Editor

9513 Posts
Zargin $6.2m kan Emefiele: Boss Mustapha ya bayyana a kotu don wanke kansa

Zargin $6.2m kan Emefiele: Boss Mustapha ya bayyana a kotu don wanke kansa

Daga BASHIR ISAH An gabatar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, a Babbar Kotu mai zamanta a Abuja dangane da shari’ar tsohon Gwanan CBN, Godwin Emefiele da ke gudana. An gurfanar da Emefiele a gaban Mai Shari’a Muazu ne kan sabbin tuhume-tuhume guda 20 da suka hada rashawa, hadin baki, amfanin da bayanan karya wajen karbar makudan kudi har $6,230,000 da sauran su. Kazalika, tuhumar ta hada da yin shigar burtu a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya wajen karbe kudi $6.2m ba bisa ka’ida ba. Da yake ba da bahasi a gaban kotu game da zargin badakalar miliyan $6.2, Mustapha…
Read More
Bayan tattaunawa da Gwamna Lawal, WAEC ta amince ta saki sakamakon ɗaliban Zamfara da ta riƙe

Bayan tattaunawa da Gwamna Lawal, WAEC ta amince ta saki sakamakon ɗaliban Zamfara da ta riƙe

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya samu amicewar Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC kan sakin sakamakon daliban sakandaren jihar da hukumar ta rike. WAEC ta rike sakamakon ne saboda bashin kudin jarrabawa sama da Naira biloyan 1.4 da take bin gwamnatin da ta gabata. Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a sanarwar da ya fitar cewar, a ranar Litinin Gwamna Lawal ya gana da shugabancin WAEC a ofishinsa da ke Abuja. Ya kara da cewa, babbar jami’ar WAEC, Hajiya Binta Abdulkadir ce ya jagoranci tawagar hukumar yayin ganawar, yayin da sauran jami’an suka hada…
Read More
Yadda manyan Arewa suka kassara cigaban yankin da al’ummarsa 

Yadda manyan Arewa suka kassara cigaban yankin da al’ummarsa 

Daga NAFI’U SALISU Idan aka yi maganar tushen tattalin arziki da tarin dukiya a Nijeriya yankin Arewa ne, haka nan idan ana maganar ƙasar noma da yin kiwo duka yankin Arewa ne aka san nan ce tushen duk wani arzikin Nijeriya. Sanannen abu ne cewa ita kanta ƙasar an gina ta ne da arzikin da yankin Arewa ke samarwa har ƙasar ta kawo zuwa wannan lokaci da arziki ya havaka bila-adadin, ta yadda masu hannu-da-shuni suka bunƙasa, suka yi ɗaukaka ta fannin kasuwanci da tara dukiya mai yawa a yankin Arewacin Nijeriya. Na daɗe ina nazari tare da lura da…
Read More
Ya kamata gwamnati ta yaƙi yunwa a ƙasa

Ya kamata gwamnati ta yaƙi yunwa a ƙasa

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Tun bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke bai wa dillalan da ke shigo da shi cikin ƙasa, rayuwar ’yan Nijeriya ta canja, musamman sakamakon ƙaruwar farashin mai wanda ya ta'azzara farashin kusan duk wani abu da talaka ke mu'amala da shi a rayuwarsa. Kama daga farashin kuɗin motar haya zuwa farashin abinci a kasuwanni, kuɗin makarantar yara da sauran al'amura na yau da kullum. Gwamnati tun a wancan lokacin ta yi ta ƙoƙarin ganin ta ɓullo da wasu tsare-tsare da za su sauƙaƙa…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 ciki har da ‘yan sanda, sun yi awon gaba da mutum 40 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 ciki har da ‘yan sanda, sun yi awon gaba da mutum 40 a Zamfara

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kashe wasu jami'an 'yan sanda biyu haɗi da wasu mutum biyu kana suka yi awon gaba da aƙalla mutum 40 a wani hari da suka kai garin Kasuwa-Daji da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda. Mazauna yankin sun ce, 'yan fashin dajin sun kai harin ne da safiyar ranar Talata tare da harba bindiga a iska don razana jama'a. Wani mai suna Abubakar Kaura ya faɗa wa jaridar News Point Nigeria cewa, 'yan bindigar su mamaye garin ne ɗauke da manyan makamai ciki har da bindigar kakkaɓo jirgin sama. Ya ƙara da…
Read More
HOTUNA: Yadda aka yi zagayen gari da kofin da Ivory Coast ta lashe a Gasar AFCON 2023

HOTUNA: Yadda aka yi zagayen gari da kofin da Ivory Coast ta lashe a Gasar AFCON 2023

A ranar Talata mazauna Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast, suka yi dafifi a wasun manyan hanyoyin birnin domin tarbar 'yan wasan kasar dauke da kofin da suka lashe a Gasar AFCON 2023 da aka kammala a Lahadin da ta gabata. Ivory Coast ta zama zakaran gasar ce bayan da ta doke Super Eagle na Nijeriya da ci 2 da 1. Ga karin hotuna daga zagayen garin da aka yi da kofin Abidjan:
Read More
Tsaftace zuciya a game da batun kishi (2)

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Masu karatu sannun ku da jimirin karanta wannan fili naku na Zamantakewa, wanda ya ke zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Kamar yadda muka fara tattaunawa a makon da ya gabata a game da zafin kishin mata da ya addabi al'umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi, to yanzu za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon da ya gabata. A sha karatu lafiya.  Abu na gaba shi ne, ya ke Uwargida ki sani: kasancewarki ta farko a wajensa…
Read More
Amarya ta yi wa angonta yankan rago a Neja

Amarya ta yi wa angonta yankan rago a Neja

Daga BASHIR ISAH Ana zargin wata amarya mai suna Aisha Aliyu a kauyen Nasarawa cikin Karamar Hukumar Lapai a Jihar Neja, da kashe mijinta Idris Ahmadu ta hanyar yi masa yankan rako. Majiyarmu ta ce Aisha ta yi ajalin angon nata ne makonni shida da yin aurensu. News Point Nigeriya ta rawaito cewar, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata da misalin karfe 1:00 na tsakar dare. Bayanai sun nuna an samu rashin jituwa a tsakanin ma’auratan da yammacin Lahadin da ta gabata, inda aka shiga tsakani aka sulhunta su. Amma bayan da dare ya tsala sai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya bai wa ’yan wasan Super Eagles tukwicin filaye da gidaje bayan dawowa daga Gasar AFCON 2023

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya bai wa ’yan wasan Super Eagles tukwicin filaye da gidaje bayan dawowa daga Gasar AFCON 2023

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya karrama ‘yan wasan Super Eagles da lambar yabo ta MON hadi da tukwicin fili da gida a birnin tarayya Abuja. Tinubu ya yi wa ‘yan wasan goma ta arzikin ne a ranar Talata a lokacin da ya karbi bakuncinsu tare da jami’an Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya (NFF) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Tawagar ta ziyarci Tinubu ne bisa jagorancin Ministan Bunkasa  Wasannin Motsa Jiki, Saenata John Owan Enoh. Wata sanarwar da ya fitar, Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar Super Eagles bisa…
Read More