Editor

9513 Posts
Namiji mai dukan matarsa

Namiji mai dukan matarsa

Daga AISHA ASAS  Idan an yi zancen namiji mai dukan matarsa a Arewacin Najeriya, ko ma ince a Ƙasar Najeriya bakiɗaya, ba a cika ɗaga kai a dube batun ba, kasancewar ta zama ruwan dare, kuma iyaye da kakani sun mata gurbi a zamantakewar aure, don haka matar da ba ta jure dukan mijinta ana sanya ta a layin marasa haƙuri. Yayin da ka ce duka ba kyau a addinin Musulunci, to fa ka janyo wa kanka abinda za a iya kiranka ɗan tawayen addini, saboda ya yi wa masu yin sa rana. Mazaje da dama suna kafa hujja da…
Read More
Nijeriya ta gaza lashe Kofin AFCON 2023

Nijeriya ta gaza lashe Kofin AFCON 2023

Daga BASHIR ISAH A ranar Lahadi aka kammala Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2023 inda aka ɓarje gumi tsakanin Nijeriya da Ivory Coast a wasan ƙarshe. A ƙarshe, Ivory Coast ce ta zo ta ɗaya a gasar bayan da ta doke Najeriya da ci 2 da 1 a wasan ƙarshe na gasar. Mai masaukin bakin ta zama zakara ne, bayan ta warware ƙwallon da Nijeriya ta jefa mata kafin tafiya hutun rabin lokaci. AFCON: Tinubu ya janye aniyyarsa ta zuwa kallon wasan Nijeriya na ƙarshe, ya wakilta Shettima a madadinsa Shettima ya taya Super Eagles murnar shiga zagayen…
Read More
Gwamna Lawal ya nuna alhini kan mutuwar Shugaban Access Holdings, Herbert Wigwe

Gwamna Lawal ya nuna alhini kan mutuwar Shugaban Access Holdings, Herbert Wigwe

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana mutuwar Babban Shugaban Kamfanin Access Holdings plc, Herbert Wigwe, a matsayin babban rashi ga masana'antar banki a Nijeriya. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar ta hannun kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ranar Lahadi a Gusau, babban birnin jihar, Lawal ya nuna alhininsa game da rasuwar Herbert Wigwe. Marigayin ya ra su ne a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi da matarsa da kuma ɗansa a California ta ƙasar Amurka. A cewar Lawal, “Da rasuwar ' Wigwe, na yi rashin aboki wanda ya bada gudummawa matuƙa…
Read More
Matsalar tsaro: Ƙabilun Nasarawa sun buƙaci a dakatar da sabuwar ƙungiyar ‘yan bangan Nomadi

Matsalar tsaro: Ƙabilun Nasarawa sun buƙaci a dakatar da sabuwar ƙungiyar ‘yan bangan Nomadi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Wata haɗakar ƙungiyoyin shugabannin matasan ƙabilu daban-daban da ake kira da Furum of Ethnic Youth Presidents a Turance a Jihar Nasarawa, ta yi kira na musamman ga Gwamnatin Tarayya ta gaugauta dakatar da ayyukan 'yan sabuwar ƙungiyar nan na 'yan bangan Nomadi da aka ƙaddamar kwanan nan a jihar. Shugaban haɗakar ƙungiyoyin, Silas Dauda Yilmi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar 'yan jarida da ke Lafiya, babban birnin jihar. Ya ce, kiran ya zama wajibi don kafa sabuwar ƙungiyar na 'yan bangan Nomadi ɗin ba shakka…
Read More
Boko Haram ta kashe sufeton ‘yan sanda da wasu mutane biyu a Borno

Boko Haram ta kashe sufeton ‘yan sanda da wasu mutane biyu a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An kashe mutane uku ciki har da wani sifeton 'yan sanda a ranar Laraba a wani sabon harin da ’yan Boko Haram suka kai a garin Kukareta da ke ƙaramar hukumar Kaga a jihar Borno. An tattaro cewa ’yan ta’addan sun ƙona jami’in ɗan sandan tare da wani gini. Sun kuma kwashe makamai da alburusai a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. An harbe wasu fararen hula biyu tare da ƙona motar hakimin gundumar tare da motar ƙirar Hilux guda ɗaya na rundunar haɗin gwiwa ta farar hula da ke aiki a wannan yankin. Tsaro: Hukumomin Abuja…
Read More
Ministocin ECOWAS sun gana a kan batun Burkina Faso, Mali da Nijar

