Editor

9513 Posts
Ƙona Majalisar Ribas: Kotu ta ɗaure wasu magoyan bayan Fubara

Ƙona Majalisar Ribas: Kotu ta ɗaure wasu magoyan bayan Fubara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin garkame wasu magoya bayan gwamna Siminalayi Fubara su biyar a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bisa zarginsu da hannu wajen kona ginin Majalisar Dokokin jihar Ribas da ke Fatakwal, Jihar Ribas. Mai shari’a Bolaji Olajuwon ya ba da umarnin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024, jim kadan bayan gurfanar da su a gaban kotu kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi ta’addanci da kisan kai. Ko da yake sun qi amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake tuhumar su da su, amma alkalin kotun…
Read More
Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

Fargabar matsalar tattalin arzikin Nijeriya

A makon da ya gabata, Bankin Duniya ya fitar da rahotonsa kan tabarberewar tattalin arzikin Nijeriya. Rahoto a karkashin duba irin cigaban da Nijeriya ta samu, Cibiyar Hada-hadar Kudi Ta Duniya ta bayyana cewa, tabarbarewar yanayin tattalin arzikin Nijeriya na kara jefa al'ummar kasar cikin wani hali. Rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki ya zama annoba ga rayuwar ’yan Nijeriya wanda dole ne hukumomi su yi yaki da hakan. Habakar hauhawar farashin kayayyaki da ke fitowa daga matsalar rashin tsaro, Bankin ya ce, zai iya jefa karin 'yan Nijeriya miliyan daya cikin matsanancin talauci. Tabbas tashe-tashen hankulan da hauhawar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Sabon Gwamnan Kogi ya yi muhimman naɗe-naɗe sa’o’i bayan shan rantsuwar kama aiki

Da Ɗumi-ɗumi: Sabon Gwamnan Kogi ya yi muhimman naɗe-naɗe sa’o’i bayan shan rantsuwar kama aiki

Daga BASHIR ISAH Sabon Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi wasu muhimman naɗe-naɗe 'yan sa'o'i bayan shan rantsuwar kama aiki. Daga cikin waɗanda naɗe-naɗen ya shafa har da Ali Bello wanda aka naɗa a matsayin Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati. MANHAJA ta kalato cewa Bello ɗan uwa ne ga gwamna mai barin gado, Yahaya Bello. Sauran sun haɗa da Folashade Ayodele Arike a matsayin Sakataren Gwamnati, Hilary Ojoma a matsayin Mataimakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati, Elijah Evinemi a matsayin Shugaban Ma'aikatan Gwamnati, Jerry Omodara a matsayin mai bai wa Gwamna shawara kan tsaro, Isah Ismail a matsayin mai bai…
Read More
Kisan fararen hula 37 a Nasarawa: Rundunar tsaro ta amince ta yi kuskuri

Kisan fararen hula 37 a Nasarawa: Rundunar tsaro ta amince ta yi kuskuri

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Rundunar Tsaron Sama ta Nijeriya, ta kai wata ziyarar ta’aziyya na musamman a jihar Nasarawa don jajantawa gwamnatin jihar da iyalai da ‘yan uwan al’ummar Fulani da suka rasa rayukansu sakamakon wasu bama-bamai da sojojin saman suka sako wa wasu matasan Fulani a kauyen Rukubi dake Karamar Hukumar Doma a jihar a shekarar 2023 da ta gabata. Idan za a iya tunawa kimanin shekara 1 kenan daidai da afkuwar wannan mummunan al’amarin a jihar. Da yake bayyana wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, makasudin ziyarar tasu, shugaban rundunar tsaron sama na Nijeriya, Iya…
Read More
AKCOE da FUDMA sun ilimantar da ɗalibansu yadda ake karatun digiri

AKCOE da FUDMA sun ilimantar da ɗalibansu yadda ake karatun digiri

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano A ranar Asabar da ta gabata ne shugabnnin hukumar kwalegin ilimi ta Aminu Kano, mai hadin gwiwa da Jami'ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-ma tare da sauran fitattun masana da shugabanni a matakin jiha da na tarayya da sarakuna da sauran al'umma suka taru a harabar kwalejin AKCOE dake Kano wato Aminu Kano College of Education. Domin taron wayar da kan dinbin dalibai da suka samu shiga wannan kwaleji domin karatun digiri a kwalejin inda masana da dama karkashin shugabancin shugaban hukumar zartarwa na kwalejin Farfesa Tijjani Hassan Darma, da sauran masana suka gabatar da jawabai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An rantsar da Ododo a matsayin sabon Gwamnan Kogi

