Editor

9513 Posts
Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Tsaftace zuciya a game da batun kishi (1)

Tare da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Masu karatu sannunku da jimirin karanta wannan fili namu na Zamantakewa wanda yake zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan makon za mu tattauna a kan zafin kishin mata da ya addabi al'umma da abin da yake kawo shi, da kuma yadda za a magance shi. A sha karatu lafiya.Kafin na shiga rubutun gadan-gadan. Ya kamata na tuna wa 'yanuwana mata cewa: mu ne jinsin da muka fi nuna muna da hadin kai yayin da wata 'yaruwarmu ta shiga wani hali fiye da maza. Kuma mu…
Read More
EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn

EFCC ta tsare ƙanin Hadi Sirika kan binciken badaƙalar N8bn

Daga BASHIR ISAH Jami’an Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta tsare Abubakar Ahmad Sirika, kani ga tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Abubakar Sirika. News Point Nigeria ta rawaito cewar, jami’an sun cika hannu da dan’uwan tsohon ministan ne a ranar Lahadi bayan da binciken da EFCC ke gudanarwa a Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ya biyo ta kansa. Ana zargin Sirika da tafka almundahanar da ta kai N8,069,176,864 a lokacin da yake rike da mukamin Minista. Hukumar ta ce kudaden na wasu kwangila ne guda hudu wanda Sirika ya bai wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakar kanin…
Read More
An cafke matar da ta sayar da yara sama da 42

An cafke matar da ta sayar da yara sama da 42

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ’yar shekara 45 mai suna Alimot Haruna mai fataucin kananan yara, ta bayyana cewa ta sayar da yara sama da 42 a cikin shekaru biyar da suka gabata. A ranar Laraba ne wata tawagar ’yan sanda daga ofishin ’yan sanda na Ijora Badia na rundunar ’yan sandan Legas ta cafke wadda ake zargin. An tattaro cewa wadda ake zargin wanda cibiyarta ke a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta kasance cikin jerin sunayen ’yan sandan da ake nema ruwa a jallo kan irin wannan laifin. Wadda ake zargin a cikin sanarwar da ta yi na…
Read More
Mai gadin makaranta ya kashe kansa saboda tsohuwar matarsa ta auri wani

Mai gadin makaranta ya kashe kansa saboda tsohuwar matarsa ta auri wani

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani mai gadi a kwalejin Prestige International College, Nurudeen Shehu, mai shekaru 37, ya kashe kansa sakamakon labarin kara auren tsohuwar matarsa a Kano. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usaini Gumel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a cikin daya daga cikin azuzuwan kwalejin a ranar Lahadi. Gumel ya ce, “A ranar 28 ga watan Janairu da misalin karfe 10:30 na safe, Abdullahi Abdulsalam na Rijiyar Zaki ya ruwaito cewa an samu Shehu a rataye ba motsi a cikin aji. “’Yan sanda daga sashin Gwale, karkashin jagorancin DPO,…
Read More
Alhassan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta yamma a shekarar 1950

Alhassan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta yamma a shekarar 1950

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhassan Dantata, fitaccen attajiri a fadin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga sayar da Goro da Gyada. Haihuwa da nasaba; Alhassan Dantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani qaramin qauye da ake kira Danshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar aqalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan daya ne daga cikin ’ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa. Shi Abdullahi da ne ga wani mutum…
Read More
Matsalar da fyaɗe ke haifarwa ga ‘ya mace

Matsalar da fyaɗe ke haifarwa ga ‘ya mace

Daga AISHA ASAS Kafin komai zan so mu fara da bayyana ma'anar kalmar fyade kafin mu kai ga tattauna matsalolin da ake fuskata bayan fyaden. Fyade wani nau'in cin zarafi ne ta bangaren jima'i, amfani da karfi yayin kusantar mace ko namiji, ma'ana yi ba da amincewar abokin tarayya ba. Idan aka ce fyade, hankalin mutane ya fi tafiya ne ga mata, a ganin su mata ne kawai ake yi wa cin zarafi ta ɓangaren fyade. Ko kaɗan wannan zance ba haka yake ba, domin an tabbatar kaso 29 bisa dari na mazan duniya sun fuskanci cin zarafi ta ɓangaren…
Read More
Abin da ya faru a Minna aikin ɓata-gari ne ba zanga-zangar tsadar rayuwa ba – Gwamna Bago

Abin da ya faru a Minna aikin ɓata-gari ne ba zanga-zangar tsadar rayuwa ba – Gwamna Bago

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya ce dandazon jama'a da aka gani a kan hanya a wasu titunan garin Minna a ranar Litinin, ba zanga-zangar tsafar rayuwa ba ne face ayyukan wasu ɓata-gari ne masu neman daburta zaman lumanar al'umma. Ya ce wasu bata-gari ne suka shirya dandanzon don samun danar wawure kayan abincin da wata mota ke da su wadda ke kan hanyar shigowa gari daga hanyar Bida. Gwamnan ya kara da cewa, "Yanzun haka mun kama wasu daga cikin bata-garin kuma za mu ci gaba da daukar matakin ganin ba mu bari an kawo…
Read More
‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan rakiyar A’amarya 35 a Katsina

‘Yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan rakiyar A’amarya 35 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata dabar 'yan bindiga ta sace mata 35 a lokacin da suke dawowa daga rakiyar amarya a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da misalin karfe 8: 30 na daren ranar Alhamis. Amma sai a wannan Litinin labarin ya yadu bayan da hukumomi suka ziyarci kauyen. 'Yan bindigar sun yi wa motar 'yan kai amaryar dirar mikiya inda suka harbi direman motar wanda yanzu haka yana kwance yana karbar magani. Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewar wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun…
Read More
Ƙananan asibitoci masu zaman kansu na buƙatar tallafi – Gabare Clinic

Ƙananan asibitoci masu zaman kansu na buƙatar tallafi – Gabare Clinic

Daga ABDULLAHI Sani Doguwa a Kano An buƙaci masu hali da ke cikin alumar musulmi a ko'ina da su rinka tallafa wa kananan asibitoci masu zaman kansu da gudunmawar da ta dace, musamman asibitochin da ke duba larurar iyaye mata masu dauke da juna biyu, ko dai sauran alumma da suke da larurori daban-daban, duba da halin da alumma ke ciki na matsin tsadar rayu. Mukaddashin babban daraktan lura da masu dauke da lafiyar iyali na asibitin Gabare Clinic & Maternity dake Sumaila, da ya bukaci a sakaye sunansa, shi ne ya yi wannan kira yayin ganawarsa da manema labarai.…
Read More
Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Neja

Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Neja

Daga BASHIR ISAH Al'ummar garin Minna, babban birnin Jihar Neja, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu dangane da tsadar rayuwar da ake ci gaba da fuskanta a Nijeriya. An ga masu zanga-zangar a ranar Litinin sun mamaye wasu manyan hanyoyin garin wanda hakan ya haifar da tsaikon zirga-zirgar abubuwan hawa. MANHAJA ta kalato cewar, mazauna yinkin Kpakungu da ke Minna sun yi cincirindo a kan hanya daidai randabawul da ke yankin inda suka hana masu abubuwa hawa shiga da fita. Bayanai sun ce jama'ar sun bukaci 'yan sandan da suka bayyana a wurin don kula da…
Read More