Editor

9513 Posts
‘Ba mu amince da ficewar Burkina Faso, Mali, Nijar ba’ –  ECOWAS

‘Ba mu amince da ficewar Burkina Faso, Mali, Nijar ba’ –  ECOWAS

Daga BASHIR ISAH Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), ta bayyana cewa har yanzu ba ta samu a hukumace sanarwar ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nija daga kungiyar ba, don haka ba ta amince da ficewar da suka ce sun yi daga kungiyar ba. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, ECOWAS ta ce “tana aiki tukuru tare da wadannan kasashe domin maido da tsarin mulkin dimokradiyya. "Burkina Faso da Nija da kuma Mali, kasashe ne masu matukar muhimmanci ga Kungiyar, kuma tana ci gaba da kokarin ganin an samu mafita game da tsarin…
Read More
Rashawa ke hana ganin bayan matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya – Shettima

Rashawa ke hana ganin bayan matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya – Shettima

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya danganta matsalar tsaron da ta ki ci, ta ki cinyewa a yankin Arewacin Nijeriya da rashawar da ake fama da ita a tsakanin shugabannin al’umma. Ya bayyana haka ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron lacca da bada lamba karramawa na shekara-shekara karo 10 wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya sannan Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dauki nauyin gudanarwa. A jawabin nasa, Shettima ya jaddada yadda rashawa ta yi matukar tasiri wajen zama babban kalubale ga fannin tsaron kasar nan. Matamakin Shugaban Kasar wanda ya samu wakilicin…
Read More
Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Akwai buƙatar malamai su duba lamarin walimar sauka da ake yi yanzu

Daga SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI, Zariya A zamanin dauri duk lokacin da iyaye suka ga 'ya'yansu sun kusa sauke Alkur'ani mai girma zuciyarsu kan cika da murna da farin ciki ne tare da fatan Ubangiji ya nuna musu lokacin. Idan ranar ta taho masu aka tabbatar da hakan, iyaye kan bi malamai da kyautar da ba ta taka kara ta karya ba don nuna godiya ga malaman da kara musu kwarin gwiwa domin su kara jajircewa kan abinda suke yi, su kuma su karva suna farin ciki da matukar godiyar karamcin da iyayen yara suka nuna musu. Idan makarantar allo ce,…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ƙaryata rahotannin da ake zargin ɗan PDP na kai wa ‘yan bindiga makamai

Gwamnatin Zamfara ta ƙaryata rahotannin da ake zargin ɗan PDP na kai wa ‘yan bindiga makamai

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta karyata rahotannin baya-bayan nan da wasu kafafen yada labarai suka rika yadawa cewa an kama daya daga cikin shugaban jam’iyyar PDP  da hannu kan badakalar kai wa ‘yan bindiga makamai a jihar. Mai ba wa Gwamna shawara kan harkokin siyasa ga Gwamna Dauda Lawal, Hon.  Yahaya Yari, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Laraba a ofishinsa. Yari ya bayyana rahotannin a matsayin na sharri da rashin tushe balle makama, yana mai bayyana hakan a matsayin siyasa ce da yarfe daga wasu tsirarun mutane.…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Nijar, Burkina Faso, Mali sun yi adabo da ECOWAS

Da Ɗumi-ɗumi: Nijar, Burkina Faso, Mali sun yi adabo da ECOWAS

Daga BASHIR ISAH Kasashen Burkina Faso da Mali da Nija sun sanar da ficewarsu daga Kungiyar Bunkasa Tattalin Azrzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS). Shugabannin kasashen yankin Sahel ukun sun fitar da wata sanarwa inda suka ce "shawara ce mai cikakken iko" ta barin kungiyar "ba tare da bata lokaci ba". Kasashen masu fama da matsalolin tsaro dtun bayan da sjoji suka karbe mulkin kasashen. Idan dai za a iya tunawa, a watan Yulin Bara ne sojoji suka yi juyin mulki a Nijar, haka ma Burkina Faso 2022, sai kuma Mali a 2020. Duaka kasashen uku ECOWAS ta takatar da su…
Read More
Rundunar Soja ta yi wasan shekare-shekara a Gusau

