Editor

9513 Posts
Fim ɗin ‘Fanan’ ya fito da ni idon duniya – Jaruma Sabira Mukhtar

Fim ɗin ‘Fanan’ ya fito da ni idon duniya – Jaruma Sabira Mukhtar

DAGa MUKHTAR YAKUBU, a Kano Sabuwar jaruma a masana'antar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywwod, Sabira Mukhtar, tana ɗaya daga cikin jarumai mata da a ke ganin nan gaba kaɗan za ta zamo babbar jaruma, saboda irin rawar da ake ganin ta taka a cikin fim ɗin 'Fanan'. Duk da cewar ba shi ne fim ɗinta na farko ba, amma dai fim ɗin 'Fanan' shi ne ya fito da ita. A cikin tattaunawar su da wakilinmu, jarumar ta yi bayani a kan shigowarta harkar fim, da kuma yadda fim ɗin 'Fanan' ya ɗaga darajarta, har ya zamo abin alfahi a gare…
Read More
Ta banka wa budurwar mijinta wuta har lahira

Ta banka wa budurwar mijinta wuta har lahira

Daga WAKILINMU Wata matar aure mai ’ya'ya uku a jihar Ogun, Kehinde, ta yi wa budurwar mijinta wanka da man fetur sannan ta cinna ma ta wuta kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwarta. Kakakin hukumar ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ta tabbatar da labarin inda ta ce, tuni an damƙe matar. A cewar ’yar sandan, sun damƙe matar ne bayan tsohon mijin matar da aka ƙona mai suna Fatai Olugbade ya kai ƙara hedikwatarsu da ke Ota. Fatai ya bayyana wa ’yan sanda cewa, tuni sun rabu kuma ta koma soyayya da wani. Ya ce, “ina zargin tana hulɗa da…
Read More
Matashiya ta maka likitar da ta bari aka haife ta a kotu

Matashiya ta maka likitar da ta bari aka haife ta a kotu

Wata matashiya da ta yi ƙarar likitar mahaifiyarta a kotu, saboda ta bari an haife ta, za ta samu miliyoyi a matsayin diyya. Evie Tombes ta yi ƙarar likitar mahaifiyarta ne kan kuskure yayin ɗaukar cikinta da maharfiyarta ta yi, inda ta bari aka haife ta da wata cuta da ake kira ‘Spina Bifida’ a shekarar 2001. Cutar da ba a cika samun ta ba ta na shafar ƙashin baya ne kuma wasu lokutan ta na nakasa mutum har abada. Hakan ya sa Evie a duk rayuwarta sai an jona ma ta robobi na magani. Evie za ta samu matsaloli…
Read More
Da ɗumi-ɗuminsa: An fatattaki ’yan bindiga cikin dare a Kaduna

Da ɗumi-ɗuminsa: An fatattaki ’yan bindiga cikin dare a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga da yawansu sun kai hari unguwar Sabon Tasha, ƙaramar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna cikin daren Asabar, 11 ga watan Disamba, 2021. Rahotanni sun nuna cewa, ’yan bindigar sun banka wa gidan wani mutumi wuta bayan ƙoƙarin garkuwa da shi. Jami'an Sojojin Nijeriya sun samu nasarar fatattakarsu bayan kirar da wani ya yi musu. An tattaro cewa, Sojoji da ’yan bindigar sun yi musayar wuta da daddaren. Wani shaidar gani da ido, Benjamin, ya bayyana wa manema labarai cewa, “’yan bindiga na ƙoƙarin shiga gida-gida kwashe mutane lokacin da sojoji suka isa.…
Read More
Mun rasa fiye da mutum 1000 a kisan kiyashin Zariya – ‘Yan Shi’a

Mun rasa fiye da mutum 1000 a kisan kiyashin Zariya – ‘Yan Shi’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Harkar Musulunci a Nijeriya ta sake yin kira da a tabbatar da adalci ga ɗaruruwan 'ya'yanta da ake zargin sojojin Nijeriya sun kashe a watan Disambar 2015 bayan wani farmaki da sojojin suka kai bisa zargin tare wa shugaban hafsan sojin ƙasa na lokacin, Laftanar Janar Tukur Buratai hanya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. A wata sanarwa da harkar ta fitar a ranar Juma’a mai taken ‘Kira da Adalci ga waɗanda aka kashe a Zariya’, harkar ta bayyana cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su sun kai mutum 1,000 na kowane jinsi…
Read More
Sama da mutum 400 aka kashe a Nijeriya cikin watan Nuwamba – Bincike

