Editor

9513 Posts
Batun sake dawo da martabar noma a Nijeriya

Batun sake dawo da martabar noma a Nijeriya

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai matuƙar gayar muhimmanci ga Gwamnatin Nijeriya ta sake duba batun bunƙasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiƙi kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗqaya. Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba. Haka…
Read More
Buhari ya sauka a Maiduguri duk da hare-hare

Buhari ya sauka a Maiduguri duk da hare-hare

*Boko Haram ta harba rokoki da boma-bomai kafin saukar Shugaban Ƙasar Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, a jiya Alhamis, ya kai ziyarar aiki ta yini guda da kuma ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamnatin Jihar Borno ta aiwatar a Maiduguri, Babban Birnin Jihar, mintuna kaɗan bayan ’yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri ɗin. Manyan ma'aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Bornon, inda jirginsa ya dira da misalin ƙarfe 11.45 na safiyar ranar Alhamis. An samu shakkun cewa, ko shugaba Buhari zai sauka a Maiduguri yayin da wasu…
Read More
Yaƙi da bautar da yara ƙanana

Yaƙi da bautar da yara ƙanana

Sanarwar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Majalisar Ɗinkin Duniya (ILO) ta yi na baya-bayan nan ya nuna cewa, sama da yara miliyan 152 ko kusan ɗaya cikin yara 10 a duniya na fama da tilastawa wajen aure ko yin aikin ƙwadago wanda hakan ba wai kawai abin baƙin ciki ba ne amma har da nuna rashin mutuntaka. Ƙungiyar ta ce, ƙananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a qasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta. Ƙididigar da hukumar ta bayar cikin makon da ya gabata, ya nuna cewa, cikin adadin kashi…
Read More
Shigo da mata da matasa cikin harkokin siyasa ne mafita ga Nijeriya — CITAD

Shigo da mata da matasa cikin harkokin siyasa ne mafita ga Nijeriya — CITAD

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Cibiyar ɓunkasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma, wato Centre for Information Technology and Development (Citad) ta bayyana muhimmancin shigo da mata da matasa cikin harkokin siyasa musamman a zaɓen 2023, inda ta ce ba kawai matasa su fito kaɗa ƙuri'a ko jagaliyar siyasa ne su ke da rawar takawa ba, a'a, ya zama cewa su ma a zaɓe su a matsayin shugabannin jam'iyyu ko kuma a zaɓi wasunsu su zama shugabanni a zaɓen 2023, Babban Jami'in shirye-shirye na cibiyar, Isa Garba ne ya bayyana hakan a wata ziyarar haɗin gwiwa da cibiyar ta kai wa…
Read More
Mun kakkaɓe miyagu a dazukan Katagum, cewar magajin Ali Ƙwara

Mun kakkaɓe miyagu a dazukan Katagum, cewar magajin Ali Ƙwara

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ahmad Muhammad Ƙwara ƙani ne ga Marigayi Alhaji Ali ƙwara, kuma uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da marigayin, kuma shine ya gaje shi wajen yaƙi da 'yan fashi da ɓarayi. A farkon makon da ya gabata ne Ƙungiyar Matasan Arewa ta shirya taron lakca don tunawa da Marigayi Ali Ƙwara kan irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta harkokin tsaro, kasuwanci da kuma taimakon al'umma, wanda aka gudanar a garin Azare ta ƙasar Katagum da ke cikin jihar Bauchi. A ƙarshen taron, manema labarai sun tattauna da Ahmad Ƙwara, kamar haka: Me za ka ce kan…
Read More
Boko Haram sun harba rokoki a Maiduguri gabanin ziyarar Buhari

