Editor

9513 Posts
Ɗan Sarauniya ya shawarci Ganduje ya koma makarantar allo

Ɗan Sarauniya ya shawarci Ganduje ya koma makarantar allo

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano Injiniya Mu'azu Magaji, ya shawarci gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya koma makarantar allo domin koyon yadda ake tafiyar da al’umma, tare da sanin matsayin iyali a tsari na tafiyar da mulki. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwmnatin Kano ta fitar da sanarwa Gwamna Ganduje ya tafi ƙasar Amurka domin ɗaukar kwas kan yadda ake gudanar da mulki a jami’ar Harvard. Cikin wani rubutu da Muazu Magaji wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a wannan lokaci Gwamna…
Read More
Malaman jami’a su na rara-gefen koma wa yajin aiki

Malaman jami’a su na rara-gefen koma wa yajin aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Alhamis da ta gabata Ƙungiyar Malaman Jami'a ta Nijeriya ASUU ta koka kan yadda Gwamnatin Tarayya ta kasa cika mata alƙawarin da aka daɗe ana kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar da gwamnati. Lamarin da ya sa ƙungiyar ASUU ta fara rara-gefe da barazanar komawa yajin aiki.  Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa Ƙungiyar Malaman Jami'a ASUU tana cewa har zuwa yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta ce komai ba game da buƙatun da suke nema daga gareta bayan shafe sati uku da suka gindaya. Kwadinetan ƙungiyar ta ASUU, Dr. Salahu…
Read More
Yadda bayyanar Omicron ke barazana ga walwalar ’yan Nijeriya

Yadda bayyanar Omicron ke barazana ga walwalar ’yan Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Duk da tallafin da gwamnatin tarayya ta ce tana bayarwa don rage raɗaɗin talauci da karayar tattalin arziki ga wasu ’yan Nijeriya, sakamakon tasirin da annobar COVID-19 ta haifar ga rayuwar miliyoyin al'ummar ƙasar nan da harkokin su, har yanzu rayuwar wasu da dama ba ta koma daidai ba. Sai a makon da ya gabata ne, a hukumance Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin ma'aikatan gwamnati da ke matakin albashi na 12 zuwa ƙasa su koma bakin aikin su, bayan shafe tsawon watanni takwas suna aiki daga gida, kamar yadda gwamnati ta ba da umarni, domin…
Read More
Sakar wa uwa nauyin ’ya’ya bayan rasuwar mahaifinsu

Sakar wa uwa nauyin ’ya’ya bayan rasuwar mahaifinsu

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Da fatan na same ku lafiya. Yau ma ga mu a filinmu mai albarka, za mu taɓo matsalar da ta addabi mata yanzu. Abinda ya sa na ce ta addabi mata shi ne, yadda matan ke alhini da yadda mazaje suke mutuwa suke barin matansu da nauyin yara, babu mataimaki sai Allah. Ba kuma don ba su da dangin uba ba, suna nan da ransu amma da zarar ɗan'uwansu ya mutu ya bar mace da yaranta, to babu mai damuwa da su, ko taimaka musu. Innallilahi wa inna ilaihi rajiun! Ba wai wannan maganar ƙarya ce…
Read More
Tsaron Nijeriya zai inganta a 2022, inji Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Tsaron Nijeriya zai inganta a 2022, inji Babban Hafsan Sojojin Ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Juma’a ne shugaban hafsan sojin ƙasan Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya da cewa, za a inganta tsaro a faɗin ƙasar nan a shekara mai zuwa. Yahaya ya ba da wannan tabbacin ne a Abuja a wajen rufe taron shekara-shekara na shugaban sojin ƙasa na 2021 mai taken ‘Gina ƙarfin Sojojin Nijeriya wajen yaƙi da barazanar tsaro da ke kunnu kai a ƙasar’. “A yayin taron, mun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi gudanar da ayyukanmu na tsarin mulki da kuma samar da ƙwarewa. Mun kuma yi la’akari da…
Read More
Zanga-zangar rashin tsaro a Arewa; Abin da ya biyo bayan sako Zainab

