Editor

9513 Posts
Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta yi sabon shugaba

Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta yi sabon shugaba

Daga BASHIR ISAH A ranar Talata aka rantsar da Hon. Oludaisi Elemide a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun inda ya maye gurbin Olakunle Oluomo wanda ska tsige shi a matsayin kakin majalisar makon jiya. Yayin zaman majalisar karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar, Bolanle Ajayi wanda ya samu halarcin mambobi 22, Hon. Musefiu Lamidi ya karanto rahoton kwamitin da majalisar ta kafa don binke kan zarge-zargen da ake yi wa Oluomo. Rahoton Kwamitin ya ce rashin da'ar da tsohon Kakakin ya nuna wa Kwamitin a lokacin gudanar da bincikensa rashin martabaws ne ga Kwamitin da ma Majalisar baki daya.…
Read More
Ukraine na zargin wasu jami’anta da wawushe mata kuɗin makamai

Ukraine na zargin wasu jami’anta da wawushe mata kuɗin makamai

Daga BASHIR ISAH Binciken gwamnatin Ukraine ya bankado cewar wasu jami’an hukumar kula da makaman kasar sun hada baki da takwarorinsu na ma’aikatar tsaro, wajen karkatar da kusan Dala miliyan 40, da aka ware domin sayen makamai. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke tsaka da fafata yaki tsakaninta da Rasha. Ya zuwa yanzu an gurfanar da mutum biyar a kotu kan zargin yin rub-da-ciki a kan kudin maka kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana. Kazalika, bayanan gwamnatin Ukraine sun ce ana tsare da wani guda da aka cafke shi a lokacin da yake kokarin…
Read More
Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa

Majalisar Dattawa ta buƙaci zama da shugabannin tsaro kan tabarɓarewar tsaron ƙasa

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta gayyaci shugabannin tsaro domin su zo a zauna don tattauna matsalar tsaron da ke kara kamari a kasa. Sai dai, Majlisar ba ta ayyana takamammiyar ranar da jami'an za su bayyana a gabanta ba. Majalisar ta gayyaci shugabannin tsaron ne bayan tattaunawar sirrin da mambobinta suka yi na sama da sa'o'i uku a ranar Talata, inda suka nuna damuwarsu kan yadda ake samun karuwar sace-sacen mutane da kisa da sauran manyan laifuka. Jagogaran Majlisar, Michael Bamidele Opeyemi, ya bayyana cewa baki daya sanatocin su 109 kowannensu ya gabatar da kudurin doka kan matsalar tsaro…
Read More
Nijeriya ta nuna rashin jin daɗinta kan ficewar wasu takwarorinta daga ECOWAS

Nijeriya ta nuna rashin jin daɗinta kan ficewar wasu takwarorinta daga ECOWAS

Daga BASHIR ISAH Nijeriya ta ce ko kadan ba ta ji dadin ficewar da wasu takwarorinta suka ce sun yi ba daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS. Nijeriya ta bayyana rashin jin dadin nata ne a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta hannun Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar wanda aka wallafa a shafin X na ma'aikatar. Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ma’aikatar, Ambasada Francisca Omayuli ta ce: “Kusan shekara 50 ke nan ECOWAS take aiki don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da dimokuradiyya a yankin. “Nijeriya tana tare…
Read More
AFCON 2023: CAF za ta yi wa Osimhen gwajin ƙwayar ƙara kuzari

AFCON 2023: CAF za ta yi wa Osimhen gwajin ƙwayar ƙara kuzari

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika (CAF) ta zabi dan Nijeriya Victor Osimhen domin yin gwajin kwaya. Victor Osimhen ya taka rawar gani wa Super Eagles ta Nijeriya a Gasar Cin Kofin Afirka  da ke gudana wanda ya kai Nijeriya ga saun nasarar yin waje da kasar Kamaru. MANHAJA ta kalato cewa, CAF ta sanya wa dan wasan ido ne tun baya wasan da suka buga da Guinea-Bissau. Kazalika, dan wasan FC Nantes, Simon Moses da William Troost-Ekong na daga jerin ‘yan wasan da za su fuskanci gwajin kwayoyin kara kuzari. Ana gudanar da irin wannan gwajin ne…
Read More
Basaja a zaman aure (2)