Rundunar Soja ta yi wasan shekare-shekara a Gusau

*T yi alkawarin kara kokarin kawo karshen ‘yan bindiga a Zamfara. Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar Sojan NIjeriya ta 1 Brigade Gusau a Jihar Zamfara, ta gudanar da bikin African Social Activities WASA na shekara-shekara domin gudanar da ayyukanta a shekarar 2024 da nufin kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara. A jawabin maraba, Birgediya Janar 1 Brigade, S. Ahmed wanda ya samu wakilcin Kanar J. Umaru a wajen bikin da aka gudanar a 1 Brigade Command Gusau a ranar Asabar ya bayyana cewa an fara bikin na WASA ne a shekarar 1901 da nufin…
Read More
Maida hukumomin gwamnatin Legas: Soki-burutsu ’yan siyasar Arewa ke yi, inji Sanusi

Maida hukumomin gwamnatin Legas: Soki-burutsu ’yan siyasar Arewa ke yi, inji Sanusi

*'Yan Nijeriya na cece-kuce kan dauke canja mazaunin CBN da FAAN Daga SANI AHMAD GIWA da MAHDI M MUHAMMAD Mai Martaba Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce, “surutu” da soki-burutsu kawai ’yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja zuwa birnin Legas, wanda shi ne tsohon hedikwatar kasar. Sarki Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun, saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban…
Read More
Farashin man fetur zai sauka, inji Gwamnan CBN

Farashin man fetur zai sauka, inji Gwamnan CBN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farashin man fetur a Nijeriya zai daidaita a bana yayin da matatun mai na gwamnati da na masu zaman kansu suka fara aiki. Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana haka. Ya yi magana ne a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, a wajen kaddamar da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Nijeriya (NESG) 2024 Rahoton Muhimmanci na Macroeconomic Outlook a Legas. Mista Cardoso ya ce, ana sa ran daidaitawa ko rage farashin man fetur yana da tasiri mai nisa a sassa daban-daban, yana ba da gudummawa sosai ga ingantaccen tattalin arziki da juriya…
Read More
Tarar Kwastom babu-gaira babu-dalili ce babban matsalarmu – Ƙungiyar ’yan kasuwar Arewa

Tarar Kwastom babu-gaira babu-dalili ce babban matsalarmu – Ƙungiyar ’yan kasuwar Arewa

Daga JOHN D. WADA, A Lafiya A kwanan nan ne  dai wata hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar arewacin kasar nan bakidaya da ake kira Northern Traders Association a turance wadda ta kunshi duka jihohin arewa na kasar nan 19 ta gudanar da wani gagarumin taron ta a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa don tattauna wasu matsaloli da kalubale dake addabar ‘ya’yan kungiyar bakidaya. A jawabinsa na maraba Shugaban kungiyar na kasa alhaji Baba Usman Jos wanda mataimakinsa Alhaji Jahi Abdullahi ya wakilce shi ya bayyana cewa, kungiyar ta ga ya dace ne ta hada babban taron don samun damar tattauna…
Read More
Gombe na gab da zarta Kano a fuskar kasuwanci – Adamu Baba

Gombe na gab da zarta Kano a fuskar kasuwanci – Adamu Baba

Daga MOHAMMED ALI a Gombe Bayan dogon nazari da ya yi, fitaccen matashin dan kasuwan nan na Gombe, Alhaji Adamu Baba, sai ya yanke hukunci cewa, Jihar Gombe na gab da kamo Kano wajen kasuwanci, kuma nan da shekaru uku ko biyar masu zuwa, za ta zarta cibiyar kasuwancin ta Arewa. Dan kasuwar ya yi wannan kiyasin ce da yake hira da  wakilinmu a harabar wajen kasuwancinsa a Gombe City Stores, da ke tsakiyar birnin Gombe ranar Jumma’ar da tagabata, yana mai cewa, “ko shakka babu ganin yadda hada-hadar kasuwanci da cinakayya ke qara bunkasa a kullum a wannan Jihar…
Read More