Boko Haram sun harba rokoki a Maiduguri gabanin ziyarar Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Maiduguri babban birnin jihar Borno gabanin ziyarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. An ce, maharan sun kai hari kan wasu al'ummomi uku a babban yankin filin jirgin sama na Ngomari da ke Maiduguri. Ga dukkan alamu maharan sun nufi filin jirgin ne yayin da suka kai hari da misalin ƙarfe 10:45 na safe, mintuna kaɗan kafin isowar Buhari. Wasu mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, maharan sun afka wa al’ummomin da makaman roka, inda suka kashe mutane da ba a tabbatar da adadinsu ba, tare da lalata unguwanni da…
Read More
Har yanzu Kannywood ba ta san ciwon kanta ba, inji Abdulkareem Muhammad

Har yanzu Kannywood ba ta san ciwon kanta ba, inji Abdulkareem Muhammad

*Yadda taron Karramawa na KILAF 2021 ya gudana Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano Tsohon Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Ƙasa (MOPPAN), Alhaji Abdulkareem Mohammed, ya bayyana cewa, masana’antar shirin fim ta Kannywood har yanzu ba ta gama sanin ciwon kanta ba. Abdulkareem ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da bajekoli da kuma karramawa na KILAF a Birnin Kano da aka kammala kwanan nan. Taron bajekolin finafinai da karramawa mai taken "Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Fastival" wato KILAF AWARD da aka saba gudanarwa a duk shekara a bana ma an gudanar da shi…
Read More
‘Yan jarida suna da rawar da za su taka wajen magance ta’addanci a ƙasa – Farfesa Khalid Zaria

‘Yan jarida suna da rawar da za su taka wajen magance ta’addanci a ƙasa – Farfesa Khalid Zaria

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An bayyana 'yan jarida a matsayin wasu mutane da suke da muhimmanci a cikin al'umma, kuma waɗanda ke da rawar da za su iya takawa wajen magance tashe-tashen hankula da ta'addanci a Nijeriya. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shehin malamin nan masanin tarihi da harsunan Afrika, Farfesa Khalid Abdullahi Zaria, a wajen taron gabatar da littafin sa a ranar Lahadi a Agura Otal da ke Abuja, wanda ya rubuta akan rayuwar tsohon gwamnan Jihar Kwara, kuma tsohon shugaban majalisar dattawa ta takwas, Dr. Abubakar Bukola Saraki. Farfesa Abdullahi ya yi nuni da…
Read More
Kwararowar makiyaya: Ana zaman ɗarɗar a arewacin Jihar Bauchi

Kwararowar makiyaya: Ana zaman ɗarɗar a arewacin Jihar Bauchi

*Sun fara dirar mikiya a gonaki ɗauke da bindigogi, inji tsohon ɗan majalisa*Mu na sane da su, cewar Hakimin Gamawa*Mun fara kama waɗanda suka yi ta’adi – Rundunar ’Yan Sanda Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi Manoma mazauna Ƙaramar Hukumar Gamawa da wasu sassan arewacin  Jihar Bauchi da Jigawa na cikin zaman zulumi da ɗarɗar, saboda bayyanar wasu Fulani makiyaya da babbobinsu, waɗanda suka fito daga wasu yankuna da ake fama da rashin tsaro a Nijeriya, musamman Arewa maso Gabas da ma Jamhuriyar Nijar, inda mazauna yankin na arewacin Bauchi da jihar Jigawa ke ƙorafin makiyayan na tura dabbobinsu dubbai su…
Read More
’Yan bindiga ko ’yan ta’adda: Canja matsayinsu zai kawo ƙarshen matsalar tsaro?

’Yan bindiga ko ’yan ta’adda: Canja matsayinsu zai kawo ƙarshen matsalar tsaro?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ta ke zamanta a Abuja a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Taiwo Taiwo ta ce, ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyi makamantansu a kowane yanki na Nijeriya ya zama na ta’addanci. Don haka ta ayyana su a matsayin ’yan ta’adda ƙarara. Wannan hukunci na ayyana ’yan bindigar ‘yan ta’adda ya biyo bayan buƙatar da Daraktan Shigar da Ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Mohammed Abubakar, ya shigar ne a madadin Gwamnatin Tarayya dangane da ayyukan ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ne da sauran ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a…
Read More