Basaja a zaman aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Sannunku da jimirin karatun shafin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja! A wannan mako mun kawo muku yadda wasu ma'aurata suke yin basaja a zaman aure. Wanda abu ne da yake taka muhimmiyar rawa wajen kawo rikici a gidajen aure har ma idan abu ya yi qamari ya kai ga rusa auren gabadaya. A makon da ya gabata mun fara kwararo muku bayani ya zu kuma za mu dora a kashi na biyu na wannan maudu'in. A sha karatu lafiya. Haka su ma mata akwai kawaye da za su dinga cika muku baki…
Read More
An cafke uwa kan jefar da jaririyarta cikin rafi

An cafke uwa kan jefar da jaririyarta cikin rafi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar 'Yan Sanda ta damke wata mata da ta jefa jaririyarta mai watanni biyar a duniya a cikin kogi da nufin kashe ta. Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta cafke matar mai shekaru 30 a duniya ne kan zargin yunkurin halaka jaririyar a kogin RSS da ke Sagamu. A yammacin ranar Litinin ne ta jefar da jaririyar a ruwa domin ta nutse, amma wani wanda da ya ga abin da ta yi da ke kusa da wurin ya taimaka wajen ceto ta. Sanarwa da kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ya aikewa manema labarai a ranar Litinin…
Read More
Tarihin rikicin Maitatsine

Tarihin rikicin Maitatsine

Tare da MAHDI M. MUHAMMAD Blueprint Manhaja ta yi nazari tare da tattaro bayanai dangane da labarin rikicin Maitatsine. Makasudin rikicin Maitatsine ya faru ne a ranar 11/12/1980, wato kusan a ce ya faru ne a unguwar Malafa. Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a bangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza. A bangaren malamai kuma, akwai irinsu Malam Umar Sani Fagge, da Malam Haido da su Malam Muktar Atamma, wanda duk a yankin…
Read More
Gwamnati ta yunƙura don kwantar wa ‘yan ƙasa da hankali kan ɗauke FAAN, CBN zuwa Legas

Gwamnati ta yunƙura don kwantar wa ‘yan ƙasa da hankali kan ɗauke FAAN, CBN zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta yunkura domin kwantar da hankalun 'yan kasa kan batun wasu bangarorin CBN da babban ofishin FAAN zuwa Legas. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi. Idris ya bayyana cewa batun dauke wasu hukumomi daga Abuja zuwa Legas ba shi da wata alaka da siyasa. Idris ya ce, “Duk da cewa muna tunkarar kalubalenmu cikin gaggawa da sadaukarwa, ya zama dole mu tunatar da daukacin ‘yan Nijeriya bukatar tinkarar labaran da ake yadawa ba daidai ba da rarraba kan…
Read More
Ashe ɓarayin mutane sun shigo Abuja?

Ashe ɓarayin mutane sun shigo Abuja?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Da shigowa Abuja dan Nijeriya zai san ya shigo birnin da shugaban kasa ya ke da zama don ganin manyan ofisoshin jami'an tsaro kama daga na soja, 'yan sanda, jami'an tsaron farar hula da sauarn su. Ga mutane masu wutar jiniya na zirga-zirga. Barikoki kadai a bayan fadar shugaban kasa ta Aaso Rock na nuna akwai bambancin tsaro daga sauran yankunan kasa. Ba lalle ne birnin na da yawan dogayen gine-gine ba amma dai ga dogayen kamarorin tsaro a sassa daban-daban da ko su na aiki ko ba sa yi wannan sai jami'an tsaro ne…
Read More