Sama da mutum 400 aka kashe a Nijeriya cikin watan Nuwamba – Bincike

Daga SANI AHMAD GIWA Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting da ke fitar da rahoto tare da bayar da shawarwari ga mahukunta game da matsalar tsaro a Nijeriya duk wata, ya wallafa rahoton sa na watan Nuwamba, inda ya ce an kashe sama da mutane 400 a watan, sannan satar jama'a ta ƙaru yawanci a arewacin ƙasar. Rahoton ya kuma ce an yi kisan ne a jihohi 28 na Nijeriyar a ƙananan hukumomi 115 a cikin watan Nuwamba kaɗai. A cewar rahoton, satar mutane a Nijeriya ta ƙaru da kusan kashi 38 cikin ɗari a Nuwamba idan aka kwatanta da…
Read More
Tabbas za mu miƙa mulki ga waɗanda suka ci zaɓe a 2023 – cewar Buhari

Tabbas za mu miƙa mulki ga waɗanda suka ci zaɓe a 2023 – cewar Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bai wa 'yan Nijeriya da sauran ƙasashen duniya tabbacin gudanar da sahihin zaɓe ya zuwa 2023 tare da miƙa ragamar mulki cikin lumana. Mai magana da yawun Buhari, Mr Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja a Juma'ar da ta gabata. Yana mai cewa, Buhari ya bada tabbacin nasa ne yayin wani babban taro da shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya shirya ta bidiyo kan harkar dimukuraɗiyya. Buhari ya ce za a tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da Nijeriya ta sake shaida…
Read More
Yadda haƙuri da juriya suka kai Dr. Jibril Lawal Tafida ga matakin nasara

Yadda haƙuri da juriya suka kai Dr. Jibril Lawal Tafida ga matakin nasara

Daga BABANGIDA KAKAKI  In ka ji wane ba banza ba, in ba a sha dare ba, an sha rana. Wannan magana haka take, musamman idan aka yi duba a cikin ayyukan wasu mutane waɗanda suka ɗauri aniyar kafa tarihi da taimaka wa al'umma don samun ci gaba. A ran 18 ga watan Nuwamban 2021 ne, Jami'ar Gwamnatin Tarayya, wato Federal University Lokoja, ta jihar Kogi ta bayar da digirin girmamawa ga Alhaji jibril Lawal Tafida, wani hamshaƙin ɗan kasuwa, kuma mai taimakon al'umma, sannan ɗan siyasa mai aƙida da ƙoƙarin ganin an kamanta gaskiya da adalci, ɗan asalin jihar Kaduna.…
Read More
Me ya hana Hon. Goro halartar bikin shekaru 25 da ƙirƙiro Ƙaramar Hukumar Fagge?

Me ya hana Hon. Goro halartar bikin shekaru 25 da ƙirƙiro Ƙaramar Hukumar Fagge?

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano A cikin makon jiya ne Ƙaramar Hukumar Fagge ƙarƙashin jagorancin Hon. Ibrahim Shehi ta gudanar da taron bikin cika shekaru 25 da ƙirƙiro ƙaramar hukumar. Sai dai rashin halartar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Fagge, Honorabul Aminu Suleiman Goro taron ta sa ake ganin tamkar bai ɗauki al'amarin da muhimmanci ba, duk kuwa da cewa yana daga cikin waɗanda suka fi cin moriyar albarkacin zaman ƙaramar hukumar Fagge. Wasu na ganin wannan tsantsar nuna rashin karramawa ce ga al'ummar da xan majalisar tarayya na Faggen ya yi ga taron, domin ba na siyasa b ane,…
Read More
Ba zan jajanta maka ba don kai ka nace ka zama shugaban ƙasa – Akande ga Buhari

Ba zan jajanta maka ba don kai ka nace ka zama shugaban ƙasa – Akande ga Buhari

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Chief Bisi Akande ya ce ko kaɗan ba zai jajanta wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba dangane da suka da yake samu bisa ƙalubalolin rashin tsaron ƙasa, domin shi ya nemi ya zama shugaban Nijeriya. Akande ya yi wannan furuci ne a bikin gabatar da wani littafi mai ɗauke da tarihinsa da aka yi wa laƙabi da “Gudunmawa Ta” wanda Shugaba Buhari ya halarta da aka gudanar a Otal ɗin Eko dake Ikko jiya Alhamis. Waɗanda suka halarci bikin gabatar da littafin sun haɗa da Jigon jam’iyyar APC,…
Read More