Editor

9513 Posts
Aure mai nagarta maganin nadama

Aure mai nagarta maganin nadama

Aure abu ne wanda ya wuce a yi wasa da shi, don haka ni ke son amfani da wannan dama in kawo ‘yar shawara ga ‘yan uwa na talakawa. Duk auren da aka gina bisa cencenta ya kuvuta daga tozarta don haka sai mun yi karatu a natse mu gano bakin zaren. Kana talaka tikif amma a kullum gurin ka wanda zai zo neman auren ‘yarka daga mawadaci sai mai wata daukaka, ka manta cewa tun a zamanin baya ma su wadata kadan ne ke zuwa su auri ‘yar talakawa ina ga yanzu da zamani ya zamo na idan ba…
Read More
NYSC ta daina tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa jihohi masu fama da matsalar tsaro – Gwamnati

NYSC ta daina tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa jihohi masu fama da matsalar tsaro – Gwamnati

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta daina tura masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa jihohin da ke fama da matsalar tsaro a fadin kasa. Rahotanni sun ce masu yi wa kasa hidima da dama ne aka yi garkuwa da su yayin da aka tura su sassan kasa domin hidimta wa kasa na shekara guda bayan kammala karatu. An jiwo Ministar Harkokin Matasa, Jamila Ibrahim na cewa, gwamnati ta dauki sahihan matakai domin bai wa masu yi wa kasar hidima kariya ciki har da daina tura su zuwa yankunan da ke fama da matsalar tsaro. A cewarta,…
Read More
Zuwa ga al’ummar Arewa

Zuwa ga al’ummar Arewa

Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri gare ku duka, ina kuma mai jajanta muka akan halin da muka tsincin kanmu a yau. Ina fatan wannan wasikar tawa ta same ku lafiya, cikin koshin lafiya da walwala. Na rubutu muku wannan wasikar ne domin na isar muku da sakona tare da fatana gare ku. Ina mai shaida muku cewa, kaunarku ce ta sa na rubutu wannan wasikar, domin masu iya magana kan ce 'Idan kunne ya ji…' Wannan wasiqar ita ce babbar gudunmawar da zan iya bayarwa a halin yanzu, bayan koyar da yara da nake…
Read More
Tsohon Gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya kwanta dama

Tsohon Gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya rasu a daidai lokacin da yake jinya a wani asibitin Kasar Saudiyya. Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da rasuwar marigayin cikin sanarwar da ya fitar ta bakin Darakta Janar na Yada Labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed. Sanarwar ta ce a ranar Lahadi marigayin ya cika, kuma a Saudiyya za a binne shi. Ana sa ran Gwamna Mai Mala Buni ya yi zaman karbar ta'aziyyar rasuwar a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Damaturu. Abba Ibrahim ya bar duniya yana da shekara 75, kuma shi ne miji…
Read More
Shugaban Ƙasar Namibiya ya rasu yana da shekara 82 a duniya

Shugaban Ƙasar Namibiya ya rasu yana da shekara 82 a duniya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasar Namibiya, Hage Geingob, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, kamar yadda ofishinsa ya bayyana. Marigayin ya rasu ne sakamakon fama da cutar daji. Geingob ya mutu ne a ranar Lahadi a asibitin Lady Pohamba da ke Windhoek, babban birnin kasar, inda da matarsa ​​da 'ya'yansa suka kasance a gefensa, in ji Mukaddashin Shugaban Kasar, Nangolo Mbumba, a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na Geingob. Mbumba ya ce "Al'ummar Namibiya ta yi rashin wani fitaccen hadimin jama'a, mai fafutukar kwato 'yanci, babban mai tsara tsarin mulkinmu da kuma ginshikin Namibia," in…
Read More
EFCC ta fara bincike kan badaƙalar jirgin ‘Nigeria Air’ daga Sirika – Keyamo

