Editor

9513 Posts
Attajiri Otedola ya saka First Bank a aljihunsa

Attajiri Otedola ya saka First Bank a aljihunsa

Daga AMINA YUSUF ALI Yanzu haka, biloniyan ɗan kasuwar nan mai suna Femi Otedola shi ne mutum na farko daga cikin jerin masu hannun jari a bankin First Bank. Biloniyan ya samu nasarar ɗarewa kan matsayin wanda ya fi kowa zuba hannun jari a bankin bayan ya sake sayen ƙarin kaso 2.5 na hannun jarin kamfanin FBNH wanda FBNH shi ne ubangidan bankin na First Bank. Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu ma Otedola yana da hannun jari kaso 7.57 a FBNH. Abinda ya kai har ya doke Tunde Hassan-Odukale, Ciyaman ɗin FBNH a ƙarfin hannun jari a kamfanin.…
Read More
Ku kasance cikin shirin ƙarin haraji – Ministar Kuɗi ta gargaɗi ‘yan Nijeriya

Ku kasance cikin shirin ƙarin haraji – Ministar Kuɗi ta gargaɗi ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Ministar Kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya, Hajiya Zainab Ahmad ta gargaɗi 'yan ƙasar a kan su kasance cikin shirin samun ƙarin haraji. A cewarta, ba makawa za a samu ƙarin haraji a kan wasu mutane da wasu sana'o'i a wannan matsakaicin zangon.  Ministar ta bayyana haka ne ga 'yan kasuwa yayin gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a a game da kasafin kuɗi na shekarar 2021 ranar Litinin ɗin da ta gabata a Abuja. Hajiya Zainab ta ƙara da cewa, Gwamnatin tana tunanin ƙarin harajin ne domin neman farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan. Shi dai…
Read More
Babbaka mutum da wuta gayar azaba ce

Babbaka mutum da wuta gayar azaba ce

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ko a lahira babbar azaba ga mujurmai da wuta za a yi. Ita kuwa wutar lahira makamashin ta mutane ne da su ka saɓa wa Allah da duwatsu kamar yadda ya zo a aya ta 6 ta Suratul Tahrim. A nan duniya ma ai ba azabar da ta wuce a ƙona mutum ko a babbaka shi da ransa a wuta. Son samu aikin wuta irin wannan ta makamashi a girka abinci da ita a sha, amma in ta zama girka mutum ake yi a cikinta, to an gama mummunan mataki. Kai yau ko hukuncin kisa ake…
Read More
Dole ne a ɗore da yaƙi da cin hanci da rashawa

Dole ne a ɗore da yaƙi da cin hanci da rashawa

Ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne al'ummar duniya suka ware a matsayin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙuduri mai lamba 58/4 na ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2003 ta ware ranar 9 ga watan Disamba na kowace shekara a matsayin ranar wayar da kan jama'a game da laifukan da ke kawo cikas ga ci gaba da kuma talauta jama'a. Har ila yau, rana ce ga shugabannin siyasa, gwamnatoci, hukumomin shari'a, ƙungiyoyin fafutuka da qungiyoyin farar hula don sabunta alqawurran da suka ɗauka na kawar da wannan abu da aka gano…
Read More
An zaɓi Samuel Eto’o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Kamaru

An zaɓi Samuel Eto’o ya zama shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Kamaru

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An zaɓi shahararren ɗan ƙwallon Kamaru, Samuel Eto’o a matsayin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (FECAFOOT) a ranar Asabar, wata ɗaya kafin ƙasar ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin Afrika. Tsohon ɗan wasan gaba Eto’o, wanda ya taka leda a Barcelona, Inter Milan da Chelsea, zai karɓi ragamar ƙungiyar da ta daɗe tana fama da rigingimu, rashin gudanar da mulki da kuma zargin cin hanci da rashawa. Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta shiga tsakani sau da yawa don kawo ƙarshen cece-kuce tsakanin jami'an FECAFOOT. Eto’o mai shekaru 40 ya lashe zaɓen da ƙuri’u…
Read More
Korona: Hana ‘yan Nijeriya zarya zuwa wasu ƙasashe ya fusata Buhari, ya ce sai ya rama

