayin da aka hane su. Sai dai masu azancin magana na cewa, "ɗaurowa take a ɗaure alƙali." Yanayi da muka samu kanmu a yanzu ne abin duba ga kowacce mace mai hankali kafin ta zargi mijinta da rashin wadata da haƙoƙin da ya rataya kansa. Halin da muka…
Read More