Editor

9513 Posts
‘Yan bindiga sun kashe jigon APC a Filato

‘Yan bindiga sun kashe jigon APC a Filato

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Filato sun bindige kakin Jam'iyyar APC a jihar, Sylvanus Namang. Lamarin ya faru ne a garin Pankshin da ke yankin Ƙaramar Hukumar Pankshin a jihar. Majiya ta kusa da APC a jihar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da afkuwar lamarin. Tare da cewa, marigayin ya cika ne sabili da raunin da ya ji sakamakon harin da aka kai masa. Haka nan, majiyar ta ce APC za ta fitar da bayani a hukumance dangane da badaƙalar da ke tattare da mutuwar Namang. News Point Nigeria ta rawaito cewa, an harbe marigayin…
Read More
‘Yadda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da ‘yan mata tara a Zamfara

‘Yadda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da ‘yan mata tara a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu gungun 'yan bindiga sun afka wa Unguwar Mareri dake cikin Gusau, babban Birnin Jihar Zamfara a daren ran Asabar inda suka yi awon gaba da 'yan mata tara tare da wani maƙwabcinsu . Rahotanni sun nuna cewar 'yan bindigar da ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a Unguwar sunata harbe-harbe kafin su samu nasarar sace 'yan matan. Hakazalika, wakilinmu ya tattaro cewar 'yan matan da lamarin ya shafa 'yan asalin garin Anka ne cikin Ƙaramar Hukumar Anka a jihar ta Zamfara. Waɗanda abun ya rutsa da su sun haɗa da: Sanaratu Marafa,…
Read More
Za a kafa Babban Bankin Afirka a Nijeriya

Za a kafa Babban Bankin Afirka a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, a shirye Nijeriya take ta karɓi Babban Bankin Afirka bisa la'akari da ƙudirin birnin tarayya, Abuja. Tinubu ya yi wannan furuci ne sa'ilin da yake jawabi a wajen taron Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) da ke gudana a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha. Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta tattauna da dukkan waɗanda suka dace domin tabbatar da bankin ya fara aiki ya zuwa 2028 kamar yadda aka shirya. Shugaba Tinubu ya faɗa wa taron cewa, iya magance ƙalibalan Afirka na tattare ne da irin matsayar da shugabannin nahiyar…
Read More
Tambuwal ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike

Tambuwal ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike

Daga BASHIR ISAH A ranar Asabar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal, ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike mai bincike kan wasu ayyuka da gwamnatisa ta aiwatar a zamanin mulkinsa. Gwamnan Jihar, Ahmed Sokoto ne ya kafa kwamitin domin bincike kan yadda harkokin gwamnatin da ya gada suka gudana. Tambuwal ya isa gaban kwamitin ne tare da wasu muƙarrabansa, kuma rashin ba da shaidarsa ya sa kwamitin ya buƙace shi da ya sake dawowa ya zuwa wata ranar da za a sanar nan gaba. Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu ya wallafa a shafinsa na sohiyal midiya cewa, "Yau…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum tara, sun yi awon gaba da tsohon Daraktan CBN a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutum tara, sun yi awon gaba da tsohon Daraktan CBN a Kaduna

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun kashe mutum tara a mabambantan hare-hare da suka kai a yankunan ƙananan hukumomin Kauru da Igabi a Jihar Kaduna. Haka nan, sun yi garkuwa da mutum 35 ciki har da wani tsohon Daraka a Babban Bankin Nijeriya (CBN) haɗa da wani ƙanensa da matarsa. Sai kuma wasu mutum tara da suka tagayyara sakamakon hare-haren. A ranar Juma'a 'yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kwasam cikin yankin Ƙaramar Hukumar Kauru da misalin karfe 10 na dare inda suka firgita mazaun yankin da harbin bindiga. Bayanai sun ce, maharan sun yi amfani da wasu daga cikin…
Read More
Kawo ƙarshen satar ɗanyen mai a Nijeriya

Kawo ƙarshen satar ɗanyen mai a Nijeriya

A kwanakin baya ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal ta Jihar Ribas ta samu wasu mutane biyar da laifin satar man fetur da kuma safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba kuma ba tare da lasisin da ya dace ba sannan ta yanke musu hukunci daban-daban. Wannan dai na ɗaya daga cikin yawaitar satar mai da ake tafkawa a harkar mai da iskar gas wanda bisa ga dukkan alamu hakan ba wai a fannin mai kaɗai ya ke kawo cikas ba, har ma da ƙasa baki ɗaya. Tony Elumelu, Shugaban Kamfanin Bankin UBA kuma Shugaban…
Read More
NSCDC za ta haɗa kai da ƙananan hukumomi wajen samar da tsro a Jigawa

NSCDC za ta haɗa kai da ƙananan hukumomi wajen samar da tsro a Jigawa

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a kano Hukumar tsaro ta Civil Defence ta Ƙasa reshen Jihar Jigawa, ta ce za ta ci gaba da haɗa kai da ƙananan hukumomin jihar domin yaƙi da ƙalubalan tsaro a jihar. Kwamandan rundunar, Mohammed Ɗanjuma ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci Majalisar Ƙaramar Hukumar Taura a ci gaba da rangadin da yake yi a tsakanin ƙananan hukumomi 27 da jihar ke da su. Da yake jawabi a yayin ziyarar, Mohammed Ɗanjumma, ya ce sun kai ziyara ne da nufin neman haɗin kai dan ganin an tabbatar da tsaro ingantacce, a yankin Taura…
Read More
Tinubu ya ɗauki tsauraran matakai kan tsaro da yunwa

Tinubu ya ɗauki tsauraran matakai kan tsaro da yunwa

*Gwamnoni za su yi ’yan sandansu*Ya umarci shugabannin tsaro su dirar wa masu ɓoye abinci Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnoni suka amince da kafa ’yan sandan jihohi a ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ƙarshen wani taron gaggawa da shugaban ya kira a zauren majalisar da ke Fadar Shugaban Qasa a Abuja. Ministan ya ce, za a gudanar da tarurruka da dama,…
Read More
‘Yan daba sun wargaza zaɓen fidda gwani a Edo

‘Yan daba sun wargaza zaɓen fidda gwani a Edo

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa harabar Lushville Hotel and Suites da ke yankin GRA, Benin, inda nan ne wurin da aka shirya gudanar da zaɓen fidda gwani na Jam'iyyar APC don takarar gwamnan Jihar Edo. An ce sun wargaza shirin tattara sakamakon zaɓen ne inda suka kai wa wasu masu faɗa a ji farmaki tare kuma da ji wa 'yan jarida da dama rauni da farfasa musu kayan aiki. ’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya An sake buɗe Sahad Stores a Abuja bayan shafe sa’o’i 24 a rufe Jami'in tattara…
Read More
An sake buɗe Sahad Stores a Abuja bayan shafe sa’o’i 24 a rufe

An sake buɗe Sahad Stores a Abuja bayan shafe sa’o’i 24 a rufe

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPC), ta sake buɗe katafaren shagon nan na zamani, wato Sahad Stores, da ke yankin Garki a Abuja bayan rufe shi na kimanin sa’o’i 24. MANHAJA ta kalato cewar, an ga harkoki sun ci gaba da gudana a shagon yayin ziyarar da aka kai yankin a ranar Asabar. A ranar Juma’ar da ta gabata gwamnati ta garƙame shagon saboda rashin daidaito da gaskiya a farashin kayayyakinsa. Hukumar FCCPC ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar cewa, bincikenta ya gano farashin da ke rubuce a…
Read More