Korona: Hana ‘yan Nijeriya zarya zuwa wasu ƙasashe ya fusata Buhari, ya ce sai ya rama

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na maida martani kan hana 'yan Nijeriya shiga wasu ƙasashen duniya saboda korona, Gwamnatin Tarayya ta ce daga ranar Talata mai zuwa, 14 ga Disamba, za ta haramta wa jiragen saman da suka fito daga Canada da Birtaniya da kuma Saudiyya shigowa Nijeriya. Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, shi ne ya bada sanarwar ɗaukar wannan mataki a Legas ranar Lahadi, inda ya ce an ɗauki matakin ne don maida martani kan ƙasashen da suka haramta wa jiragen da suka fito daga Nijeriya shiga cikinsu domin ɓarkewar sabon nau'in cutar korona mai suna…
Read More
EFCC na bincikar wani gwamnan Arewa kan fitar da Naira Biliyan 60 a banki

EFCC na bincikar wani gwamnan Arewa kan fitar da Naira Biliyan 60 a banki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa tu'annati (EFCC), ta tuhumi wani Gwamnan Arewa bisa zargin fitar da kuɗi har Naira biliyan 60 daga baitulmalin jihar da kansa. Hukumar EFCC, wacce ta bayyana hakan a yau a cikin sabuwar sanarwarta, ta ce, gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan amma ba ta bayyana sunansa ba. Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, wanda ya yi magana a sanarwar, ya ce, “zan iya gaya muku cewa sabuwar sashen leƙen asirin da muka ƙirƙiro ne yake yin irin waɗannan abubuwan al’ajabi.” Ya…
Read More
ASUU ta samu biliyan N52.5 daga hannun Gwamnatin Tarayya

ASUU ta samu biliyan N52.5 daga hannun Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya malaman jami’o’i Naira biliyan 30 na asusun farfaɗo da ilimi da kuma alawus-alawus na ilimi da suka samu Naira biliyan 22.5, tare da jaddada cewa ta samu cigaba sosai wajen aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma da ma’aikatan jami’o’in. Ministan Ƙwadago, Sanata Chris Ngige shi ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawarsu da jaridar THISDAY a wannan ƙarshen makon a lokacin da yake ƙarin haske kan halin da ake ciki tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU. Ministan ya ce ya samu sanarwa daga Ma'aikatar Kuɗi ta Tarayya kan cewa…
Read More
Yadda ɗa ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Yadda ɗa ya yi wa matar mahaifinsa ciki a Nasarawa

Daga WAKILINMU Wata matar aure a jihar Nasarawa ta bayyana cewa, ɗan mijinta ne ya ɗirka ma ta ciki. Matar ta ɗora laifin kan mijin nata da ta ce, ya gabatar ma ta da ɗan nasa ne a matsayin ɗan uwansa ba ɗan cikinsa ba. Ta ƙara da cewa, “auren saurayi da budurwa muka yi ni da mijina, wanda yanzu ya rasu. Mun fara samun matsala ne bayan na shafe shekara biyar ba tare da na yi ko ɓatan wata ba. Hakan ne ya sa surukata ta dinga tsangwama ta har shi ma ya goyi bayanta saboda rashin samun ciki…
Read More
Shahararrun Mutanen Afrika: An Karrama Dr. Dauda Lawal A Birnin Landan

Shahararrun Mutanen Afrika: An Karrama Dr. Dauda Lawal A Birnin Landan

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Cibiyar Karrama Shahararrun Mutane na Afrika da ke Landan 'African Achievers Award' ta karrama Dr. Dauda Lawal Dare a shekaran jiya Juma'a, 10 ga watan Disamba a Fadar Kensisngton dake Birnin Landan. Kambun karramawa na 'African Achievers Award' shi ne mafi girma da tasiri a duniya wanda ya ke zaƙulowa tare da karrama mutane masu muhimmanci da suke taka rawa wurin bunƙasar nahiyar Afirka. Taken taron bana shi ne: 'Samar da hanya ga mazauna ƙasashen ƙetare su zuba jari don bunƙasar tattalin arzikin Afirka'. Mujallar Forbes ta ruwaito cewa, wannan bikin karramawa na 'African…
Read More