Editor

9513 Posts
Ana zargin matashi da sace mazakutar samari a Jigawa

Ana zargin matashi da sace mazakutar samari a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Tsaro ta Sibil Difens, ta cafke wani matashi mai shekaru 24 da a ke zargi da sace mazakutan wasu samari biyar a Karamar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa. Kakakin hukumar, ASC Badrudeen Tijjani Mahmud ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis. A cewarsa, matashin da ake zargi ya fito ne daga kauyen ’Yan Ciyawa na Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe. Ya ce a ranar Litinin 29 ga watan Janairu ne suka kama matashin kan zargin sace mazakutan wasu samari biyar a unguwar Gida Dubu da ke…
Read More
’Yan sanda sun ƙi karɓar cin hancin Miliyan N8 daga ’yan bindiga a Taraba

’Yan sanda sun ƙi karɓar cin hancin Miliyan N8 daga ’yan bindiga a Taraba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta kama wasu mutane 13 da ake zargin ’yan fashi ne da masu garkuwa da mutane da suka addabi mazauna qananan hukumomin Jalingo, Yorro, Lau, da Zing na jihar. Kwamishinan ’yan sandan jihar Joseph Eribo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin tare da baje kolin su a hedikwatar ’yan sanda da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Laraba. Kamen dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama'a suka yi kan munanan ayyukan 'yan ta'addar wanda a cewar 'yan sandan ya ɗauki wani salo mai…
Read More
Ɗan jari-bola ya tsunto bom da ya tashi da almajirai a Borno

Ɗan jari-bola ya tsunto bom da ya tashi da almajirai a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani abun fashewa ya kashe wasu almajiran wata makaranta hudu tare da wasu mutum biyu da ba a gano su wane ne ba a Karamar Hukumar Gubio da ke Jihar Borno. An ruwaito cewa, shugaban aaramar hukumar Alhaji Mali Gubio ne ya tabbatar mata da faruwar wannan lamari, ya ce abin ya fashe a wani kango da misali qarfe 11 na safiyar Asabar. “Duka mutanen da abin ya rutsa da su sun mutu, don haka ba za mu iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma wani abun fashewa ne ya tashi a inda ake…
Read More
Filato: An fara raba kayan aikin zaɓe babu tambarin PDP

Filato: An fara raba kayan aikin zaɓe babu tambarin PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara rabon muhimman kayan zabe a kananan hukumomi shida na jihar Filato gabanin zaben da za a sake gudanarwa ranar Asabar. An yi rabon kayayyakin zaben ne a harabar Babban Bankin Nijeriya da ke Jos, babban birnin jihar. An gudanar da rabon kayayyakin ne a gaban wakilan jam’iyyun siyasa, masu sa ido, ‘yan jarida da jami’an tsaro. Sai dai da aka fara rabon kayayyakin, an gano cewa babu tambarin Jam’iyyar PDP a takardar jefa kuri'a yayin da wasu da suka hada da APC, PRP, da…
Read More
Bayan gasar AFCON Peseiro zai san makomarsa – Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya

Bayan gasar AFCON Peseiro zai san makomarsa – Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kwallon Kafar Nijeriya, ta bayyana cewa babu wata yarjejeniya da ke tsakaninta da kocin tawagar Nijeriya a gasar kofin Afirka ta AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast, Peseiro Wary bayan kammala gasar. Shugaban hukumar Ibrahim Musa Gusau ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa. Ya kara da cewa, "abin farin ciki yanzu shi ne duk wasu basuka da yake bi, mun samu daga Gwamnatin Tarayya za a biya shi." Sai dai ya ce, za su iya daukar koci daga kowace irin kasa ta duniya ba lallai sai dan Nijeriya ba. "Abin da…
Read More
Tsaro: Tsarin da ake bi ba shi da tasiri – Kakakin Majalisar Wakilai

Tsaro: Tsarin da ake bi ba shi da tasiri – Kakakin Majalisar Wakilai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajuddeen ya bayyana a ranar Talata cewa Majalisar Tarayya za ta yi taro na musamman dangane da gagarimar matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya baki daya. Ya bayyana haka yayin da aka koma zaman majalisa, inda ya ke cewa matsalar tsaro a kasar nan ta yi muni kuma ta kazanta matukar gaske. “Ina bada shawarar gudanar da Taron Majalisar Tarayya kan Matsalar Tsaro. Taron zai kasance ya zama wurin da za a bijiro da shawarwari daga bakin masu ruwa da tsaki a bangarori da dama, kamar jami’an tsaro, sarakunan gargajiya,…
Read More
Matsin Rayuwa: Ku ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, sauƙi na tafe – kiran Idris ga ‘yan Nijeriya

Matsin Rayuwa: Ku ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu, sauƙi na tafe – kiran Idris ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga 'yan Nijeriya da su kara hakuri da gwamnatin Shugaba Tinubu bisa sauye-sauyen da take yi don cigaban kasa. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya yi wannan kira, inda ya ce watannin da Tinubu ya yi a ofis ba su taka kara sun karya ba balle a rika kukan rashin gani a kasa. Tun bayan da ya kama mulkin kasa a watan Mayun da ya gabata, Tinubu ya dauki wasu matakai ciki har da cire tallafin mai lamarin da ya jefa kasa cikin halin tsadar rayuwa. Sai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren ƙarar da aka shigar kan mawaƙi Rarara bisa zargin sukar Buhari

Da Ɗumi-ɗumi: Babbar Kotu ta hana ci gaba da sauraren ƙarar da aka shigar kan mawaƙi Rarara bisa zargin sukar Buhari

Daga BASHIR ISAH Wata Babbar Kotun Jihar Nasarawa da ke zamanta a yankin Doma ta dakatar da Kotun Majastare ta 1 da ke Lafia daga ci gaba da sauraren ƙarar da wani matashi mai suna Sani Ahmad Zangina ya shigar kan fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, bisa zarginsa da sukar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari. Lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin Rarara, Barrister A. I Ma'aji, ya bayyana wa manema labarai cewar sun ɗaukaka ƙara a gaban Mai Shari'a Abdullahi H. Shamsu Shama na Babbar Kotu da ke Doma tun ranar Litinin ta ƙarshen watan jiya, bisa rashin…
Read More
Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin 2024

Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin 2024

Daga BASHIR ISAH Hukumar Alhazan ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa Saudiyya ta yi wa Nijeriya ragin kudin aikin Hajjin bana don samun saukin wadanda za su tafi aikin Hajjin bana daga kasar. NAHCON ta ce shugabanta, Jalal Ahmad Arabi ne ya mika bukatar neman ragin domin walwalar mahajjatan Nijeriya. Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun NACHON, Fatima Sanda Usara, ta fita a ranar Laraba, inda ta ce ragin ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai yayin aikin Hajji a Saudiyya. Sanarwar ta ce biyo…
Read More
Rura wutar rikici a Filato ba alheri ba ne

Rura wutar rikici a Filato ba alheri ba ne

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A daidai lokacin da nake wannan rubutu mazauna Karamar Hukumar Mangu a Jihar Filato na zaune a gidajensu cikin cikin fargaba da takura, sakamakon dokar ta baci na tsawon awa 24 da gwamnatin jihar ta kafa, domin hana bazuwar rikicin da ya varke tsakanin matasan kabilar Mwaghavul da Hausawa da Fulani. Kodayake har kawo yanzu ba a gama kididdige yawan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi ba, amma daga bayanan da ke fitowa daga wasu mazauna yankin an salwantar da rayuka da dukiyoyi masu yawa, musamman a rana ta biyu da rikicin ya cigaba…
Read More