07
Feb
Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Ikoyi, Jihar Legas ce ta ba da wannan umarni a ranar Laraba, 7 ga Fabrairu. Umarnin Kotun ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta daidaita farashin fetur da na saura kayayyaki a cikin mako daya. Mai Shari’a Ambose Lewis-Allagoa ne ya ba da wannan umarni biyo bayan karar da Babban Lauyan Nijeriya kuam mai rajin kare hakkin dan’adam, Femi Falana SAN ya shigar Kotun. A cewar Alkalin, “Na ji mai karar Femi Falana a cikin kararsa mai lamba FHC/L/CS/869/2023 kuma na gano duk da karar da aka shigar kan masu kare kansu,…
