Editor

9513 Posts
Sarkin Zazzau ya jagoranci buɗe masallacin Juma’a a Fammadina Zariya 

Sarkin Zazzau ya jagoranci buɗe masallacin Juma’a a Fammadina Zariya 

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya A ranar Juma'ar da ta gabata Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya jagoranci buɗe masallacin juma'a a garin Fammadina a gundumar Dutsen Abba da ke Zariya. Taron buɗe masallacin ya samu halartar wanda ya gina masallaci wato Alhaji Umar Faruq Suleiman da masana ilimin addinin Musulunci da kuma fitattun 'yan siyasa da suke ciki da wajen jihar Kaduna. Mai martaba Sarkin Zazzau a jawabinsa ya fara da addu'a ta musamman ga wanda ya gina masallacin a cikin lokaci ba mai tsawo ba. Malam Ahmed Bamalli ya kuna matuƙar jin daɗinsa na…
Read More
Nijeriya ce ƙasa mafi sauƙin rayuwa a Afirka – Fadar Shugaban Nijeriya

Nijeriya ce ƙasa mafi sauƙin rayuwa a Afirka – Fadar Shugaban Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin Shugaban Nijeriya ya tayar da ƙura da iƙirarin da ya yi na cewa ƙasar ta fi ƙarancin tsadar rayuwa a nahiyar Afirka. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne ya faɗi hakan a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake yin watsi da sukar da Atiku Abubakar ya yi cewa manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu na ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala. Mista Onanuga ya bayyana wani nazari da wani kamfani intanet Numbeo ya yi kan matsayin Nijeriya a tsarin tsadar rayuwa. Ya…
Read More
Tinubu ya bada umarnin gaggawa kan raba ton 100,000 na abinci ga ‘yan ƙasa

Tinubu ya bada umarnin gaggawa kan raba ton 100,000 na abinci ga ‘yan ƙasa

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na neman daƙile tsadar rayuwa da ƙarancin abincin da 'yan ƙasa ke fuskanta, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa kan a saki kayan abinci har ton 100,000 don amfanin 'yan ƙasa. Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Bada Tallafin Abinci a ranar Alhamis. Idris ya ce, gwamnati ta shirya shigo da abinci daga ƙetare domin cike giɓin da ka iya aukuwa bayan kammala raba kayan abincin.…
Read More
Bai wa al’ummarmu tsaro ne babbar manufarmu – Gwamna Lawal

Bai wa al’ummarmu tsaro ne babbar manufarmu – Gwamna Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jadda cewa, bai wa al’ummar jihar cikakken tsaro shi ne babbar manufar da gwamnatinsa ta sa gaba. Lawal ya bayyana haka ne a wajen tsaron majalisar tsaron jihar da ya gudana a karkashin jagorancinsa  ranar Laraba a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar. Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya ce samar da Dakarun Tsaron Al’umma na Jihar Zamfara da kaddamar da kwamitin kula da Asusun Tallafa wa Sha’anin Tsaro na daga cikin manyan batutuwan da taron ya tattauna. Idris…
Read More
Mutane na girmama ni saboda lashe gasar Hikayata – Aisha Fulani

Mutane na girmama ni saboda lashe gasar Hikayata – Aisha Fulani

"Zumuncin marubuta abin a yaba ne sosai" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Aisha Abdullahi Yabo ba bakuwa ba ce a cikin marubuta, musamman marubutan onlayin, inda take daya daga cikin masu ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban adabin Hausa. Ita ce ta zo gwarzuwa ta biyu a Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023. 'Ya ce ga fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Zamfara, Sheikh Abdullahi Abubakar Yabo. Don haka babu mamaki jin cewa, Aisha da aka fi sani da Fulani, hafizar Alkur'ani Mai Girma ce, kuma masaniya a sauran fannonin ilimin addini, kuma har yanzu tana cigaba da neman…
Read More
Shettima ya taya Super Eagles murnar shiga zagayen karshe a garsa AFCON 2023

Shettima ya taya Super Eagles murnar shiga zagayen karshe a garsa AFCON 2023

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya taya ’yan wasan Super Eagles murnar samun nasarar kaiwa zagayen karsahe a gasar AFCON 2023 da ke gudana a Ivory Coast. ‘Yan wasan Super Eagles na Nijeriya sun taki wannan nasarar ce bayan da suka yi galaba a kan ‘yan wasan Bafana Bafana na Afirka ta Kudu a wasan da suka buga ranar Laraba a filin Stade de la Paix da ke Bouake. An kare wasan ne da 1-1 bayan shafe mintoci sama da 100, wanda a karshe wasan ya kammala da bugun fenariti. Yanzu dai tun da ta samu tsallake…
Read More
AFCON 2023: Tsohon ɗan majalisar Nijeriya ya mutu a wajen kallon wasan Super Eagles da Afirka ta Kudu

AFCON 2023: Tsohon ɗan majalisar Nijeriya ya mutu a wajen kallon wasan Super Eagles da Afirka ta Kudu

Daga BASHIR ISAH Bayanai da MANHAJA ta samu na nuni da cewa wani tsohon dan majalisar wakilai daga Jihar Delta ya mutu a wajen kallon wasan kwallon da aka buga tsakanin Super Eagles da Afrika ta Kudu na gasar AFCON 2023 a ranar Laraba. Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin ta ce, Ojuogboh ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da aka bai wa Afirka ta Kudu damar buga fenariti a kurarren lokaci a yayin wasan da aka buga a filin Stade de la Paix da ke Bouake. A halin rayuwarwa, marigayi Cairo Ojuogboh tsohon dan Majalisar Wakilai…
Read More
Mace ’yar jarida ta fi namiji samar da gamsasshen rahoto kan cin zarafi – Salamatu Abdullahi

Mace ’yar jarida ta fi namiji samar da gamsasshen rahoto kan cin zarafi – Salamatu Abdullahi

"Mata ne suka fi dacewa da aikin jarida" Daga AISHA ASAS Bakuwar tamu ta wannan makon dai bata buqatar doguwar gabatarwa, saboda kasancewarta ‘yar gida ga kaso mafi yawa daga cikin masu karatunmu, musamman ma mazauna Jihar Kaduna. Duk da cewa, fuskarta da gangarar jikinta bata kewaye Arewacin Nijeriya ba, sai dai tuni amon sautin muryarta ya karade mutanen Arewa, musamman ma ma’abota sauraron littafan Hausa. Kwararriya ce da ta qware wurin iya sarrafa murya yayin karanta littafan Hausa, kuma tana gabatar da shiri na musamman domin kawo gyara ga zamantakewar aure. ’Yar jarida ce da ta yi aiki a…
Read More
Kotu ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta daidaita farashin fetur, madara, sukari keke da sauransu

Kotu ta umarci Gwamnatin Nijeriya ta daidaita farashin fetur, madara, sukari keke da sauransu

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Legas ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin mako daya a kan ta daidaita kayayyakin masuru a fadin kasa don amfanin ‘yan kasa. Kayayyakin da lamarin ya shafa sun hada da madara, sikari, gishiri, keken hauwa, babur, fetur, gas, kananzir da sauransu. Kotun ta ba da wannan umarni a zaman da ta yi a ranar Laraba karkashin jagorancin Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa. Alkalin ya bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta daidaita farashin kayayyakin ne biyo bayan karar da Babban Lauyan Nijeriya kuam mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana SAN ya shigar Kotun.…
Read More