EFCC ta fara bincike kan badaƙalar jirgin ‘Nigeria Air’ daga Sirika – Keyamo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta fara gudanar da bincike a kan wata badakalar cinikin jirgin 'Nigeria Air' da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya kulla. "Hukumar EFCC na binciken wannan yarjejeniya," Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana a cikin shirin Siyasa A Yau na Channels Television a ranar Laraba wanda Blueprint Manhaja ke sa ido. Ya ce “akwai binciken manyan laifuka. Na kira ga rahoton”. Keyamo ya kuma ce babu wani kamfanin jirgin sama na cikin gida da za a…
Read More
AFCON 2023: Osimhen na fuskantar matsin lamba wajen zura ƙwallaye – Udeze

AFCON 2023: Osimhen na fuskantar matsin lamba wajen zura ƙwallaye – Udeze

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon dan wasan Nijeriya Ifeanyi Udeze ya ce dan wasan Super Eagles Victor Osimhen yana fuskantar matsin lamba wajen zira kwallaye a gasar AFCON 2023. An yi hasashen Osimhen ya shiga gasar ta bana a matsayin daya daga cikin ’yan wasan da za su fafata domin samun kyautar dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye. Sai dai Osimhen ya samu nasarar zura awallo daya ne kawai kuma ya rasa damar cin kwallo da dama. Da yake waiwayar rawar da Osimhen ya taka bayan wasanni uku na rukuni, Udeze ya yi imanin cewa rashin samun karin…
Read More
Batun matsalar damfara a yanar gizo

Batun matsalar damfara a yanar gizo

Babu makawa ga duk mai mu'amala da yanar gizo (Internet) ko wayar salula ya san matakan kariya game yadda wadansu vata gari ke baza tarko ta ko wacce irin dama su ka samu don su damfari jama'a. Idan muka ce yanar gizo to anan mu na nufin Ko wanne fanni na yanar gizo. Shin kai ma'abocin burauzin ne don karanta labarai, ko mai binciken ilmi, ko ma'abocin kafofin sada zumunci da dai sauran su. Yau za mu kawo hanyoyin da su ka fi shahara wajen yin damfara a yanar gizo, kuma sanin su zai taimaka ma wajen tsallake tarkon su,…
Read More
’Yan bindiga sun sace darakta kusa da sansanin sojoji a Abuja

’Yan bindiga sun sace darakta kusa da sansanin sojoji a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A yayin da ake cigaba da fama da matsalar rashin tsaro a Abuja, a baya-bayan nan dai wannan harin da aka kai wani gida mai tazarar mita 200 kusa da sansanin sojoji da ke Pambara, a karamar hukumar Bwari a Babban Birnin Tarayya Abuja, ya fi daure kai. A yayin harin, an yi garkuwa da wani mai suna Aondo Ver, wanda aka ce darakta ne a Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya. ’Yan bindigan sun kai farmaki gidan ne da misalin karfe 12:30 na tsakar darebn wayewar garin jiya Alhamis. Rahotanni sun nuna cewa, masu garkuwa…
Read More
Shugabancin MOPPAN: Yadda Barde ya zama magajin Sarari a Kannywood

Shugabancin MOPPAN: Yadda Barde ya zama magajin Sarari a Kannywood

Daga AISHA ASAS  A ranar Laraba da ta gabata, 31 ga Janairu, 2024, Kwamitin Amintattu na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Kasa, wato MOPPAN, ya nada Mallam Habibu Muhammd Barde, Mataimakin Shugaba na Shiyar Arewa ta Tsakiya na kungiyar, a matsayin shugaban riko na kasa. Sanarwar nadin na kunshe ne a cikin sanarwar manema labarai da Kwamitin Amintattu na kungiyar ya fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Makama Sani Mu’azu, wanda ya biyo bayan ajiye mukamin da Dakta Ahmad Sarari ya yi a matsayin Shugaban Kungiyar, duka dai a ranar ta Larabar. Sarari ya bayyana cewa, ya ajiye…
Read More