Editor

9513 Posts
Matasa mu kama sana’a

Matasa mu kama sana’a

Assalamu alaikum. Haƙiƙa ba ƙaramin tashin hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takamaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin  hakan ne ke sa ɗimbin matasa aukawa cikin miyagun ayyuka irin su; sace-sace da shaye-shaye da bangar siyasa da sauransu. A wani ɓangaren ma sana’a ta fi muhimmanci fiye da wani ilimin, dalili shi ne sau tari matasa da yawa masu ilimi sukan yi amfani da iliminsu ta hanyoyin da ba su dace ba, sakamakon rashin sana’a inda wani lokacin ma ba za ka iya bambance matashi mai ilimi da marar ilimi…
Read More
Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

Kira ga gwamnati kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya

Nijeriya dai wata babbar ƙasa ce a yammacin Afrika, wacce Allah ya albarkace ta da tarin ni'imomi da albarkatu masu yawa. Kama daga yawan jama'a da suka haura miliyan 200, da kuma ma'adinan ƙarƙashin ƙasa, na ruwa da na kan tudu, wanda ba kowacce ƙasa ce Allah ya bai wa wannan arzikin ba. Sai dai kuma ƙalubale iri iri da suka haɗa da rashin shugabanci nagari, cin hanci da rashawa, ƙabilanci da ɓangaranci, da kuma uwa uba matsalar tavarvarewar tsaro. Sai dai duk da ƙoƙarin da masu riƙe da madafun iko, ƙwararru da rundunonin tsaron ƙasa suke cewa suna yi…
Read More
Sai da aka sace ni na fara goyon bayan kuɗin fansa – Tsohon daraktan DSS

Sai da aka sace ni na fara goyon bayan kuɗin fansa – Tsohon daraktan DSS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mista Mike Ejiofor, ya bayyana cewa, tunaninsa na ƙin biyan kuɗin fansa na garkuwa da mutane ya canja bayan da a ka sace shi da kansa. Duk da cewa ya yi watsi da batun biyan kuɗin fansa, ya jaddada cewa taɓarɓarewar tattalin arzikin da ake fama da shi a ƙasar nan na sa mutane shiga harkar garkuwa da mutane a matsayin wata hanyar samun kuɗin shiga. Ejiofor ya amince da damuwar da ake samu game da ƙaruwar satar mutane tare da jaddada buƙatar samar da hanyoyin da za…
Read More
Shugaban Bankin Access da iyalinsa sun mutu a hatsarin jirgin sama a Amurka

Shugaban Bankin Access da iyalinsa sun mutu a hatsarin jirgin sama a Amurka

Daga BASHIR ISAH Shugaban Bankin Access kuma Shugaban Kamfanin Acess Holdings, Hebert Wigwe, ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya rutsa da shi a Amurka. Matarsa da ɗansa da wasu pasinjoji uku na daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su wanda baki ɗaya sun riga mu gidan gaskiya. Hatsarin ya faru ne a birnin California na ƙasar Amurka. MANHAJA ta kalato cewa, marigayan sun shiga jirgin ne da nufin zuwa kallon wasan ƙwallon ƙafar da Super Bowl za ta buga a Las Vegas. Jaridar New York Times ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba…
Read More
AFCON: Tinubu ya janye aniyyarsa ta zuwa kallon wasan Nijeriya na ƙarshe, ya wakilta Shettima a madadinsa

AFCON: Tinubu ya janye aniyyarsa ta zuwa kallon wasan Nijeriya na ƙarshe, ya wakilta Shettima a madadinsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya janye niyyarsa ta zuwa kallon wasan karshe da Nijeriya za ta kara da Côte d’Ivoire a gasar AFCON 2023 da ke gudana a kasar Côte d’Ivoire.  Maimakon haka, Tinubu ya wakilta Mataimakin Shugaban Kasa,  Kashim Shettima kan ya jagoranci tawagar Shugaban Kasa zuwa wajen kallon wasan wanda za a buga a ranar Lahadi. Hadimin Shugaban Kasa kan sha’anin yada labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, shi ne ya  bayyana haka  a ranar Asabar. MANHAJA ta rawaito da fari cewar, Tinubu zai halarci kallon wasan na karshe da Nijeriya za ta buga da Côte…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta fara biyan tsoffin ma’aikatanta bashin giraduti na N13.4bn

