18
Dec
Daga WAKILINMU Sabon gidan talabijin na Qausain ya naɗa shahararren mawaƙi Umar M. Shareef a matsayin jakadansa na farko a Kaduna. Babban Shugaban Kamfanin Qausain Group, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamarwar wanda gidan talabijin ɗin ya shirya a harabar ofishinsa da ke Sultan Road, GRA Kaduna a wannan makon. Shugaban kamfanin ya bayyana jin daɗinsa tare da kuma miƙa godiyarsa ga Allah SWT da kuma ilahirin ma'aikata da waɗanda suka bada gudumuwa har wannan gidan talabijin ya tabbata. Malam Nasir ya bada tabbacin cewa gidan talabijin ɗin zai ta fi daidai da…
