Editor

9513 Posts
Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar cin amanar ƙasa da ta ke yi wa Sowore

Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar cin amanar ƙasa da ta ke yi wa Sowore

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar da ta ke yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyole Sowore. Gwamnatin Tarayyar ta janye tuhumar ce da ta ke yi na zargin cin amanar ƙasa a kansa a ranar Laraba 14 ga watan Faburairu. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Kotun Tarayya ta fitar a ranar Laraba 14 ga watan Faburairu. Antoni Janar na Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi shi ya miƙa takardar dakatar da tuhumar kan mamallakin gidan jaridar Sahara Reporters. Sanarwar ta ce, "Duba da sashi na…
Read More
Gwamnatin ƙasar Malta tana gayyatar ‘yan Nijeriya da su zo su yi mata aiki

Gwamnatin ƙasar Malta tana gayyatar ‘yan Nijeriya da su zo su yi mata aiki

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin ƙasar Malta da ke cikin nahiyar Turai ta ƙudiri niyyar ba da guraben aiki ga ƙwararrun 'yan wasu ƙasashen da ke wajen nahiyar ta Turai kamar dai 'yan Nijeriya. Inda suka sauƙaƙa hanyar neman ga masu neman aiki da ba 'yan ƙasar ta Malta ba. Wannan yunƙuri wani martani ne da ƙasar ta yi wanda ya biyo bayan kira da nuni da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi ga ƙasar a kan ta yi wani abu a game da matsalar ƙarancin ma'aikatanta. Tun a Janairun shekarar bana ne dai gwamnatin ƙasar Malta ta ƙirƙiro da wannan…
Read More
Hauhawar farashi laifin wa? Taron CO28 ya zo da bazata

Hauhawar farashi laifin wa? Taron CO28 ya zo da bazata

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI “Ita karya fure ta ke yi, amma ba ta ’ya’ya, amma a daka, a raya sai gaskiya”, haka ma’abota hankali suka tabbatar wa al’umar duniya. Mai karatu mun yi wannan Ambato ne domin mu jawo hankalinka ne, me ya sa daga janye tallafin man fetur a kasannan shikenan sai farashin kayayyakin masarufi sai tashin gwauron zabi yake yi babu kakkautawa. Wani abin takaici duk bayan sa’a guda sai kaji farashin kaza ya karu babu gaira babu dalili. Kuma idan k nemi ba’asi sai a ce maka dalar Amurka ce ta tashi a kasuwar duniya. Idan…
Read More
Ku yaƙi masu ɓoye abinci a ƙasa – Umarnin Tinubu ga hukumomin tsaro

Ku yaƙi masu ɓoye abinci a ƙasa – Umarnin Tinubu ga hukumomin tsaro

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bai wa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu da IGP Kayode Egbetokun da Daraktan DSS, Yusuf Bichi umarni kan su yi aiki tare da gwamnoni wajen yaki da masu boye abinci a kasa. Kafin wannan umarnin na Shugaba Tinubu, ‘yan Nijeriya na fama da karancin abinci ba wai don babu abincin ba, sai don wasu ‘yan kasuwa sun tara abincin sun boye wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci a sassan kasar. Sai dai a wani yunkuri da gwamnatin kasar ta yi don yaki da…
Read More
Hukumar Zaɓe ta Katsina ta sanar da ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi

Hukumar Zaɓe ta Katsina ta sanar da ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KATSIEC) ta saka ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin ranar gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolo a jihar. Shugaban hukumar, Lawal Alhassan Faskari ne ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki kan zaɓen wanda ya gudana a hedikwatar hukumar dake G.R.A. A cewar shi, jam'iyyu masu rajista ne kawai za a bari su tsayar da 'yan takara a kujeru daban-daban. Alhaji Lawal Alhassan ya ce sashe na 28 na dokar zaɓen Nijeriya da aka yi wa gyaran fuska 2022 ne…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu da gwamnoni sun yi ittifaƙi kan ƙirƙiro ‘yan sandan jiha