Gwamnatin Zamfara ta fara biyan tsoffin ma’aikatanta bashin giraduti na N13.4bn

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamma Dauda Lawal ta fara biyan tsoffin ma’aikatan jihar bashin giraduti na Naira biliyan 13.4 da suke bin jihar. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Asabar, Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya ce, gwamnati ta kafa kwamitin musamman da ke aikin tantance ma’aikatan da suka yi ritaya domin a biya su bashin giraduti da suke bi daga 2011 zuwa yau. Idris ya kara da cewa, an tantance bashin giradutin na shekaru da tsoffin ma’aikatan ke bi, kuma tuni an fara biyan su tun daga ranar Alhamis da ta…
Read More
Yadda farashin kayan gwari ke hauhawa a Kebbi

Yadda farashin kayan gwari ke hauhawa a Kebbi

Daga Jamil Gulma a Birnin Kebbi Kayan gwari waɗansu kayan amfanin gona ne da mafi akasarinsu a kan sarrafa su ne a miya, waɗanda kuma ke da lokacin araha da kuma tsada da suka haɗa da tumatir, ataruhu, tattasai, albasa kabeji, sure ko yakuwa (taushe) alayyafo, guro, kabushi da dai sauransu. Ana noma kayan gwari a yankunan arewacin Nijeriya, musamman a vangarorin da ke da fadama ko dausayi da qoramu, inda kusan kowacce jiha a Arewa akwai wani yanki da a ke iya samun su, sai dai kawai waɗansu yankunan sun fi waɗansu. Tsadar kayan masarufi ba sabon abu ba…
Read More
AFCON: A ranar Lahadi Nijeriya za ta haɗu da Ivory Coast a wasan ƙarshe

AFCON: A ranar Lahadi Nijeriya za ta haɗu da Ivory Coast a wasan ƙarshe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tawagar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya ta Super Eagles za ta haɗu da mai masaukin baƙi Ivory Coast a wasan ƙarshe na kofin nahiyar Afrika bayan nasararorin da ƙasashen biyu suka samu a wasanninsu na daren Laraba, wasan ƙarshen da zai gudana a ranar Lahadi 11 ga watan Fabarairu. Nijeriya dai ta doke Afrika ta kudu ne da ƙwallaye 4 da 2 a bugun fenariti yayin wasan daf da ƙarshe ƙarƙashin gasar ta AFCON, nasarar da ta kawo ta wannan mataki na wasan ƙarshe wanda rabonta da kai wa tun a shekarar 2013 wanda kuma ta lashe kofin…
Read More
NLC da TUC sun ba gwamnati wa’adin shiga yajin aiki

NLC da TUC sun ba gwamnati wa’adin shiga yajin aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabbin rufewar tattalin arziki na kara kunno kai yayin da NLC da TUC suka fitar da sanarwar yajin aikin kwanaki 14 a fadin kasar. Wani sabon durƙushewar tattalin arziki na ƙara kunno kai a daidai lokacin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya NLC da kuma TUC suka fitar da sanarwar shiga yajin aiki na tsawon kwanaki 14 ga gwamnatin tarayya. Ƙungiyoyin sun fitar da sanarwar ne a cikin wata sanarwa da suka fitar jiya Alhamis, 8 ga Fabrairu, 2024. Ƙungiyoyin sun bayyana cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar mai ɗauke da abubuwa 16 da aka…
Read More
AFCON 2023: Tinubu zai halarci kallon wasan ƙarshe da Nijeriya za ta buga

AFCON 2023: Tinubu zai halarci kallon wasan ƙarshe da Nijeriya za ta buga

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai halarci kallon wasan ƙarshe da Nijeriya za ta buga a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) 2023 da ke gudana a Côte d’Ivoire. Ya zuwa ranar Lahadi ake sa ran Nijeriya da Côte d’Ivoire za su fafata a wasan ƙarshe na gasar wanda za a buga a Abidjan. Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta CAF, Patrice Motsepe, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da ya shirya ranar Juma'a a Abidjan. Za a buga wasan ƙarshen ne a filin wasannin motsa jiki na Alassanne Ouattara, Ebimpe, Abidjan. Tuni dai 'yan…
Read More