04
Feb
*Shugaban yana aiki dare da rana don gyara Nijeriya, inji ministan labarai Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya roki ‘yan Nijeriya da su kara hakuri da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa, ya yi wuri a yanke kauna ko a dawo daga raikiyar gwamnatin daga lokacin da ya dare gadon mulki zuwa yanzu. Tun da ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, Shugaba Tinubu ya bullo da wasu tsauraran sauye-sauye a fannin tattalin arziki, irin su shakewar Naira da kuma cire tallafin man fetur…
