17
Feb
Daga BASHIR ISAH Shugabannin ƙasashen Afirka ƙarƙashin Ƙungiyar Haɗi Kan Afirka (AU) sun zaɓi Shugaban Ƙasar Mauritania, Mohamed Ould Ghazouani, a matsayin sabon shugaban AU na 2024. Ghazouani ya gaji wannan kujera ne daga Shugaba Azali Assoumani na ƙasar Comoros, wanda ya yi riƙe shugabancin ƙungiyar a 2023. ’Yan Majalisa Wakilai 60 sun buƙaci a sauya fasalin Nijeriya Bankin Access ya naɗa sabuwar Babbar jamiar zartarwar rukunin bankunan ta riƙon ƙwarya An yi zaɓen a ranar Asabar, 17 ga Fabrairu yayin babban taron ƙungiyar karo na 37 wanda ke gudana a Addis Ababa, babban birnin Habasha.