Ministocin ECOWAS sun gana a kan batun Burkina Faso, Mali da Nijar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen Mambobin Ƙungiyar ECOWAS sun gana a ranar Alhamis a Abuja, karon farko bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun sanar da ficewarsu daga ƙungiyar, yayin da a vangare guda kuma shugaban aasar Senegal, Macky Sall ya dage babban zaɓen ƙasar. Taron Ministocin ya zama sharar-fage ga taron da shugabannin ƙasashen ƙungiyar za su yi don tunkurar waɗannan matsalolin. Gwamnatin Zamfara ta fara biyan tsoffin ma’aikatanta bashin giraduti na N13.4bn Taron, kamar yadda wata sanarwar da ƙungiyar ECOWAS din ta wallafa a shafinta na intanet ta nuna, taro ne na musamman…
Read More
Jami’ar Aliko Ɗangote ta dakatar da malamin da ya sa ɗalibai gwale-gwale

Jami’ar Aliko Ɗangote ta dakatar da malamin da ya sa ɗalibai gwale-gwale

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar da wani malami bisa sanya wasu ɗalibai tsallen-kwaɗo da ɗaga hannu a aji. Daily Nigerian ta rawaito cewa wani faifan bidiyo ya nuna yadda wani malami ya saka wasu ɗalibai tsallen-kwaɗo ana tsaka da darasi a aji. Bidiyon ya haifar da cecekuce da kuma alla-wadai da ga mabiya shafukan sadarwa. Sai dai hukumar jami’ar, a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sa’idu Nayaya ta ce tuni jami’ar ta ɗauki matakin dakatar da wannan malami. Jami’ar…
Read More
Tsaro: Hukumomin Abuja sun bai wa masu zama ƙasan gada wa’adin tashi

Tsaro: Hukumomin Abuja sun bai wa masu zama ƙasan gada wa’adin tashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar kula da birnin Abuja ta bai wa ɗaruruwan mutane da ke zama a ƙarƙashin gadojin da ke birnin mako guda su tashi ko kuma su fuskanci fushin hukumar. Mai taimaka wa ministan birnin na Abuja kan muhalli da kawar da shara, Fred Kpakol ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon koken da mazauna birnin ke yi kan ƙwace da fashi da ake yi wa al'umma. Fred Kpakol ya ce gadojin da ake fuskantar wannan mastaala da aka umarci waɗanda ke zaune a kasansu sun haɗa da gadojin unguwannin Garki, Wuse II, Maitama, da…
Read More
Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

Hauhawar Farashi: Dole gwamnoni su sauke nauyin da ke kansu – Fasua

Daga WAKILINMU An nuna buƙatar da ke gwamnonin jahohin ƙasar su duba tare da sauke nauyin al'umma da ya ɗauru a kansu domin samun daidaiton rayuwa Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan sha'anin tattalin arziki, Mr Tope Fasua ne ya yi wannan kira. A cewarsa, ya zama wajibi gwamnonin jihohi su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar amfani da kuɗaɗen da gwamati ke ba su wajen biyan basussukan albashi, fansho, haƙƙoƙin ‘yan kwangila da tallafi. Tope ya ci gaba da cewa, “A ƙarshen makon nan na yi bincike a kasuwanni kan hauhawar farashin ababen masarufi, abin…
Read More
Yadda ake tunkarar tsadar rayuwa a Nijeriya

Yadda ake tunkarar tsadar rayuwa a Nijeriya

*Kotu ta tsoma baki*Bankin CBN ya yi bayani*Jiga-jigan gwamnati sun rufe ƙofa*Shin zanga-zanga mafita ce? Daga MAHDI M. MUHAMMAD Matsalar tsadar rayuwa ta zama babban abinda a yau a Nijeriya aka fi tattaunawa a kai, saboda yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabo a kullum, yayin da talakawan ƙasar ke faɗi-tashin ganin sun tsira daga yanayin sakamakon yadda ƙarancin abin hannu ke cigaba da ta’azzara. A ɗaya ɓangaren kuwa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta na iƙirarin cewa, lallai ta na yin iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan lamarin, wanda masana da masu nazari da dama…
Read More