Editor

9513 Posts
Ɗauke ragamar sassan CBN zuwa Legas: Cika baki kawai kuke, cewar Sanusi ga ’yan siyasar Arewa

Ɗauke ragamar sassan CBN zuwa Legas: Cika baki kawai kuke, cewar Sanusi ga ’yan siyasar Arewa

Daga BASHIR ISAH Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi, ya ce “surutu” kawai ‘yan siyasar Arewa ke yi dangane da shirin Babban Bankin Nijeriya (CBN) na dauke ragamar gudanarwa na wasu sassan bankin daga Abuja zuwa Jihar Legas. Sanusi ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa da su yi watsi da surutan da ‘yan siyasar Arewa ke yi kan batun saboda a cewarsa, Abuja a matsayin Babban Birnin Tarayya ba matsalar Arewa ba ne. Idan dai za a iya tunawa, tun bayan da CBN ya bada sanarwar shirinsa na dauke wasu muhimman sassan CBN daga Abuja zuwa Legas, aka yi…
Read More
Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Sakkwato

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamnan Sakkwato

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Aliyu Ahmad din ne a zaman da ta yi ranar Alhamis inda ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben da Aliyu ya samu a zaben 2023. A hukuncin kotun, wanda Mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta, ya yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Saidu Umar suka shigar na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ahmed Aliyu. Kwamitin alkalin ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke na cewa PDP…
Read More
Kotun Ƙoli ta ayyana Fubara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Ribas

Kotun Ƙoli ta ayyana Fubara a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Ribas

Daga BASHIR ISAH Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta ayyana Sim Fubara a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a Jihar Ribas. Kotun ta yanke hukuncin haka ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis bayan da ta karbi bayana daga bangarorin da shari’ar ta shafa. an takarar gwamnan na Jama’iyyar APC a jihar a zaben 2023 da ya gudana, shi ne ya daukaka kara inda ya kalubalanci nasarar da Gwamna Fubara ya samu a zaben. Nasarar Fubara  a Kotun Kolin na zuwa ne a daidai lokacin da ruwa ke ci gaba da tsami a tsakaninsa da…
Read More
Tasirin marubuci a cikin al’umma tamkar tasirin gishiri ne a cikin miya – Hauwa Shehu

Tasirin marubuci a cikin al’umma tamkar tasirin gishiri ne a cikin miya – Hauwa Shehu

"Yawaitar matsalolin damfara da satar bayanai a yanar gizo ya sa na rubuta 'Harin Gajimare" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Rubutun adabi abu ne da ke buqatar samun jigo mai karfi da zai ja hankalin masu karatu, kuma su amfana da darussan da marubuci ya sarkafa cikin labarinsa, bayan bincike mai zurfi da nazari mai kyau. Wannan shi ne irin tunanin da marubuciya Hauwa Shehu ke son sauran marubuta su fahimta, a kokarinta na fadakar da su yadda za su inganta rubutunsu na onlayin da yake kara samun karbuwa a tsakanin marubuta. Wannan jarumar marubuciya da ta kasance gwarzuwa ta farko…
Read More
Aljeriya ta kori kocinta bayan cire ta a gasar AFCON

Aljeriya ta kori kocinta bayan cire ta a gasar AFCON

Daga BASHIR ISAH A ranar Laraba Aljeriya ta kori kocinta, Djamel Belmadi, bayan da aka fitar da ita daga Gasar Cin Kofin Afrika. Aljeriya ta dauki wannan mataki a kan Belmadi ne bayan da ta sha kashi a hannun Mauritania a ranar Talata a wasansu na karshe na rukuninsu a Ivory Coast. Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Aljeriya, Walid Sadi, ya wallafa a shafinsa na X cewa, "Na hadu da kocin kasar Djamel Belmadi don tattauna abubuwan da ke tattare da wannan rashin nasarar, kuma mun cimma yarjejeniyar kawo karshen dangantakarmu da kuma dakatar da kwantiraginsa." Korar Belmadi ta zo ne…
Read More
Zargin ɓata suna: Kotu ta aike da Ɗanbilki Kwamanda gidan yari a Kano