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu da gwamnoni sun yi ittifaƙi kan ƙirƙiro ‘yan sandan jiha

Daga BASHIR ISAH Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin Nijeriya sun cimma wannan matsaya ne a wata ganawa da suka yi ranar Alhamis. Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a Fadar Shugaban Ƙasa jim kaɗan bayan kammala taron gaggawar da Shugaba Tinubu ya shirya. Idris ya ce za yi tarurruka da daman gaske a kan yadda zs a tsara da kuma samar da 'yan sandan jihar a Nijeriya . A cewarsa, “Amma a yanzu ana kan tattauna batun 'yan sandan jiha. Gwamnatin Tarayya da ta jihohi suna tattauna yiwuwar samar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Kula da Fetur na shirin ɗauke muhimman sassanta zuwa Legas

Da Ɗumi-ɗumi: Hukumar Kula da Fetur na shirin ɗauke muhimman sassanta zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Man Fetur ta Ƙasa da aka fi sani da Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission a Turance, na duba yiwuwar ɗauke wasu muhimman sassanta zuwa Legas, kamar yadda wata takardar bayani wadda News Point Nigeria ta samu leƙawa ta nuna. Takardar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Fabrairu, 2024 ta ce, an yanke shawarar haka ne domin bunƙasa ayyukan hukumar, rage yawan kuɗin da hukumar ke kashewa wajen gudanar da ayyukanta da kuma tabbatar da hukumar na morar kadarorinta a Legas. A cewar takardar, “Bisa manufar bunƙasa ayyukan hukumar da cigaban masana'anta da kuma…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 9 a Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 9 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu gungun 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutum tara a kan hanyarsu ta dawowa daga bikini maulidi da ya gudana a Abuja kwanan nan. Rahotanni sun nuna waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin 'yan asalin garin Ɗangulbi ne da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar Zamfara. Yazuwa haɗa wannan rahoton, babu wani cikakken bayani game da batun. Majiyarmu ta tattaro cewar, har zuwa haɗa wannan labarin 'yan ta'addan ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka yi garkuwan da su ba. Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Alhaji Ghazali da Alhaji Hamza, Zakiru…
Read More
Rubutacciyar waƙa ta masu ilimi ce, waƙar baka kuwa ta kowa ce – Malumman Matazu

Rubutacciyar waƙa ta masu ilimi ce, waƙar baka kuwa ta kowa ce – Malumman Matazu

"Duk wanda yake yin rubutacciyar waƙa zai iya waƙar baka" Daga AISHA ASAS  A wannan satin dai ba bako shafin adabi ya kawo wa masu karatu ba, kasancewar mun saba kawo shi a bangarori da dama na adabi. Don haka za mu wuce kai tsaye ga tattaunawar.  Idan kun shirya Aisha Asas ce tare da Malumman Matazu: MANHAJA: Duk da ba ka kasance bako a jaridar Manhaja ba, za mu so mu ji takaitaccen tarihinka? MALUMMAN MATAZU: Bismillahirrahmanirrahim. Da farko dai cikakken sunana shi ne: Abdulhamid Muh'd Sani Matazu (Malumman Matazu). An haife ni a Gidan marigayi liman Malam Bala…
Read More
Mace halitta ce da Allah ya ba wa baiwa ta musamman – Salamatu Bello

Mace halitta ce da Allah ya ba wa baiwa ta musamman – Salamatu Bello

"Kaso saba'in bisa ɗari na mata na taimakon mazajensu a matsalolin gida" (Cigaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, ya ibada? Allah Ya karva, Ya sa mu a bayinSa da zai 'yanta a wannan wata mai daraja. Idan ba mu manta ba, a satin da ya gabata, mun fara tattaunawa da Salamatu Bello Abdullahi, ƙwararriyar 'yar jarida da ke gudanar da shirye-shirye masu ilimintarwa gami da nishaɗantarwa. Mun soma ne da jin tarihin rayuwarta da kuma ƙalubalen da ta fuskata a aikin jarida, sannan mun ja birki kan tambayar da muka…
Read More