10
Feb
Daga BASHIR ISAH Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta ce tana neman matar tsohon Gwamnan CBN, Margaret Emefiele da wasu mutum uku ruwa a jallo a kan batun da ya shafi almundahana. Majiyarmu ta bayyana cewa a daren Juma'ar da ta gabata EFCC ta sanar da neman da take yi wa Mrs Emefiele da Mr Eric Odoh da Anita Omoile tare da mijinta Jonathan Omoile. Hukumar na neman waɗanda lamarin ya shafa ne bisa zargin haɗin baki da tsohon Gwamnan na CBN "wajen karkatar da maƙudan kuɗi mallakar Gwamnatin Tarayya wanda hakan ya sa suka mallaki kuɗi ta hanyar…