Zargin ɓata suna: Kotu ta aike da Ɗanbilki Kwamanda gidan yari a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar gidan yari bisa zargin yin kalaman da ka iya tayar da tarzoma a cikin al’umma. Danbilki dai zai ci gaba gaba da zama a gidan yari har zuwa 29 ga watan Janairu. Tun da farko rundunar tsaron farin kaya ta DSS ce ta gayyaci Danbilki Kwamanda din wanda tsohon makusanci ne ga tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, kafin daga bisani su gurfanar da shi gaban kotun Majistiri da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma. Sai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra, Anayo Nnebe ya kwanta dama

Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra, Anayo Nnebe ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Anayo Nnebe ya rasu ne a ranar Laraba a wani asibitin da aka sakaya sunansa. Gwamnan Anambra, Chales Soludo ya tabbatar da rasuwar marigayin a wata sanarwa da ya fitar ta bakin Sakataren Yada Labarai, Mr Christian Aburime. Soludo ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APGA da ma daukacin al’ummar Jihar Anambra. A halin rayuwarsa, marigayin ya zama Kakakin Majalisar Anambra ne daga 2007 zuwa 2011 inda ya shiga majalisar a matsayin wakilin Awka ta Kudu 1. Haka nan, an zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai ta Kasa inda ya wakilci shiyyar…
Read More
Ndume ya gargaɗi Tinubu kan shirin ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas

Ndume ya gargaɗi Tinubu kan shirin ɗauke CBN da FAAN zuwa Legas

Daga BASHIR ISAH Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar Datawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya gargadi Shugaban Kasa Bola Tinubu game da shirin da yake da shi na mayar da ragamar wasu muhimman bangarorin CBN da kuma Hedikwatar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (FAAN) zuwa Jihar Legas. Ndume ya ce muddin hakan ta tabbata, akwai sakamakon da zai biyo baya a siyasance. Ya ce, “Ba za mu yarda da wannan ba. Hasali ma, ba taimakon Shugaban Kasa suke yi ba, domin kuwa hakan na da sakamako a siyasance” Sanatan ya yi wadannan kalaman ne yayin wata tattauna da…
Read More
Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Fitar matasan Arewa ƙasashen waje: Ya kai mai shirin fecewa, ga wata ’yar shawara

Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI A mafi yawan lamura, za ka samu akwai alheri, kuma akan samu akasinsa. Don haka, a irin wannan dambarwar da mafi girman abin da ya jawo ta shi ne rashin kyakkyawan shugabanci, dole sai an yi taka-tsan-tsan. Lallai masu jan ragamar jagorancin al'umma a Najeriya, yawancinsu suna ha'intar al'umma.  Wani bawan Allah yake cewa da fita ko fecewa daga qasa abu ke mai sauki, to watakila shugabannin kasarmu sai dai su juyo su ga ba kowa, kowa ya kama gabansa. To shi dan'adam da Allah ya yi shi ba ya son a hana shi walwalar abin…
Read More
Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Tasirin fina-finan Hausa sun wuce yadda ake ɗaukar su a ƙasar Hausa

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH Wato fina-finan Hausa sun yi nisa wajen jan hankalin al'umma. Ko shakka babu wannan dama ce da za a yi amfani da ita wajen sauya tunanin al'umma zuwa ingantatciyar rayuwa da bin dokoki.  Kwanakin baya a kafofin sada zumunci har majalusu na unguwanni, maganar da na ji ana ta yi ita ce wai raba gardama ya bayyana. Da yake na kwana biyu ba na kallo, na ce wanene wannan raba gardama? Ashe a cikin shirin Labarina ne na Malam Aminu Saira. A satin nan da muka fita daga shi, sai na ji sabon batu. Ko'ina maganar…
Read More