01
Feb
"Taɓarɓarewar tarbiyya daga gida ke samo asali" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gimbiyarmu ta wannan mako ba kowa ba ce illa Hajiya Jamila Tijjani Abdullahi, tsohuwar lauya, tsohuwar ma'aikaciyar banki, tsohuwar jami'ar gwamnati, malamar makaranta, ƴar kasuwa, kuma mai kishin cigaban rayuwar mata da matasa, kuma shugabar kungiyar Jam'iyyar Matan Arewa a Jihar Filato. 'Ya ce a wajen fitaccen dan siyasar nan na Arewa kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Ambasada Yahaya Kwande. Har-wa-yau, mijinta Alhaji Tijjani Abdullahi, mai lakabi da George Best, tsohon dan siyasa ne kuma babban dan kasuwa a cikin garin Jos. A zantawarta da wakilin Blueprint…
