Editor

9513 Posts
‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

‘Yan Arewa sama da 20,000 sun samu aikin a MTN sanadiyyar Amina Magaji Danbatta – Dr. Sarari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Ƙungiyar abokan mu'amala da kamfanin MTN a Arewa, wato Customer Acquisition Partners CAP, sun gudanar da taron karramawa ga Hajiya Amina Usman Danbatta wacce ta riƙe Babbar Manajan Kamfanin MTN a yankin arewacin Nijeriya. Taron ya gudana ne a ranar Asabar da ta gabata a Bristol Hotel da ke cikin birnin Kano. Kafin yajiye aikinta a ranar 31 ga Oktoban 2023, Hajiya Amina ta shafe shekara 21 tana aiki da Kamfanin MTN a matsayin manaja a shiyyar Arewa. Dr. Ahmad Muhammad Sarari shi ne shugaban Kamfanin Sarari Clasiq, ya bayyana cewa dauba irin gudunmwar da…
Read More
Zaɓen cike gurbi: Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa ya rantsar da mambobi biyu

Zaɓen cike gurbi: Kakakin Majalisar Dokokin Nasarawa ya rantsar da mambobi biyu

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Honorabul Danladi Jatau, ya rantsar da mambobin majalisar biyu wadanda suka lashe zaben cike gurbi wanda aka gudanar a karshen mako da ya gabata a mazabunsu. Mambobin biyu da aka rantsar su ne; Hon. Mohammed Adamu Omadefu (APC Keana) da Hon. Musa Ibrahim Abubakar (NNPP Doma ta Kudu). A jawabinsa a lokacin da yake rantsar da sabbin ‘yan majlisar a zauren majalisar da Lafiya Fadar Gwamnatin jihar, Kakakin Majalisar, Danladi Jatau, bayan ya taya 'yan majalisar murna dangane da sake mallakar kujerunsu a majalisar, ya kuma kalubalence su da…
Read More
Zargin lalata abu ne da ke faruwa a kowacce masana’antar fim – Maje El-Hajeej 

Zargin lalata abu ne da ke faruwa a kowacce masana’antar fim – Maje El-Hajeej 

"Ni ne marubucin da ya fara siyar da labari mafi tsada a Kannywood" Daga AISHA ASAS  Masana’antar Kannywood cike take da haziƙan marubuta da aka jima ana shan romon baiwar da suke da ita, duk da cewa a harkar fim suna ɗaya daga jerin mutanen ɓoye, sai dai hakan ba yana nufin muhimmancinsu ga fim kaɗan ne ba, domin marubuci shine zuciyar kowane fim.  A wannan makon, shafin Nishaɗi ya ɗauko wa masu karatu ɗaya cikin manyan marubutan da masana’antar Kannywood ke alfahari da su, hakazalika mai shirya finafinai da ya samar da finafinai na ji da faɗa a Ƙasar…
Read More
Wane ne Dr. Aliyu Ishaq Namangi?

Wane ne Dr. Aliyu Ishaq Namangi?

Daga MOHAMMED BALA GARBA Aliyu Namangi Malami ne, kuma mawaƙi mai wa'azi, wanda ya fito daga wani ƙauye mai suna Mangi a kusa da ƙaramar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, a Arewacin Nijeriya. Wakoƙinsa sun yi matuƙar tasiri wajen ilmantarwa da karantarwa game da sukar mulkin kama-karya. Sufi ne mabiyin tafarkin Sufaye.  Masana da manazarta da dama sun kawo tarihin Aliyu Namangi a aikace-aikacensu da suka gudanar, ire-iren waɗannan ayyuka na manazarta kan Aliyu Namangi sun haɗa da Skinner (1969) da Ɗangambo (1973) da Hassan (1973) da Birniwa (1989) da Yakawada (1987) da Sankalawa (2005) da Muhammad (2010) da Muhammad…
Read More
‘Ku mara mini baya don kwalliya ta biya kuɗin sabulu’ – Baffa Bello

‘Ku mara mini baya don kwalliya ta biya kuɗin sabulu’ – Baffa Bello

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a kno An buƙaci al'umar yankin Ƙaramar hukumar Minjibir da ke Jihar Kano da su bai wa Sabon kantoman riƙo na yankin ta yadda zai sami damar aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa don amfanin jama'ar yankin. Sabon kantoman riƙo na yankin Minjibir, injiniya Baffa Bello, shi ne ya buƙaci hakan a ranar Litinin jim kaɗan da karɓar ragamar aiki daga hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar mai barin gado, Hon. Sale Ado Minjibir. Kafin tabbatar Baffa Ado a matsayin sabon kantoman riƙon na shiyyar ta Minjibir, ya kasance Darkta na sashen kula da ma'aikata na hukumar yankin.…
Read More
‘Ki faɗa wa Shugaban Ƙasa akwai yunwa a ƙasa’ – Cewar Sarkin Kano ga Uwargidan Shugaban Ƙasa

