27
Jan
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano na shirin samar da dokar da za ta bada cikakkiyar damar aiwatar da tsarin gudanar da aikin gwamnati ta amfani da fasahar sadarwa a duk fadin jihar, domin saukaka ayyukan gwamnati da bunkasa fannin tattalin arzikin ta amfani da fasahar sadarwa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka ne a wajen rufe taron Majalisar Sadarwa, kirkira da fasahar sadarwa karo na 11, wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano jiya Alhamis. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya aikowa Manhaja…