Da Ɗumi-ɗumi: An rantsar da Ododo a matsayin sabon Gwamnan Kogi

An rantsar da Alhaji Ahmed Usman Ododo a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kogi na biyar inda zai ja ragamar mulkin jihar na shekaru hudu masu zuwa. Alkalin Alkalan Jihar, Mai Shari’a Josiah Mejabi ne ya jagoranci rantsar da Ododo a dandalin Muhammadu Buhari Civic Centre da ke Lokoja, babban birnin jihar a ranar Asabar. Taron rantsarwar ya samu halartar dimbin masoya da magoya bayan sabon gwamnan, inda aka fara rantsar da Mataimakin Gwamna, Elder Joel Salifu Oyibo, kafin daga bisani Ododo ya sha tasa rantsuwar. Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, shi ne ya wakilci Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu a…
Read More
Gomman mutane sun mutu a musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a Filato

Gomman mutane sun mutu a musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a Filato

Bayanai daga Jihar Filato sun ce gomman mutane ne suka rasa rayukansu sakamakon dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a wasu kauyuka biyu da ke yankin Karamar Hukumar Mangu a jihar da safiyar ranar Asabar. MANHAJA ta tattaro cewa an yi artabun ne bayan da Gwamnan Jihar, Caleb Mutfwang, ya sassauta dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 da ya kafa a yankin tun farko. Mutfwang ya ce sakamakon cigaban da aka samu game da sha’anin tsaro a yankin, ya sa ya sassauta dokar daga karfe  8 na safe zuwa 4 na rana. Majiyarmu ta rawaito cewa, kimanin…
Read More
Burina na sauke nauyin al’ummar da nake shugabanta – Hon. Baba-Goni

Burina na sauke nauyin al’ummar da nake shugabanta – Hon. Baba-Goni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe, Hon. Baba-Goni Mustapha Bade ya ce babban burinsa shi ne ya sauke nauyin al'ummar da yake shugabanta, bayan da ya bayyana irin romon dimukradiyyar da ya samar tun bayan hawansa kujerar mulki a qaramar hukumar, inda ya bayyana cewa dukkan nasarorin sun samu ne bisa kyakkyawan jagorancin na Gwamna Mai Mala Buni. Hon. Baba-Goni ya ce babban burinsa shi ne ya ga ya sauke nauyin da al'ummarsa suka dora mishi, ta hanyar ayyukan raya karamar hukumar da inganta rayuwar matasa, tsofaffi, yara da manya. Ya ce shi…
Read More
Ganduje ya buƙaci Kwankwaso, Abba, Shekarau su sauya sheƙa zuwa APC

Ganduje ya buƙaci Kwankwaso, Abba, Shekarau su sauya sheƙa zuwa APC

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bukaci manyan abokan hamayyarsa a siyasa irin su Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Yusuf da Sanata Ibrahim Shekarau da sauransu, su sauya sheka zuwa jam’iyyarsa. Ganduje ya bukaci hakan ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis a Kano. Ya ce dalilinsa na neman abokan hamayyar nasu su komo jam’iyyarsa, shi ne don a hadu a ciyar  da kasa gaba karkashin jam’iyya guda wanda kuma hakan zai amfani al’ummar Jihar Kano. Ya ba su tabbacin komai zai tafi daidai yadda ya kamata muddin suka sauya sheka zuwa jam’iyya…
Read More
Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta fara tantance kadarorin manyan jami’an gwamnati

Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta fara tantance kadarorin manyan jami’an gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Da'ar Ma'aikata (CCB) ta fara tantance kadarorin masu rike da mukaman siyasa da kuma wasu manyan kadarorin gwamnati a wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa da aka sabunta a kasar. Shugaban riko na hukumar, Murtala Aliyu-Kankia, ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin tantancewar da ake yi a ranar Litinin a Katsina. Ya ce atisayen zai shafi manyan jami’an gwamnati da ma’aikatan gwamnati da suka hada da sakatarorin dindindin, daraktoci da sauran manyan jami’an gwamnati.
Read More