‘Ki faɗa wa Shugaban Ƙasa akwai yunwa a ƙasa’ – Cewar Sarkin Kano ga Uwargidan Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya buƙaci matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da ta isar da saƙon talakawa ga Shugaban Ƙasa dangane da yunwar da ake fuskanta a ƙasa saboda tsadar rayuwa, yana mai cewa wahalar da ake sha ta yi yawa. Basaraken ya bayyana haka ne a lokacin da Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kai masa ziyara a ranar Litinin a fadarsa. MANHAJA ta kalato cewar, Oluremi ta ziyarci Kano ne domin halartar ƙaddamar da ginin Sashen Nazarin Doka a Jami'ar Maryam Abacha wanda aka yi wa ginin laƙabi da sunanta. Sarkin Kano…
Read More
Gobara ta kama ofishin ‘yan sanda a Kano

Gobara ta kama ofishin ‘yan sanda a Kano

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Kano ta ce babban ofishinta na shiyya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Nasarawa a jihar ya kama da wuta. Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar, Mr Hussaini Gumel ne ya tabbatar da afkuwar hakan ga Kamfanin Dillanci Labarai na Nijeriya (NAN) a Kano, inda ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin. A cewarsa, ‘’Gobara ta kama a hedikwatar ofishin shiyya da misalin ƙarfe 5:45 na asuba inda sashe mai yawa na ginin ya ƙone ƙurmus. ‘’Hakan ya faru ne duk kuwa da ƙoƙarin Hukumar Kashe Gobara ta yi wajen kashe…
Read More
Ƙungiyar Zaɓi Sonka ta yi gagarumin taro a Dutsen-wai

Ƙungiyar Zaɓi Sonka ta yi gagarumin taro a Dutsen-wai

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya A ranar Lahadin makon jiya, ƙungiyar zaɓi sonka da taimakon juna reshen shiyya ta ɗaya a jihar Kaduna suka yi wani babban taro da shugabanni da kuma mabobin ƙungiyar da suka fito daga kananan hukumomi takwas na shiyya ta ɗaya suka halarta da taron ya gudana a garin Dutsen Wai ta ƙaramar hukumar Kubau. A lokacin wannan taro na tsawon yini guda, mahalarta taron da suka haɗa da shugaban ƙungiyar a shiyya ta ɗaya Injiniya Garba Bala, kyauta ba ta hana arziki, Ramin Kura da Sakataren ƙungiyar Alhaji Ɗanjuma mai nama furana da kuma…
Read More
Hedikwatar tsaro ta gargaɗi ƙungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Hedikwatar tsaro ta gargaɗi ƙungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Daga WAKILINMU Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya, ta ja hankalin ƙungiyoyi masu ƙoƙarin ta'azzara al'amura a daidai lokacin da sojojin suke iya bakin ƙoƙarinsu dangane da samar da zaman lafiya yankin da ke fama da rikici a Jihar Filato. Wannan dai na ɗauke a cikin wata sanarwa da hedikwatar ta fitar mai sa hannun darektan yaɗa labaranta, Burgediya Janar Tukur Gusau ranar Litinin ɗin nan a Abuja. Birgediya General Gusau dai ya maryar da martani ne ga ƙungiyar HURIWA ta marubuta masu rajin kare haƙƙin bil'adama wadda ta soki kwamitin da aka kafa domin samo bakin zaren rikicin da ya dabaibaye…
Read More
Jaruma Fatima Sa’id ta kwanta dama

Jaruma Fatima Sa’id ta kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Allah Ya yi wa jaruma Fatima Sa’id Abdullahi da aka fi sani da Bintu a cikin shirin Ɗaɗin Kowa, rasuwa. Jarumi Abba El-Mustafa ne ya bayyana rasuwar jarumar a shafukansa na sada zumunta a ranar Lahadi. Nijeriya ta gaza lashe Kofin AFCON 2023 Shugabancin MOPPAN: Yadda Barde ya zama magajin Sarari a Kannywood Sai dai babu wani karin haske kan abin da ya yi ajalin marigayiyar. Masoyan marigayiyar daga sassa daban-daban na ci gaba da nuna alhininsu dangane da rasuwar jarumar.
Read More