Zanga-zangar rashin tsaro a Arewa; Abin da ya biyo bayan sako Zainab

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Al'ummomi arewacin Nigeriya sun fara zanga zangar akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Nijeriya. Zanga zangar da aka yi wa lakabi da "A dena Kashemu haka" wato NoMoreBloodShed, Masu zanga-zangar suna bukatar gwamnatin Nigeriya ta samar da sharo a sassan Nigeriya musamman arewa da a ke wa kisan ƙiyashi Kuma suna bukatar a tona asirin masu daukar nauyin ƴan ta'adda kowa ya ji, Suka kara da cewa, idan shugaban ƙasa ba zai iya bada tsaro ga ƙasar ba, to ya sauka ya baiwa wanda ba zai iya. An dai gudanar da zanga-zangar a jahohin…
Read More
Dole a kamo waɗanda suka kashe kwamishinan Jihar Katsina, inji Buhari

Dole a kamo waɗanda suka kashe kwamishinan Jihar Katsina, inji Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da rahoton kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dakta Rabe Nasir da aka yi a yammacin ranar Alhamis. Shugaban a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana kisan kwamishinan a matsayin wani mummunan aiki da Allah wadai da shi, inda ya ƙara da cewa, “ba zai yiwu a riƙa samun irin wannan tashin hankali a ƙasarmu ba.” Shugaban ya ce, ya ji takaicin kisan gillar da aka yi wa wannan shugaba mai…
Read More
Ku mara wa wanda zan kawo a zaɓen 2023 – El-Rufai ga ‘yan Kaduna

Ku mara wa wanda zan kawo a zaɓen 2023 – El-Rufai ga ‘yan Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi kira ga jama’ar jihar da su yarda da shi su mara wa duk ɗan takarar da ya ɗaga wa hannu kakar zaɓen 2023, domin a cewar sa shi ya fi cancanta kuma ya san zai zama gwarzon gwamna. Manhaja ta ruwaito yadda Malam Nasiru El-Rufai ke magana a cikin wani faifan bidiyo cikin harshen turanci yana cewa “wasu suna cewa wai abinda muka yi a yanzu ba za yiwu a maida hannun agogo baya ba, to ba haka ba ne, muddin aka yi rashin sa’a…
Read More
Layikan waya a ƙananan hukumomin Katsina bakwai za su cigaba da kasancewa a rufe – Masari

Layikan waya a ƙananan hukumomin Katsina bakwai za su cigaba da kasancewa a rufe – Masari

Daga SANI AHMAD GIWA Gwamnatin Jihar Katsina ta bada sanarwar cewa ƙananan hukumomi 7 daga cikin 17 da gwamnatin jihar ta katse wa layukan sadarwa a ƙoƙarin ta na magance matsalar tsaron da ta addabi jihar, za su ci gaba da zama a rufe. Hakan ya fito ne daga bakin Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna Masari, Alhaji Abdu Labaran a ranar Juma'ar nan. "Gwamna Masari ya rubuta wa Kamfanin da ke Kula da Harkokin Sadarwa na Nijeriya (NCC) takardar neman buƙatar a maido da hanyoyin sadarwar ƙananan hukumomi 10 daga cikin 17 da aka katse wa layuka fiye da wata…
Read More
Tinubu ne kaɗai ya iya tsallake makircin Obasanjo, inji Buhari

Tinubu ne kaɗai ya iya tsallake makircin Obasanjo, inji Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ne kaɗai ya tsallake makircin Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo a fagen siyasa. Buhari ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi game da rayuwar Baba Bisi Akande a otel ɗin Eko kwanan nan a Legas. A cewar Buhari, "Asiwaju Ahmed Tinubu ya tsallake makircin da gwamnatin Obasanjo ta shirya" a wancan lokaci. Buhari ya yi wannan furuci ne biyo bayan waiwaye da aka yi dangane da tarihin kafuwar jam'iyyar 'All Progressive Congress' (APC) daga jam'iyyar 'Action congress of Nigeria' (ACN). Kazalika, Buhari ya ce makircin…
Read More